AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Shekaru 21 da waki’ar Abacha: Ina da shekaru 2 aka kashe Mahaifina -Hamida Shahid Nuhu Adam


Maulid Sayyada Fatima

A ranar Talatar nan da ta gabata ne aka yi tarurrukan cika shekara 21 da waki’ar Abacha, wacce aka kama Shaikh Ibraheem Zakzaky, washegari kuma aka yi Muzahara, inda jami’an tsaro suka bude wuta a daidai Kofar Doka, har suka kashe mutane 14. A cikin wadanda suka yi shahada a ranar har da Shahid Nuhu Adam Dokar Mai Jaki.

A cikin hirar da Aliyu Saleh ya yi da ’yar Shahidin, Malama Hamida Nuhu, ta bayyana masa yadda ta samu labarin irin kisan da aka yi wa Mahaifinta, domin ya yi shahada ne tana da shekara biyu a duniya, da kuma irin yadda take tsaye kyam a kan tafarkin da ya bar su a kai.

ALMIZAN: Za mu ji suna da shekarunki?

HADIMA SHAHID NUHU: Sunana Hamida Shahid Nuhu, shekaruna 23 a duniya. Na yi aure a cikin wani gari mai suna Raga da ke yankin Karamar Hukumar Gamawa a Jihar Bauchi a cikin watan Fabairu 2017.

ALMIZAN: Kina cikin ’ya’yan Shahidan da suka yi shahada a waki’ar Abacha, kina da shekara nawa a lokacin?

HADIMA SHAHID NUHU: A lokacin ina da shekara biyu a duniya.

ALMIZAN: Ke nan ba ki san Mahaifinki ba, sai dai daga baya aka ba ki labarinsa?

HADIMA SHAHID NUHU: Gaskiya ne ban san shi ba ko a hoto. Ban samu hoton da ya fito sosai wanda zan iya gane shi ba.

ALMIZAN: A ina Mahaifin naku yake da zama kafin waki’ar?

HADIMA SHAHID NUHU: Muna garinmu da ake kira Dokar Mai Jaki a cikin Karamar Hukumar Kubau a Jihar Kaduna.

ALMIZAN: Me kika samu labarin ya faru da Mahaifinki?

HADIMA SHAHID NUHU: Na samu labarin Maihafina ya tafi Muzahara a Zariya ranar Juma’a 13/9/1996, bayan an kama Sayyid Zakzaky a ranar Alhamis 12/9/1996, sai abokin tafiyar tasa ya ce bai gan shi ba. Da yake jami’an tsaro sun bude wuta a daidai Kofar Doka, da aka bincika cikin Shahidai sai aka ga yana cikin su. Sai aka hada shi abokin tafiyar Maihaifin nawa da wani Buraza suka je can garin namu suka shaida wa Mahaifinsa abin da ya faru, kuma aka ce ana son dan uwasa na jini ya zo Babban Dodo, Zariya gidan Alhaji Hamid Danlami. Mahaifin nawa yana cikin wadanda aka binne su a makabartar Unguwar Bishir da ke Zariya.

ALMIZAN: Yanzu ina Mahaifiyarki take?

HADIMA SHAHID NUHU: Tana can garinmu Dokar Mai Jaki, ta yi wani auren bayan shahadar Mahaifinmu.

ALMIZAN: Ku nawa ne a wajen Mahaifinku?

HADIMA SHAHID NUHU: Mu uku ne, ni da kuma Yayata Maryam, da kanwarmu Shahida. Ita Maryam ta yi aure a Kaduna tana da ’ya’ya biyu; Nusaiba da Zainab. Ita kuma kanwar tamu Shahida dama an haife ta ne bayan shahadar Mahaifinmu, sai aka sa mata suna Shahida. Ba ta yi shekara daya a duniya ba ta rasu. Yanzu mu biyu muka rage.

ALMIZAN: Yanzu ana tarurrukan cika shekara 21, wanda ya yi sanadiyar rasuwar Mahaifinki, me za ki ce ga wadanda suka aukar da waki’ar?

HADIMA SHAHID NUHU: Ni dai ba abin da zan ce masu, sai jan kunne, tare da gargadi da cewa sun dai gani, duk da sun kashe Mahaifinmu, ba mu gushe a kan tafarkin da su Mahaifan namu suka rasu a kai ba. Muna nan daram, ba gudu ba ja da baya, har sai mun riske su a inda suke.

ALMIZAN: Wato duk da cewa sun yi kisan ne domin su firgita ku, wannan bai sa kun ji tsoron kasancewa a Harka Islamiyya ba?

HADIMA SHAHID NUHU: Ba wata razana, muna ci gaba da bin tafarkin da aka kashe iyayenmu a kai. Za mu ci gaba da kasancewa har fitar numfashinmu na karshe insha Allah.

ALMIZAN: A tsawon shekaru 21 da kashe Mahaifin naku, ko gwamnati ta taba yi maku jaje, ko kuma ba ku wani tallafi?

HADIMA SHAHID NUHU: Gaskiya gwamnati ba ta taba yi mana jaje, ko kuma ba mu wani tallafi ba. Ba mu ma taba jin an yi wata magana a kan Mahaifanmu da Abacha ya kashe ba tare da ya aikata laifin komai ba.

ALMIZAN: Akwai Mu’assasatus Shuhada da aka kafa domin tallafa wa iyalan Shahidai, ita ta taba tallafa maku kuwa?

HADIMA SHAHID NUHU: Ni dai gaskiya babu abin da zan ce wa Mu’assasatus Shuhada sai dai godiya. Tun bayan Shahadar Mahaifinmu, sai karatu da rayuwata ta dawo Zariya. Na yi firamare da sakandire a Fudiyya Zariya. Na je Jama’atu School of Health na yi diploma. Duk su suka dauki nauyin karatuna har na gama. Da zan yi aure ma su suka dauki nauyin komai nawa. Wato su suka aurar da ni. Don haka babu abin da zai ce masu sai godiya.

Don haka zan yi godiya ta musamman ga Wakilan Mu’asassatu Shuhada, musamman Shaikh Abdulhamid Bello da kuma wanda ya rike ni tun ban san kaina ba, Malam Ibrahim Potiskum (Allah ya ba shi lafiya) da Malaman makarantarmu. Allah ya saka wa kowa da alheri.

ALMIZAN: Yanzu kuma ana cikin wata waki’ar bayan shekaru 21 da kashe Mahaifinku, wanda Sojoji suka kai hari gidan Shaikh Zakzaky har suka kashe mutane sama da 1,000, kuma suka tafi da shi bayan sun harbe shi, ban san me za ki ce a kan haka ba.

HADIMA SHAHID NUHU: Ina son in fada wa ’ya’yan Shahidai da Iyalansu da sauran ’yan uwa cewa su yi hakuri, duk abin da yi farko, zai wuce. Kamar yadda aka ga karshen waki’ar Abacha, insha Allahu wannan ma za ta zo karshe.

ALMIZAN: Akwai sako da kike da shi ga makasa Mahaifinki?

HADIMA SHAHID NUHU: Sakona gare su shi ne su sani cewa ba mu manta ba, kuma ba mu yafe ba. In za su hankalta su hankalta, domin idan sun kashe iyayen yara sun bar su da rai, su sani yaran suna tasowa ne da kaunar abin da aka kashe Mahaifansu a kai, ba wai tsoro ba. Kuma insha Allah muna fatan kamar yadda waki’ar Abacha ta zama tarihi shekaru 21 da suka wuce, ita ma wannan za ta zama tarihi. Kamar yadda jariran da aka bari irin mu, suka taso, haka su ma wadanda aka kashe iyayensu a wannan waki’ar za su taso da soyayyar Harka Islamiyya da Jagoranta Sayyid Ibraheem Zakzaky, har azzaluman da ke zaluntar mu su ji kunya.

ALMIZAN: Mun gode kwarai da gaske.

HADIMA SHAHID NUHU: Ni ma na gode.