AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 JBugu na 1308 ISSN 1595-4474

Rahotanni

Shekara 10 da WaKi'ar Sakkwato: WaDanne darussa muka koya?

Daga Sulaiman Musa Bodinga


soji

Tun bayan assasuwar Harka Musulunci KarKashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), shekara 40 da suka gabata, aka soma samu waKi'oi daban-daban a cikin Harka. Wasu waKi'o'in kan zo da kisa kai tsaye, yayin da wani lokaci kuma a haDa biyun, kisa da Dauri, har ya zuwa kan wannan waKi'a ta tarihi da aka yi a Zariya, wadda ta Kara tambatsa Harka zuwa sassan duniya, ta kuma Kara fito da sunan Shaikh Zakzaky (H) da kuma matsayinsa a duniya

Kamar sauran waKi'oi, ita ma waKi'ar Sakkwato, na Daya daga cikin waKi'oin da a tarihin Harka ba za a manta da ita ba. Domin kuwa waKi'a ce babba, wadda lamarinta ya girmama Kwarai. Kusan shekaru goma bayan aukuwarta, amma har yanzu burbushinta bai kwaranye ba.

Tsohon Gwamnan Sakkwato Attahiru Bafarawa ne ya soma assasa murahu da tubalin gini da suka zama makunni da ya zama silar aukuwar waKi'ar, a shekarar 2005, kafin zuwa Gwamna Alu Magatakar Wamakko, ya aiwatar da tsararren shirin rusa Harka a garin Sakkwato, ba tare da tsoro ko fargabar abin da zai biyo baya ba. Inda da hawansa matsayin Gwamna a jihar, a shekarar 2007, ya yi amfani da kujerarsa wajen KoKarin cika alKawarin da ya yi wa Sakkwatawa a lokacin yaKin neman zabe na dira kan yan'uwa da Daukar matakin rusa Harkar baki Daya.

Ga masu neman sanin asali ko dalilin da ya aukar da waKi'ar Sakkwato, lallai bisa abin da aka fahimta, dalili guda Daya ne, shi ne, kallon Dagowar ba-zata da Harka ta yi a garin Sakkwato, musamman tsakanin shekarar 2001 zuwa 2004, domin a Kashin gaskiya Allah ya yi wa Da'irar Sakkwato baiwa da tsayayyun jagorori da suke da zalaKa da kuma baiwa ta magana da salo na isar da saKon Harka a baki da kuma a aikace ga al'umma. Wannan sirri da kuma dagewa da shiga lungu da saKo wajen isar da saKon Harka da yan'uwan suka yi ne ya sa al'umma da yawan gaske a garin suka fahimci Da'awar Shaikh Zakzaky (H). Wannan ci gaban da motsi da Harka ke yi ne ya soma Kona zukatan mahukuntan garin, musamman masarauta garin. Wannan ya sa suka haDu waje Daya suka soma Kulle-Kulle da makirce-makirce da sharruka don ganin sun taka birki ga abin da suka kira barazana ga mulkinsu.

Sun soma muguwar saKarsu ne da ingiza wasu da sunan Malamai suna tashi a masallatai, suna yawo unguwanni, suna soke-soke a kan Shi'a da manufar faDakar da al'umma haDarin Shi'a da KoKarin dawo da mutane daga fahimtar Harka Musulunci, wadda suka ambata a matsayin sabon Addini. Tun ba a je ko'ina ba suka fahimci aikin da aka Dora wa Malaman, sun kasa. Shi ne mahukuntan suka sake dabarar sake Karfafa su da dafa masu baya, musamman lokacin da suka ji Malaman sun yi fatawar halasta kisan yan Shi'a, suka kuma bayyana kadarorinsu a matsayin ganima. HaKiKa a yayin wannan aikin na ta'addanci, Fwamna Alu Wamakko a Kashin kansa ya nuna rashin imani da rashin tausayin bil'adama da ba a taba gani ba a tarihi, sai zuwan tsohon soja Buhari Dan Adamu, inda duk da Musuluncin da suke iKirari, bai sa sun Dauki kashe rai a bakin komai ba.

Tabbas abubuwan da suka faru a waKi'ar Sakkwato da ba su faru ba, da Kilan hankali ba zai sawwala cewa hakan zai iya faruwa ba. Abubuwa masu muni da sosa rai sun faru a waKi'ar Sakkwato, shigen irin abubuwan dabbancin da suka faru a waKi'ar Zariya. Ba mamaki wannan dalilin ne ya sa Shaikh Zakzaky (H) ya girmamar da al'amarin waKi'ar Sakkwato, a tsokacin da ya yi kan waKi'ar. Ya faDa da bakinsa mai albarka cewa, tun bayan waKi'ar Karbala, wadda wasu maKiya da suke amsa sunan Musulmi suka dira kan iyalan Gidan Manzon Allah (s), suka kashe su da nufin dushe hasken Musulunci, tarihi bai zo da waKi'a irin ta Sakkwato ba. Yanzu idan aka yi duba, a waKi'ar da ta faru a Zariya, a iya cewa ba abin mamaki ba ne don sojan Nijeriya, wanda a rayuwarsa ya fi Koshi da ruwan barasa (giya) bisa ruwan da yake sha, ya sa bindiga ya harbe mutum, ko ya harbe mace ko jariri. Wannan wani abu ne? Amma abin mamaki ne a ji mutum ya haDa kai da yan iskan gari su kashe Dan'uwansa na jini, saboda an yi fatawa an ce kafiri ne. Har ila yau ba abin mamaki ba ne sojan Nijeriya bisa tarbiyyar da aka yi masa da kuma umurni kai tsaye da aka ba shi, don ya kashe mutum ya Kona gawarsa da wuta, amma har gobe abin mamaki ne a wayi gari mutane yan unguwarku da ka sani, suka san ka, dare Daya su Dauko makamai su yi ta saran ka da shi har sai sun ji numfashinka ya Dauke, alhali ba ka yi masu laifin komai ba.

Da za a lura ba abin mamaki ba ne don sojan Nijeriya da aka tura shi ya je ya yi kisa, ya sa bindiga ya kashe mutum, ya kuma yi amfani da dammar, ya sace abin amfani a jikinka, amma zai zama abin mamaki idan har yan'uwan mutum na jini da suke amfana da shi, suka haDa kai da wasu, don a kashe shi, ko a Kona dukiyarsa, su bar ganin sa a bisa doron Kasa. Ashe ba abin mamaki ba ne Kwace shago, fili, ko gida da yan'uwa suka mallaka tare da taimakon dangi da abokai? Duk an yi fiye da haka a waKi'ar Sakkwato!

Meye bambancin ire-iren waDannan abubuwan da aka yi a waKi'ar Sakkwato da wanda ya faru a Karbala? WaDanda suka kashe ya'yan Ma'aiki (s) a Karbala, sun san matsayinsu, sun kuma san ko su waye. Haka su ma waDanda suka yi ta'addanci a kan yan'uwa na Sakkwato. Akwai abubuwa da dama da suka faru na rashin imani da rashin tausayi da yan'uwa suka fuskanta daga mahukunta a garin Sakkwato a lokacin waKi'ar, amma cikin iko da hukunci na Ubangiji, ga al'amarin waKi'ar ya zo ya wuce. Burin da mahukuntan suke da shi na ganin bayan yan'uwa da Harka Musulunci a garin Sakkwato bai cika ba. Kuma lallai ba za su iya ba, kuma wannan burin nasu ba zai cika ba har abada. A daidai lokacin da waKi'ar ke cika shekaru goma, mun yi bitar kaDan daga darussan da yan'uwa suka koya a waKi'ar:

SADAUKARWA: Sakamakon yadda mahukunta garin Sakkwato suka fito da iya Karfinsu domin share yan'uwa a garin da kuma rusa Harka baki Daya, matakin ya Karfafi yan'uwa sosai wajen Kara masu Kumaji da sadaukarwa kan al'amuran gwagwarmaya, tun daga kan yan'uwan da suka yi hijira har kan waDanda suke tsare a kurkuku, da ma ragowar yan'uwan da suka yi saura a garin, a wannan lokacin yan'uwa sun sadaukar. Ma'ana sun yi gudummuwa daidai gwargwado na abin da za su iya, don kada Harkar gwagwarmaya ta tsaya. A wannan lokaci jama'ar gari da su kan su Azzaluman da suka sabbaba waKi'ar, sun yi mamaki irin jarumta da kuma sadaukarwar da yan'uwa suka nuna, ganin iya makirci da makida da suka yi a kan yan'uwa, wadda a zatonsu al'amarin Harka Din ya zo Karshe, sai suka ga ba haka ba.

JAGORANCI: Jagoranci muhimmin abu ne a kowane al'amari. Daga cikin mummunar dasisar da Azzaluman suka yi a lokacin waKi'ar shi ne, a zato da tsanmaninsu, tsananin Kunci da mawuyacin hali da suka saka yan'uwa zai sa su kauce hadafin Harka ma'ana su nesanta daga amsa umurni ko hani a cikin Harka wanda hakan zai sauKaKa masu su cimma hadafin suna tarwatsa Harka, sai dai kidahumancin azzaluman ya sa sun manta ba wannan ce waKi'a ta farko da yan'uwa suka fuskanta ba. Kuma ba su san cewa yan'uwa ba haka suke a kara zube ba, suna da tsari da manufa. Lallai tsayuwa da bin jagoranci da yan'uwa suka yi a lokacin waKi'ar ya yi tasiri, ta yadda maKiya suka kasa samun kafa har ya zuwa lokacin da waKi'ar ta kwaranye.

ADDU'A: Tabbas addu'a makami ce, kuma ibada ce. Akan yi ta a cikin yanayin sauKi ko wahala. HaKiKa halin da yan'uwa Sakkwato suka tsinci kansu a ciki ba wani abu da ya rage masu a lokacin face addu'a. Fahimtar hakan da suka yi, ya sa ba su yi wasa ba. A lokacin addu'a ta zamo ita ce abincinsu, dare da rana, sun duKufa ga yin ta a kodayaushe. Kuma lalle a wannan marra Din sun ga tasirin addu'oi ta janibobi daban-daban. HaKiKa yawaita addu'oin da yan'uwa suka yi a lokacin ya taimaka masu wajen samun nutsuwa. Haka kuma sirrin addu'oin da samun ijaba ne ya sa azzaluman suka kasa ganin bayan yan'uwa, domin duk abin da azzaluman suka yi wa yan'uwa a lokacin kaDan ne, ba shi ne ainihin abin da suka shirya su yi masu ba.

’YANUWANTAKA: Har kullum Dan'uwan addini shi ne Dan'uwa, tabbas yan'uwan Sakkwato sun Dauki darasi babba a wannan bangaren, domin kuwa a lokacin waKi'a ba wani mutum da Dan'uwa ke da siKKa ko aminci da shi sai Dan'uwa (Buraza). Da misali Kila wani zai ce da buraza ni Dan'uwanka ne, zo ga hanya nan ka fita ka zo nan gidana ka kwana, idan har da wani Buraza a kusa, duk shawarar da ya bayar ita Dan'uwan zai Dauka a matsayin mafita gare shi. A yayin hijira da ’yan'uwa suka yi a garuruwa sakamakon matsin da takura da suka fuskanta, haKiKa irin jinKai, soyayya, da Kauna da yan'uwa suka nuna masu, ba a taba ganin irin haka ba a wannan zamani, sai idan an koma a tarihin magabata. Kamar yadda wasu bayin Allah magabata suka yi hijira suka baro garin Makka suka zo Madina suka zauna matsayin waDanda suka yi hijira saboda addini suka rayu a Madina har suka koma ga Allah, haka a waKi'ar Sakkwato akwai yan'uwa da dama da suka hijira a wasu garuruwa, sun bar garinsu na haihuwa saboda addini, kuma za su cigaba da rayuwa a inda suka yi hijira, ba za su dawo ba, mutuwarsu za ta riske su ne a inda suka yi hijira.

HAkURI: HaKuri ne zai sa mutum ya cimma duk wani buri na rayuwa. Yana da wuya, amma in an daure, ko mene zai zo ya wuce. Yan'uwan da suke a wajen Sakkwato, zancensu na Karshe a duk sa'ad da suke magana kan waKi'ar Sakkwato sukan ce da yan'uwa su yi haKuri jarabawa ce, musamman shi kansa jagoran Harka Shaikh Zakzaky (H) a koyaushe wannan kalmar ce yake ambatawa, yake kuma nanata faDarta a duk sa'ad da yake ganawa da yan'uwan yankin Sakkwato ko da sistoci ko da burazun da suke hijira a Zariya. Haka ko waDanda suke a kurkuku, saKon Shaikh Zakzaky (H) gare su shi ne su daDa haKuri, jarabawa ce, kuma yanayin Kuncin da ake ciki ba za a dawwama a cikin sa ba.

Lallai wannan wannan waKi'a ta Sakkwato ba yan'uwa na yankin Sakkwato ne kaDai suka koyi darussa a cikin ta ba, duk wani Dan'uwa da yake amsa sunan Dalibin Shaikh Zakzaky (H) a nan Kasar ko wajenta, ya yi jimami, kana ya shiga damuwa tsawon shekaru na yadda ya ga maKiya Allah sun dira a kan yan'uwansa bisa zalunci. Darasi babba da Kilan kowa zai Kara fahimta kan waKi'ar shi ne shi Azzalumi ba ya da wani suna sai Azzalumi. Kuma Azzalumai na da, da aka karanta a tarihi, da na yanzu, duk Daya ne. Munanan ayyukansu na ta'addanci da rashin imani ga raunana, babu bambanci. Haka ma mummunan Karshen da Allah Ta'ala ya yi masu alKawari zai zamo Daya. Haka makomarsu a Kiyama za ta zamo Daya in har ba su tuba ba.

HaKiKa har a naDe Kasa, tarihi ba zai manta da abin da Alu Wamakko ya yi wa yan'uwa a Sakkwato ba. Dodo ne masha jini, ya kashe yan'uwa, ya daure wasu, ya rusa gidaje da shaguna, ya sanya adadi mai yawa hijira zuwa wasu garuruwa Ketare, ya raba mata da yawa da mazajensu, ya raba ya'ya da ubaninsu, ya raba iyaye da ya'yansu, haka ma bayan rushe gine-ginensu, ya Kwace duk wani fili da suka mallaka, kana ya sa aka Daure wasu shekaru 11 kowanensu a gidan yari, ba tare da la'akari da masu iyali ko Daliban da ke karatu ba. Kan wannan zalunci roKon da muke ga Allah tun lokacin waKi'ar har yanzu shi ne, duk mai hannu ko gudummuwa a kan zaluntar yan'uwa a Sakkwato, ya yi masu sakayya tun a nan duniya kafin gobe Kiyama.