AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

’Ya’yana sun gaya min lokacin da sojoji suka harbe su a ciki - In ji Malam Bashir Taura Kano

Daga Ibraheem El-Tafseer


Imam Aliy

A kwanakin baya ne Wakilinmu na Suleja Magaji A. Idris ya sami tattaunawa da Malam Bashir Taura Kano, mazaunin garin Suleja, kuma mahaifin Shahidan waki'ar Zariya biyu. Wato Shahid Muhammad (Abba), da Shahid Hujjatullah. Malam Bashir Taura ya yi bayanai masu amfanarwa. Sai wanda ya karanta ne zai fahimci hakan. Ga tattaunawar kamar yadda aka yi ta:-

AL-MIZAN:- Masu karatunmu za su so ka gabatar da kanka.

BASHIR TAURA :- Sunana Bashir Muhammad Taura. Mahaifin shahidai biyu,

Abba, wanda sunan mahaifina ne aka sa masa (Muhammad). An haife shi a shekarar 1994. Sai kuma Hujjatullah, shi kuma an haife shi a shekarar 1997.

AL-MIZAN:- Yaya za ka kwatanta mana halayen Shahidan nan guda biyu?

BASHIR TAURA:- Daga cikin abin da zan iya fada a matsayina na mahaifinsu, akwai irin ashariya da yara kan yi in suna kanana, to su ban taba ji ba a tsakanin su. Kuma ban taba yin tir da dabi'unsu ba. Shi Abba tun daga yarantarsa har zuwa girmansa, Allah ya yi shi mutum ne mai kunya. Ko baki aka yi a gida, sai ka ga ya koma daki ya yi zamansa. Ko kuma ma ya fita gidan gaba daya. Mafi yawan lokutansa dai yana daki. Ko dai yana tunani, ko kuma yana karatu. Kuma tunda ya taso da ma karatu ya sanya a gaba. Sukan je makarantar boko tun daga safe har Azuhur. Bayan sun yi Sallah, sai su tafi makarantar Arabiyya har zuwa karfe shida na yamma. Haka kuma da dare za su tafi makarantar Islamiyya. Haka suke rayuwarsu.

AL-MIZAN:- A bangaren karatun boko, meye darajar karatunsu?

BASHIR TAURA:- Shi Abba yana ‘School of art and Managment studies’. Yana ‘200 level’ dinsa ne. Shi kuma Hujjatullah yana ‘Fudiyya Science Callage’, wanda Shaikh Turi ya bude din nan.

AL-MIZAN:- Ko lokacin da suke Zariya, ma'ana lokacin waki'a, ko kun yi magana da su?

BASHIR TAURA:- "E". Lokacin da aka harbe su suna tare da kaninsu Haidar. Tunda suka tafi ranar Asabar wayarsu babu caji. Kodayake shi Abba bai tafi da waya ba. Hujjatullahi ne ya tafi da waya. Na yi ta neman su a waya ban same su ba. Sai daga baya da kaninsu Haidar ya dawo yake ce mana sun sa wayarsu ne a caji a wani shago. Ya ce, mana lokacin da Sojojin suka zo, sai suka dinga jeho bom a shagunan da ke wajen. A nan ne duk shagunan suka kone. To, sai ranar Lahadi da misalin karfe goma na safe na ga an kira ni da wata lamba. A daidai lokacin muna shirin zuwa Zariya din. To, da na dauki waya sai na ji muryar Hujjatullah ne. Ina jin haka sai na sanya wayar a ‘recording’. Shi ne yake fada mani cewa, ya kira ne ya fada mani cewa an harbi Yayansa a ciki, shi kuma an harbe shi a ciki da hannu. Ya ce mu yafe musu. Sai Allah ya sada mu da alheri. Ni kuma na ce na yafe musu. Har yake ce mani kada in fada wa mahaifiyarsu. Shi ne ma yake fada mani cewa Shaikh Turi ya yi Shahada. Ko shi kanin nasu wanda ya dawo, ya ce, suna tare da Shaikh Turi. Shaikh Turi yake ce musu yau ba maganar harbi da danko ba ce. Sai Shaikh Turi ya dauki dutse ya yi kabbara ya jefa musu. Su ma suka dauka suka yi kabbara suka jefa musu. Sai aka harbi Shaikh Turi. Ya fadi yana ‘Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Raji'un’. Shaikh Turi ya sake mikewa, la'anannun Sojojin nan suka sake harbin sa ko a hannu ne? Sai ya sake faduwa! To, sai su Hujjatullah suka kwanta suna jan Shaikh Turi. Sai suka ji ya yi musu nauyi, domin a kwance suke jan sa. Sai suka tashi tsaye. To, a nan ne aka harbe su dukkan su.

AL-MIZAN:- Ko bayan Shahadarsu an sami wadanda suka yi mafarki da su?

BASHIR TAURA:- A makarantarsu ta allo da suke zuwa, wato makarantar Alaramma Malam Salihu, akwai wani yaro Abdullahi da ya yi mafarki da shi Hujjatullah. Da yake shi da ma abokin Hujjatullah din ne. Ya yi mafarki da shi ya zo cikin fararen kaya, da babbar riga. Tare da taron mutane masu yawa ana bin sa kamar Gwamna. Ya ce Hujjatullah ya zo wajensu da wani flask na ‘silver’. Ya kira Abdullahi ya ba shi ‘flask’ din. Ya ce masa su je su ci abin da ke ciki. Ya ce ko da suka bude, sai ya ga soyayyen nama ne. Ya ce masa ya ci. Ya kuma mika wa sauran. Ya ce, da aka gama, sai Shahid ya ce su kawo masa ‘flask’ dinsa. Sai suka ce masa "Shahid bari mu raka ka". Da suka raka shi, sai suka je wani gida. Gidan kamar ma ‘glass’ ne. Da suka je, sai Shahid ya fara tattaka matakalar hawa gidan. Ya ce musu su ma su hawo matakalan. Sai suka kasa. Ya sake ce musu su hawo mana. Sai suka ce masa ba za su iya hawa ba. Sai ya ce, musu to su miko masa ‘flask’ dinsa. Ya biyo matakalar shiga gidan, ya dawo ya karbi ‘flask’ dinsa. Har zai tafi, sai ya sake tambayar su,, "Ba za ku iya hawowa ba?" Suka ce masa "Ba za mu iya ba". Sai ya karbi ‘flask’ dinsa ya juya. Yana ta hawa matakalar shiga gidan nan har ya bace musu.

Shi kuma Abba kwanan nan mahaifiyarsa ta yi mafarki da shi. Ya zo a irin motar nan ‘Luxurious’. Ta ce, su biyu ne a gaban motar. Sai Shahid ya bude kofar motar yana ce wa danginsa su zo su shiga motar. Akwai wata matar abokina da suke ce mata Umma. Shahid Abba yake ce mata "Umma ki zo mu shiga". Haka ya kwashi mutane da yawa a wannan motar.

AL-MIZAN :- Wane kira kake da shi ga azzalumar hukumar da ta aikata wannan ta'addanci ga wadannan 'ya'ya naka?

BASHIR TAURA:- To, ai ita hukuma kunnen kashi ke gare ta. In ma an fada ba ji za ta yi ba. Sai dai kawai don a sauke uzuri kamar yadda Sayyid (H) yake cewa, suna da hakkin mu fada musu gaskiya. Haka kuma wannan waki'a da ba a yi ta ba, da ba mu kawo inda muke a yanzu ba. Yin wannan waki'a, sai ya zama gagarumar nasara wanda Harka ta samu. Gagarumar nasara ne ga Sayyid (H). Gagarumar nasara ce mabiyansa suka samu. Kuma da ma ya zo a cikin hadisi cewa manya-manyan jarrabawowi suna tare da manya-manyan bala'o'i. Domin in ka duba yanzu yadda jama’a ke yin tururuwa zuwa ga wannan Harka, suke tururuwar bincike a kan Harka, da sauran al'ummu. To, wannan nasara ce. Harka yanzu ta fantsama a duniya, ba ma Afirka ba. Babu wani bangare yanzu a duniya da ba a san mece ce IMN ba. Kuma ba a san waye Sayyid Zakzaky (H) ba. Ko kuma a ce ba a san me yake kira a kai ba. Kuma duk duniya a yanzu kokari ake a samu jawabansa, don jin abin da yake cewa. Kuma su ji abin da ya sa aka yi masa abin da ake yi masa. Saboda haka ’yan’uwa mu dake. Kuma mu da muke a nan kalubale ne a kanmu. Mu sake rungume Jagoranmu. Mu yi kam-kam da wannan da'awa. Duk wanda yake sako-sako, to zai zo ya zamo dan rakiya. Kana gani wanda ba Musulmi ba zai zo ya Musulunta ya ba da gudummawar da kai ba ka ba da ba. Don haka kowane dan’uwa ya tsaya ya duba, cikin baiwowin da Allah ya yi wa dan’adam mene ne Allah ya yi masa baiwa da shi? Tunani ne? Ilmi ne? Wata sana'a ce? Dukiya ce? Duk abin da Allah ya yi maka baiwa da shi ka yi kokari ka sadaukar. Domin abin da za ka iya yi fa shi ne nasararka. Idan ba ka yi ba, sai ka yi nadama. Saboda haka dan’uwa ya dage iya iyawarsa. Kuma ya yi yadda ya kamata.

ALMIZAN: Malam mun gode.

BASHIR TAURA:- Ni ma na gode.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron