AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Ana mulkin Soja ne a kasar nan a cikin rigar dimokradiyya -Shaikh Adamu Tsoho

Daga Saifullahi M. Kabir


Imam Aliy

Wakilin ’yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na Da’irar Jos, Shaikh Adamu Ahmad Tsoho ya nuna matukar takaicinsa ga al’amarin kasar nan da ya zama yanzu ana mulkin Soja ne a cikin rigar dimukradiyya.

Shaikh Adamu Tsoho, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Wakilinmu bayan samamen da Sojoji suka kai Markaz da ke Unguwar Rogo Jos ranar Alhamis 9 ga Zulhijja a lokacin da suke gudanar da addu’ar Arfa, ya yi mamakin irin zaluncin da gwamnatin ke yi masu.

Ya ce; “Ka ji wai mu nemi izinin soja, ba a ce Gwamna, wanda yake shi ne ‘chief-security’ na Jiha ba, ba a kuma ce Kwamishinan ’yan sanda, wanda shi aka sani da tsaron cikin gari ba? Sai aka ce mu je mu samu shugabannin Sojoji mu nemi izininsu, wanda hakan ke nuna maka kasar nan ana mulkin Soji ne a cikin rigar farar hula.”

Ya kara da cewa: “Dama su Sojojin ne suka rusa mana Markaz din a ranar Ashura, domin sun zo nan gidan suka ga akwai mutane da yawa, suka karo ’yan sanda da ’yan banga suka yi ta harba mana tiyagas da dukan wasun mu, sannan Sojoji da kakinsu suka debi zugar ’yan iskan gari suka je suka sace kayan Markaz din, suka kona ta, sannan suka rusa. A yayin da Sojojin suna kallon hakan suna daukar hoto ana masu wakar ‘oyoyo Buratai’. Bayan hakan kuma lokaci bayan lokaci Sojojin suna hanyar gidana da nufin su samu kankanuwar dama su rusa ko su auka mana.”

Wakilinmu ya shaida mana cewa a lokacin da Sojojin suka isa wajen addu’ar, ’yan uwan da ke wajen ba su haura mutum 10 ba, cikin su har da Shaikh Adamu Tsoho da ’ya’yansa kanana guda biyu, ’yan uwa mata guda uku da kuma Harisawa.

Kodayake mota daya ce ta jami’an tsaron ta je Markaz din, amma shaidun ganin da ido sun tabbatar mana da cewa motoci kusan 20 ne aka gani sun tunkaro wajen, a yayin da suka samu labarin cewa wadanda ke wajen ba yawa ne da su ba, sai suka dakatar da sauran motocin suka isa da mota daya, dauke da jami’an tsaro guda takwas.

Isowar jami’an tsaron ke nan suka kewaye Shaikh Adamu Tsoho, tare da ’yan uwan da suke addu’a tare da shi, cikin shirin harbi. Nan suka fara musayar yawu a tsakanin su. Yayin da wani wanda yake Musulmi ne a cikin su ke cewa; “Mu tashe su kawai, ba mun zo kallon su ba ne”. Sai Ogansu, wanda shi ba Musulmi ba ne ya ce; “A bari su karasa”, domin shi ba zai wulakanta mai addini ba.

Yayin da Shaikh Adamu Tsoho ya kammala addu’ar, sun nemi tattaunawa da shi, inda suka bayyana cewa an sanar da su ne daga ‘sama’ cewa ana taro a nan wajen, don haka aka turo su a kan su tarwatsa su.

Sai dai kamar yadda shi wannan da ba Musulmin ba yake fada; “Ko da muka zo mun ga kuna addu’a, don haka sai na ji ban so a ce ni aka turo na maku abin da aka ce ba. Don haka ne ma muka bari ku kammala, sai mu sanar da ku cewa daga yau an hana ku taro a nan wajen sai kun nemi izinin sojoji daga sama.”

Ya kara da cewa, idan an nemi izinin manyansu, kuma suka amince, to su a shirye suke su rika zuwa wajen ma suna ba ’yan uwa kariya.

Ganin yanayin da yake magana ya sa Shaikh Adamu Tsoho ya ba shi amsa mai gamsarwa da cewa; “Wannan muhallin namu ne ba na mutanen gari ba, ba kuma na Sojoji ba ne, kuma har zuwa yau ba mu ji ko da gwamnati ta yi shela cewa ta kwace wajen namu ba. Kafin a ce an hana mu karatun da muke yi ko addu’a a wajenmu, yana da kyau a sanar da cewa an kwace wajen ne, sai mu sani duniya ma ta sani cewa an zalunce mu ne. Amma yanzu Sojoji ba su da ikon kawai su zo su ce wajenmu idan za mu yi taro a cikinsa sai mun nemi izininsu.”

Ya kara da cewa: “Tun da muke Harkar nan ta Musulunci babu wani abu da muke yi da ya sabawa hatta dokar kasar da kuke karewa. Don haka ne ma a kowane lokaci za mu yi taro ba mu da bukatar zuwa wajen wani don neman izininsa a kan taronmu, saboda abu ne da hatta a kundin tsarin mulkin kasar ba mu saba ba. Don haka za mu ci gaba da taronmu yadda ya samu, kuma nan wajen dama lalura ta sa muka bar shi tsawon lokaci tunda aka rusa mana ba mu zo mun gyara ba, insha Allah za mu gyara kayanmu mu ci gaba da karatu da ibadarmu a wajenmu.”

Duk da yake alamu sun nuna cewa shi wanda aka yi tattaunawar da shi ya fahimci zantukan Shaikh Adamu Tsoho din, sai dai ya ce turo su ake yi, don haka suna fatan ’yan uwa su ci gaba da zama lafiya. “Amma bayan sun koma mun samu labarin cewa sun samu sabani a tsakanin su, saboda an ba su umurnin su zo su bude mana wuta ne, suka zo kuma suka yi magana da mu har suka fahimce mu,” cewar Shaikh Adamu Tsoho a yayin da yake bayani ga Wakilinmu.

Don haka ya ce; “Akwai bukatar al’ummar kasar nan su fadada tunaninsu, su fahimci cewa ba komai ake mana ba face zalunci a fili, kuma duk wanda ya goyi bayan zalunci yana matsayi daya da azzalumi ne a ranar lahira. Wajibi ne kowane mai hankali ya fito ya nuna rashin amincewar sa da zaluncin da ake yi wa ’yan uwa da ma al’umma baki daya. Idan ba haka ba kuma, da sannu Allah zai jarabce su da fiye da abin da ake mana, kamar yadda yanzu muna iya ganin tun bayan abin da aka yi a Zariya a karshen shekarar 2015 har yau kasar nan a rikice take”.

Ya karkare da cewa; “Mu kam, ko gezau ba za mu yi ba, muna addini ne ga Allah (T) wanda shi ne ya halicce mu. Amma lallai ba za mu yi sako-sako ba, ba za mu ji tsoron azabar waninsa, mu rungumi ta Allah (T) a sakamakon bin azzalumai ba.”


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron