AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Abubuwan da suka fi ta da hanalina a waki’ar tattakin Kano - Cewar Malama Khadija Dawud Hadejia

Daga A. M Taheer Hadejia


Imam Aliyu

>ALMIZAN: Malama da farko gabatar da kanki ga masu karatunmu.

MALAMA KHADIJA DAWUD: Sunana Khadija Dawud Hadejia. Ina daya daga cikin wadanda waki'ar tattaki ta rutsa da su.

ALMIZAN: Ba mu labarin waki’ar yadda ta faru?

MALAMA KHADIJA DAWUD: Muna sahu muka fara jin ‘tear gas,’ dan wani lokaci sai suka fara harbi. A nan ne na fadi, sai ga Ummi Yahya da Sukaina suka zo suka dauke ni, suka kai ni cikin mota. To, a lokacin suna ta harbi, sai suka zo motarmu. Suna zuwa suke ihu akwai mutane a ciki. Akwai wani dan’uwa a gaban motar, suna ta harbin sa, suna cewa “ka tashi ka gudu!”

Suna harbin sa har sai da idonsa ya fado. A nan dai ya yi shahada. Sai suka dawo baya suna harbowa, sai ya same ni a kafa. Sai Fatima ta ce ni ma an harbe ni. Akwai wata yarinya ma suka barbe ta, a take ta yi shahada. Akwai wani dan’uwa a bayan motar, shi ma suka karasa shi ya yi shahada. Suka fito da mu, sai suka ce a nemo yayi a kone mu. Har wani ya debo, wani ya ce kar ka kone su. Sai wani ya ce wa Batula ta kwanta, da ma ita kadai ce ba a harba ba. Ta kwanta, ya harbe ta ta baya, ya fito ta kirjinta.

ALMIZAN: Bayan nan sai me ya faru?

MALAMA KHADIJA DAWUD: Sai suka debe mu suka bar ita Batula a can, suka kai mu asibiti, suka wanke mana ciwon da ruwa, sannan aka dura mana ruwa. Da ya kare a sake sa mana. Ni lokacin ba na gani ma saboda tsabar ciwo. Wani Likita ya zo ya ce za a yi mana aiki, sai dansandan ya ce, a rabu da mu za su kai mu asibitinsu can Bompai su yi mana aiki. Sun dauke ni ke nan, to, akwai wani dan’uwa yana cewa, “ruwa”, suna: “Ba za a ba ka ba”. Ni kuma ina cewa ku taimaka ku ba shi. Wani dan Santa ya ce: “To ’yar masu imani, ba za a bayar ba, sai ya yi shahada.” Bayan sun kai mu asibiti, mun fi awa daya a motar sun aje mu sannan suka kai mu asibitinsu suka ce sun tashi. “Yanzu muka gama da ’yan’uwanku”.

Duk gun jini, sannan suka ba mu ‘statement’. Ni tsabar ciwo ban iya rubutu ba. Can aka kai ni wani daki na suma. Da na farfado sannan na ga ’yan’uwa, sannan suka kawo mana tea da bread muka sha, ba ma iya tashi. Muna kwance sai aka kawo wasu Sisters. Daya ta daga ni za ta ba ni, amma ban iya sha ba, saboda ciwo, dayar kuma Batula, haka dai. Bayan kwana biyu suka zo da Azahar aka fito da ’yan’uwa maza da mata.

Wadanda aka karbi wayarsu aka ba su, suka ce yau za mu tafi gida, har suna tsokanar Amaryar cikin mu cewa, yau za ta koma gidanta. Suka sa mu a wata babbar mota suka dinga gudu da mu. Wasu ma a nan suka karasa karyewa. Mota biyu ta ’yansanda a gaba da bayanmu. Sannan suka kai mu kotu.

ALMIZAN: Za ki iya tuno abin da ya faru a kotu?

MALAMA KHADIJA DAWUD: Bayan sun kai mu kotu, aka kira Alkali. Aka karanto cewa ana tuhumar mu da kashe dansanda. Muka ce mu ba mu kashe dansanda ba. Sai ya ce, a kai mu gidan yari na wata daya, aka kai mu.

ALMIZAN: To, ko yaya zamantakewa a cikin ku da kuma sauran mutanen gidan yari? .

MALAMA KHADIJA DAWUD: Muna zaune lafiya da mutanen gidan yari. Suna tausaya mana, suna son mu, amma duk da haka ba mu taba yarda wani abu ya hada mu ba. Sai dai ka san dole ne wani lokaci a samu sabani. Ba mu yarda sun zagi agoranmu ba ko akidarmu. Kuma tsakanin mu ’yan’uwa muna taimakawa juna. Burazu suna taimaka mana sosai. Gaskiya mun ji dadi sosai.

ALMIZAN: Sun kara kai ku kotun?

MALAMA KHADIJA DAWUD: E, sai lokacin da suka ce za mu koma kotu, Mal. Jafari ya ce, ba za mu je ba, suna mana yawo da hankali.

ALMIZAN: Kamar mene ne ya fi ta da miki hankali a waki’ar?

MALAMA KHADIJA DAWUD: Gaskiya abin da ya fi ta da min hankali, yadda na ga ana harbin wannan dan’uwan har sai da idonsa ya zazzago da kuma yadda na ga halin da Batula take ciki, harbin ta da kuma yadda take rarumar kasa tana neman ruwa, amma sun hana ta, da kuma yadda na ga ’yan’uwa suna karasa yin shahada a cikin motar. Wadannan sun fi ta da min hankali.

ALMIZAN: Wadanne darussa kika koya a wannnan waki’ar da kuma abubuwan da suka burge ki wanda ’yan’uwa suka yi?

MALAMA KHADIJA DAWUD: Gaskiya na koyi darussa da yawa. Na ga yadda ’yan’uwa suka samu sabati. Kuma ni kaina lokacin da ake harba tear gas na rasa sabati, amma bayan da muna motar ji nake wani irin sabati da dakewa a cikin raina, komai za su yi mana ma su yi mana. Sai lokacin da nake ce wa dansandan nan ya ba wa wannan ruwa, ji nake kamar in kwace in ba shi.

ALMIZAN: Yaya kike ji a ranki, za ki kara komawa tattaki?

KHADIJA DAWUD: Hmmmm! Wallahi ko yau aka ce a fita zan fito, don har mutanen gidan yarin suna ce mana: “za ku koma?” Muka ce musu daga nan gidan yari wallahi za mu dau hanya, kuma rigata da na je da ita zan koma da ita, haka harsashin da aka harbe ni da shi za ai min dankunni da shi.

ALMIZAN: Yaya kuna gabatar da ‘programs’ da addu’o’i?

KHADIJA DAWUD: Kullum muna gabatar da addu’o’inmu da karatun Alkur'ani da kuma wasu munasabobin, don a daren haihuwar Sayyida Zahra, bayan mun yi sallolinmu, mun dan kwanta, sai wannan Amaryar ta ga Sayyida Zahra (a.s) sai ta tashi Batula take nuna mata, amma ina ba ta gani ba. Ni ma haka ta nuna min, amma ban gani ba, sai take kuka. Kukan nata ya tashi mutane, tana ta nunawa, amma ina sai ta ce: “Ga ta nan tana dafa kan Batula tana addu’a, ta zo kaina ta min addu’a”. Haka dai sai ta ce mana ga ta nan za ta tafi kofa ta bude tana dago mana hannu, haka mu ma muka daddaga kamar muna ganin ta. Washe gari kuwa muka yi wanka, muka sa sabbin kaya, muka fesa turare, sannan kuma muka daukin bokitai muna kida, muna murnar Maulidin har ma muka yi kwarya-kwaryar Muzahara a gidan.

ALMIZAN: Ya kuma batun ’yan’uwa na waje da na jini suna kai muku ziyara?

KHADIJA DAWUD: A gaskiya ’yan’uwa sun yi kokari sosai, Allah ya saka da alheri, don suna ziyartar mu sosai. Kuma ko magani ’yan’uwa ne suke kawo mana. Haka in za a yi mana aiki, ’yan’uwa ne suke kawo wa Likitoti. Kuma haka ’yan’uwa na jini suna zuwa ziyara.

ALMIZAN: Wace shawara kike da ita ga ’yan’uwa?

KHADIJA DAWUD: Shawarata ita ce ’yan’uwa a ba da kaimi a dage, don Wallahi azzalumai su ba za su bar mu mu yi addini ba, kuma mu ma ba za mu fasa ba. Kuma Allah ya saka wa Sayyid Zakzaky (h) da alheri don shi ne ya nuna mana wannan tafarkin shiriya. Kuma Allah ya kara kare shi, ya kara masa lafiya, ya gaggauta kwato mana shi daga hannun azzalumai. Ilahii.

ALMIZAN: Malama mun gode.

KHADIJA DAWUD: Ni ma na gode.