AlmizanAlmizan logo
Jum'a 27 ga Shawwal, 1438. Bugu na 1298 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Mun amince Shaikh Zakzaky ya zama makwabcinmu - Mista Deji Adeyanju

Daga Aliyu Saleh


Maulid Sayyada Fatima

Mista Deji Adeyanju shi ne Shugaban kungiyar fafutikar kare hakkin bil’adama ta ‘CONCERNED NIGERIANS’ da ke hedikwata a Abuja. A cikin wannan hirar da ya yi da Aliyu Saleh, ya yi watsi da abin da Ministan yada labarai, al’udu da yawon bude ido, Barista Lai Mohammed ya fada a hirarsa da gidan talabijin na Channels TV cewa, ba suna tsare da Shaikh Ibraheem Zakzaky ba ne, amma suna ajiye da shi ne a wani gida da suka gina masa saboda sun rasa wanda zai yarda ya yi mukwabtaka da shi. Kuma ya nuna damuwa matuka kan kin bin umurnin kotu da gwamnati take yi. Ku sha karatu lafiya.

ALMIZAN: A wannan makon ne kuka fitar da sanarwar manema labarai, inda kuka mai da wa Ministan yada labarai da al’adu martani kan hirar da ya yi da gidan talabijin na Channels TV da yake bayyana dalilinsu na kin sakin Shaikh Ibraheem Zakzaky, me kuke cewa ne?

MISTA DEJI ADEYANJU: Na farko muna so mu tabbatar wa da al’ummar Nijeriya cewa karya Lai Mohammed yake yi. A maganar da ya yi a Channels TV ya bayyana cewa, wai Shaikh Zakzaky ba yana kulle ba ne a hannun ’yan sand, DSS, ko kuma kurkuku, mu kuma mun karyata shi, mun ce karya ne, saboda muna da mutane a DSS da suka fada mana cewa har yanzu Shaikh yana tsare ne a hannunsu da matarsa, don haka karya Lai Mohammed yake yi. Abin takaici ba yau ne ya fara karya tun da ya hau kan wannan mukamin ba. Kullum yana cikin karya don ya kare gwamnatin nan. Amma gaskiya gwamnati bai kamata tana yi wa jama’ar kasa karya ba.

Abin da ya sa muka ce za mu amshi Shaikh Zakzaky shi ne, mun san cewa maganar da Lai Mohammed ya yi na cewa, ’yan Nijeriya ba su son su zauna da Shaikh Zakzaky da matarsa karya ne. Mu Coordinator dinmu a Kaduna ya shirya don ya zauna da Malam, mambobinmu sun shirya su zauna da Malam, mun ma dauki matakin kama wa Shaikh Zakzaky gida a Kaduna, ko kuma a ko’ina a Arewacin kasar nan na shekara daya, za mu biya, kuma za mu zauna da Malam. Mun shirya mu zama makwabtansa. Don haka muna rokon gwamnatin Tarayya ta saki Shaikh Zakzaky, ta ba mu shi. Mun amince za mu zauna tare da shi.

ALMIZAN: A baya gwamnati tana cewa ta daukaka kara kan hukuncin da aka yanke, yanzu kuma ga abin da Lai Mohammed ya fada, wasu na cewa akwai tufka da warwara ke nan?

MISTA DEJI ADEYANJU: Wane ‘Appeal’ suka yi? Ba gaskiya ba ne, ba su yi wani ‘Appeal’ ba. Gwamnati da kanta ta zo kotu a lokacin da ake shari’ar kafin a yanke hukunci, ta bayyana cewa Shaikh Zakzaky bai aikata laifin komai ba. To wane ‘Appeal’ ne kuma za a yi a kan hukuncin? Gwamnati da bakinta ta bayyana cewa Shaikh Zakzaky bai aikata laifin komai ba. A kotu suka fadi wannan. Mutumin da bai aikata laifin komai ba, amma kuna rike da shi har kusan shekaru biyu? A ina ake irin wannan, in ba a wannan kasar da ba a bin doka ba? A duk duniya ba inda ake yin haka. A ce gwamnati ba za ta bi dokarta ba? A ina ake irin wannan? Ko a ‘Animal Farm’ (Gandun dabbobi) ma suna da doka, ballantana kuma a ce gwamnati ce da kanta za ta rika karya dokar kasa. Idan har gwamnati za ta karya dokar kasa da kanta, ai ba ta da bakin da za ta ce wani dan kasa ya bi doka. Idan har gwamnati za ta karya dokarta, meye ma’anar a ce wani dan kasa ya bi doka? Wannan maganar banza ce, maganar wofi, batun ‘Appeal’ ma bai taso ba, tunda gwamnati da bakinta ta ce Shaikh Zakzaky bai aikata wani laifi ba. ‘Appeal’ na me, kan me?

ALMIZAN: Wannan jinkiri da gwamnati ke nunawa na aiwatar da umurnin kotu, me yake nunawa?

MISTA DEJI ADEYANJU: Abin da yake nunawa shi ne wannan gwamnati ba ta bin doka, ba ta bai wa tsarin mulkin kasar nan wata daraja ba, kuma wannan gwamnati ta cin zalun ce, gwamnatin zalunci ce. Tun da aka kafa kasar nan ba a taba yin gwamnatin da take saba wa doka irin wannan gwamnatin ba. Ita wannan gwamnatin, ita ke da mummunan tarihi na take hakkin bil’adama a kasar nan. Ko lokacin mulkin Soja, kai ko lokacin Janar Sani Abacha ma ba a yi irin haka ba. Abin takaici har kotu ta yanke hukunci, amma gwamnati ba za ta bi wannan umurnin ba. A ina ne ake irin wannan? Ai ko a Afganistan ko Iraki ba a yin irin haka. Ko lokacin da Mu’ammar Gaddafi ma yake kan mulki, ba a yi irin haka ba. Turawa suna cewa ‘Judiciary is the last hope of the common man’ (bangaren shari’a ne fata na karshe ga wanda aka tauye wa hakki). A ce kotu ta yanke hukunci a kan wata shari’a, amma su ki bi? Gwamnati ta fi karfin kotu ne? An zama muna ‘Animal Farm’ ke nan.

ALMIZAN: Wannan dalilin ne ya sa kuka shigo cikin wannan maganar har kuka shirya zanga-zanga kwanakin baya ke nan?

MISTA DEJI ADEYANJU: Tabbas! Wannan shi ne dalilin da ya sa muka shigo cikin maganar ke nan. Kafin kotu ta yanke hukunci, ai ba mu shigo cikin maganar ba. Sai da muka ga kotu ta yanke hukunci, gwamnati ta ki bi, sai muka ga lallai ba mu ga ta zama ba, muka ce ai ba a yin haka. Doka ce ta samar da wannan gwamnatin, don haka dole ne ta bi doka. Idan aka ce kotu ta yanke hukunci a kan magana, wajibi ne gwamnati ta bi wannan umurnin tunda ba wanda ya fi karfin doka, don ta ba da kyakkyawan misali ga ’yan kasa. Abin da ya sa ke nan muka shigo cikin maganar, muka ce wannan ba adalci ba ne. Duk inda aka ji wannan maganar, ba wanda zai goyi bayan gwamnati. Ba za ku zo ku kashe mutane kusan 1,000 ba, ku kashe ’ya’yan mutum shida, ba ku kama makasan ba, sannan ku zo ku ajiye shi da matarsa kawai. Ai wannan zalunci ne. Shi ya sa muka shigo cikin maganar.

ALMIZAN: Ke nan dai ba gaskiya ba ne da gwamnati ta ce Shaikh Zakzaky ba a tsare yake ba?

MISTA DEJI ADEYANJU: A’a ba gaskiya ba ne. Wannan ko yaron da aka haifa jiya ya san wannan ba gaskiya ba ne. Idan kuma maganar gaskiya ce, me ya sa ba sa barin ’yan uwansa su je wajensa su gan shi? Me ya sa Lauyoyinsa ba za sa zuwa wajensa? Me ya sa Almajiransa ba za su iya zuwa wajensa? Me ya sa mu ba za su bar mu, mu je wajensa ba? Me ya sa suka hana ’yan jarida su je wajen Shaikh Zakzaky da matarsa? Wannan maganar banza, maganar wofi ce.

ALMIZAN: Wannan fafutika da kake yi ta haifar maka barazana a rayuwarka, har kwanakin baya an kama ka a kan wannan batun, wannan bai sa ka firgita ba?

MISTA DEJI ADEYANJU: Bai tsorata ni ba. Ai ba za mu bari ba har sai an yi adalci. A duk duniya duk wanda zai fito ya rika fada da zalunci, wajibi ne ya fuskanci irin wannan tsangwamar. Zai fuskanci cin mutunci, bata suna, dauri, kai har ma da kisa. Duk wanda yake so ya bi gaskiya, sai ya shirya wa wannan. Abin da nake so ’yan IMN su sani ke nan, kar su taba gajiyawa a kan wannan fafutikar da suke yi, su ci gaba da tsayawa a kan gaskiya, su ci gaba da addu’a. Duk wani azzalumi, tun zamanin Fur’auna, zai yi iyakacin abin da zai iya ne, Allah ya fi karfin azzalumai. Abin da ya kamata dukkan mu mu sani ke nan. Don haka kar su gaji, mu ma ba mu za mu gajiya ba. Za mu ci gaba da gwagwarmayar neman tabbatar da adalci a tare da su.

ALMIZAN: Daga karshe me kuke so gwamnati ta yi ne?

MISTA DEJI ADEYANJU: Muna rokon gwamnati ta saki Malam. Mun shirya mu amshe shi duk lokacin da ta bi umurnin kotu ta sake shi. Mun shirya mu zama makwabtansa, shi da matarsa. Mun san cewa akwai dubban mutane da suke shirye su zama makwabtan Shaikh Zakzaky a ko’ina a fadin kasar nan.

ALMIZAN: Mun gode.

MISTA DEJI ADEYANJU: Ni ma na gode.

…Gwamnati za a zarga kan matsalar

-Alhaji Ibrahim Musa Gashash

Daga Aliyu Saleh

Shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya ta National Tranquility Movement (NTM) da ke Kaduna, Alhaji Ibrahim Musa Gashash, ya yi zargin cewa matsalar satar mutane da garkuwa da su domin neman kudin fansa da ake fama da ita a kasar nan, laifin gwamnati ne, domin ita ke da alhakin magance matsalar.

Alhaji Ibrahim Musa Gashash, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa, bayan ya shirya wa jama’a buda bakin Azumin watan Ramadan, ya yi watsi da zargin da ake yi wa Fulani makiyaya a kan cewa su ke da hannu a kan wannan lamarin.

Ya ce wannan matsala ce da za ta zama ruwan dare a tsakanin duk kabilun kasar nan. “An tabbatar Fulani ne suke yi wannan abin? Mu mun san an kama wadanda ba Fulani ba, ba ma Musulmi ba ne. Saboda haka zarga wa Fulani wannan matsalar, neman a yi masu yarfe ne don a samu biyan bukata”.

Alhaji Gashash, wanda ya yi zargin cewa akwai sa hannun wasu manya a kan wannan matsalar da garkuwa da mutane, ya jadadda cewa; “Abin nan da ake yi ba kananan mutane ne ke yin sa ba, akwai manyan da ke bayansa. Na tabbatar da haka. Domin matsalar nan na san ta ciki da waje.

“Bafullatani ba shi da hanyar da zai samarwa kansa bindigogin da wadannan barayin ke amfani da su. Bai san yadda zai sarrafa ta ba sai an zo an koya masa. Su wa suka zo suka koya masa? A ina yake samo bindigar? A binciki wannan tukunna. In aka toshe wannan kafar, watakila Fulanin za su rasa harsashi, za su rasa bingida”.

Ya ci gaba da bayyana cewa; “Ta ina suke samun harsashin nan da suke amfani da yau da kullum? Idan kuwa haka ne, gwamnati ce ta yi sakaci har yake shigowa cikin al’umma. Kafin a zargi Fulani, ko wani mai yin ta’addanci, ko mai garkuwa da mutane, sai a fara zargin gwamnati da ta yi sakaci har abu ya kawo haka.

Ya ba da misali da rikicin da ake yi a kudancin Kaduna, wanda aka zargi Fulani da kabilun da ke zaune a wannan yankin; “An kama mutanen da ba su da alaka da wannan wajen. Me ya kawo su? ’Yan siyasa ne suke ba su makamai don su je su tayar da hankali, don su samu biyan bukata. Manyanmu su fito su yi maganar gaskiya, sun san komai. Amma don bai shafe su ba, kowa ya kame bakinsa ya yi shiru.

Da yake tsokaci a kan hanyar da za a shawo kan matsalar, Alhaji Ibrahim Musa Gashash ya bayyana cewa; “Za a shawo kan matsalar ne in an zargi gwamnati don ta tashi ta yi aikinta yadda ya kamata. Ai zaman lafiyar mutane, kwanciyar hankali da arzikinsu duk yana wuyan gwamnati ne. In ba za su iya ba, sai su sauka mu kawo wasu”.

Alhaji Ibrahim Musa Gashash, ya yi wa Musulmi nasiha a kan muhimmancin hadin kai a tsakanin su. “Ina kira ga Musulmi su nemi hadin kai a tsakanin su. Rabe-raben kai saboda Dariku ba alheri ba ne a tsakanin mu, fitana ce wacce Allah bai son ta. Wajibi ne kowa ya sani daidai abin da wuyansa ya dauka, da shi zai je lahira, da shi za a yi masa hisabi.

“Don kana wata Darika, Allah bai ba ka aikin tilasta wa mutane su shige ta ba. Saboda haka duk wanda yake addini, ya yi shi tsakanin sa da Allah. A kan haka Allah zai yi masa hisabi. Ina so Musulmi su kawar da bambancin da ke tsakanin su, su zauna laifiya da juna”.

Tun a farko ya bayyana dalilin kiran mutane zuwa buda baki; “Cin abincin buda baki na Azumi, na farko lada ne. Na biyu kuma mutanen da ake tare da su tsawon shekarar da ta gabata, zai yi kyau a koyaushe a sadu, a samu lokaci tare da juna domin a tattauna”.

Da yake magana a kan shirin da yake yi na tsara wani shiri don wanzar da zaman lafiya a kasar Mali kuwa, Alhaji Ibrahim Musa Gashash, ya bayyana aikin da ya yi na gayyato wasu ’yan Mali da hadin kan ’ya’yansa don su tsara jadawalin wanzar da zaman lafiya a kasar, ciki har da shirya wakoki.

“Akwai abokina dan Mali, wanda ke zaune a Faransa da na gayyato da shi suka hadu da yaron wajena; Usman, suka shirya waka ta wanzar da zaman lafiya. Muna fata wannan wakar ta isa ga kunnuwan wadanda abin ya shafa. Na sani ta hanyarku (’yan jarida) sakon neman zaman lafiya a Mali zai kai inda ake so ya kai”, ya jadadda.