AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

DA WANE LAIFI SOJOJI SUKA KASHE ’YAN SHI’A A ZARIYA 23

Daga Aliyu Saleh


Imam Aliyu

AMSAR TUHUME-TUHUME EL-RUFA’I

Kamar yadda muka yi alkawari a baya cewa za mu ba Gwamnan jihar Kaduna amsa a kan wasu tuhume-tuhume 16 da ya yi wa Harka Islamiyya, wadanda ba su da tushe balle makama, amma kafin mu fara ba shi amsa, bari mu yi nazarin maganganun da wasu mutane suka fada a kansa. Wannan zai bai wa masu karatu saukin gano ko tuhume-tuhumen nasa na da rauni ko inganci.

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ubangidan Nasiru El-Rufa’i ne a siyasance. Shi ya dauko shi ya ba shi mukamin Shugaban Hukumar sai da kadarorin gwamnati, daga bisani ya yi masa Ministan Abuja, wanda ya yi sandiyyar samun duk wasu kudade da kadarorin da ya mallaka a gida da waje; amma ga abin da ya kira shi a cikin littafinsa da ya rubuta mai suna MY WATCH. “Nasiru Ahmad El-Rufa’i za a iya bayyana shi a matsayin tantirin makaryaci (pathological liar), wato mutum ne marar tunani da hangen nesa, wanda karya ta zama jinin jikinsa, mai nuna kiyayya a fili, marar son zaman lafiya, ga kokarin haddasa kiyayya da gangan”.

Shi ma tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya taimaka masa a rayuwa. Ya shaida wa BBC cewa, Nasiru El-Rufa’i mutum ne mai butulci, wanda bai san darajar mutane ba. Kuma ya kware da kuruciyar bera. Bai girmama na gaba da shi, kullum burinsa ya tadiye kafar wanda ya taimake shi, kuma ya ciji hannun da ya ciyar da shi.

Yayin da su ma matasan jam’iyyar PDP da ake kira ‘Peoples Democratic Party National Youth Frontiers’ (PDPNYF) suke mai da martani ga Nasir El-Rufa’i a shafinsu na Twitter dangane da maganganun da ya yi a kan Atiku Abubakar cewa suka yi. “Tarihi bai ruwaito wani mutum mai iya tsara maganganun da ba na gaskiya ba, kuma wanda ya kware wajen iya butulci kamar Nasir El-Rufa’i. Atiku ne ya sa aka nada shi Darakta a Hukumar sayar da kadarorin gwamnati, (BPE), daga bisani aka nada shi Minista, amma dubi abin da yake yi masa”.

Justice Bashir Sambo, 76, tsohon Shugaban kotun da’ar ma’aikata (Code of Conduct Tribunal) yana cikin abokan Mahaifin Nasiru El-Rufa’i. Yana cikin wadanda suka taimake shi ga taka duk wani matsayi na rayuwa. Amma kowa ya ga yadda jaridu (ciki har da Daily Trust) suka buga hotonsa yana zaune, yana kuka a kan kayansa, bayan El-Rufa’i ya sa an watso masa su waje a cikin watan Agusta, 2016 daga gidan da yake zaune a No1, Aso Drive, Maitama District, Abuja, saboda wai wa’adin zamansa a gidan ya kare. Iyalansa suka ce wannan cin mutuncin na cikin dalilin kamuwarsa da ciwon zuciyar da ya yi sanadiyyar rasuwarsa ranar 29/04/2007.

Akwai mutanen da suka taimaka masa a siyasance, hatta a lokacin da ya fito takarar Gwamna, amma yanzu haka ba sa ga-maciji da juna. A cikin mutanen akwai Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, tsohon Shugaban PDP na jihar Kaduna, Alhaji Yaro Makama Rigachikum, Shugaban gidan Talabijin na DITV da Alheri Radio, Dakta Hakeem Baba Ahmad, Shugaban gidan Radio da Talabijin na Liberty, Dakta Tijjani Ramalan, tsohuwar Shugabar mata ta APC, Hajiya Hafsat Baba da sauransu. Yanzu haka duk yana takun-saka da su.

A makon jiya ma an ji Shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma, Barista Inuwa Abdulkadari, wanda shi ma yana cikin wadanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin ya zaman Gwamna, yana kokawa da barazanar da El-Rufa’i ya yi masa na dukan sa a gaban Gwamnonin Arewa, da kuma hana shi shiga garin Kaduna. Ya yi masa wannan barazana ne saboda ya ce ya yi amfani da jagoranci mai kyau wurin ganin ya sulhunta fitintinun da ke cike da jam’iyyar tasu ta APC a jihar Kaduna.

Ita kanta jam’iyyar APC din a jihar ya kwace ta ya mai da ta gidan gwamnati, wanda hakan ya tilasta wa jiga-jigan jam’iyyar na jihar Kaduna da suka jawo shi cikinta a lokacin yana cikin PDP domin ya yi takara, yanzu suka balle suka kafa wata sabuwar APC da suka kira ‘APC Akida’.

Wani abu da zai sa mu kara gane wane ne Nasiru El-Rufa’i shi ne; a ranar Alhamis 28 ga Jimada Sani 1436, gab da za a gudanar zaben Gwamna, ya yi hira da kafafen yada labarai da ke garin Kaduna guda shida da suka hada da FREEDOM RADIO, NAGARTA, KARAMA, KADA FM, LIBERTY da ALHERI RADIO, inda a ciki ya bayyana wasu manufofinsa da kuma wanke kansa a kan wasu zarge-zarge da ake masa.

A karshen shirin, fitaccen Bawahabiye mai yaki da Shi’a, kuma Shugaban Sashen shirye-shirye na gidan RADION FREEDOM, Abubakar Jidda Usman, ya yi masa wata tambaya cewa; “Wasu na zargin ko kai ne Abdullahi Bn Saba’a?” Cike da mamaki El-Rufa’i ya amsa da cewa; “Waye Abdullahi Bn Saba’i!? Sai Jidda Usman ya ce; “Maganar Shi’a ce ake tambaya, kuma shi ne Shugaban Shi’a”.

Ga amsar da Nasiru El-Rufa’i ya ba shi. “To ban sani ba, kamar yadda na ce ita wannan gwamnati ta PDP idan ta fito da wani sharri aka warware, sai su fito da wani. Ina da labarin wai ana cewa ni dan Shi’a ne, kuma abin da ake bayarwa a matsayin hujja shi ne an gan ni da Alzakzaky, na je na yi masa ta’aziyya. Ban sani ba ita gwamnatin da yake ba ta da imani ba ta je ta yi wa Alzakzaky ta’aziyya ba da aka kashe ’ya’yansa guda uku, amma ni dai duk mutumin da a rana daya aka kashe masa ’ya’ya uku, kowane irin mutum ne, zan je in ce Allah ba da hakuri, Allah ya ji kan su, Allah ya ba da hakuri da dangana. Abin da na je na yi ke nan a gidan Alzakzaky.

“Kuma Alzakzaky mun yi makaranta da shi, mun yi University yana gabana shekara daya, mun yi Musulmi Student Sociaty (MSS) tare da shi, saboda haka mutum ne wanda na san shi shekaru 40 da suka wuce. An kashe ’ya’yansa guda uku a rana daya, na je na yi masa ta’aziyya. Na san zafin haka, domin ni kaina Allah ya jarabce ni ’ya’yana guda biyu Allah ya dauki ransu. Daya da aka dauka, sai da na yi kwana da kwanaki ina bakin ciki ina kuka, balle a ce an kashe ’ya’yanka guda uku a rana daya. Duk wanda ya ce wanda aka kashe ’ya’yansa guda uku, kada a je a yi masa ta’aziyya don wani dalili, to shi ne yake da busasshiyar zuciya, ba shi da imani, kuma na bar shi da Allah. Amma ni duk wanda ya ce wai don na je na gai da Alzakzaky na zama dan Shi’a, Allah ya isa. Na bar shi da Allah”.

Kamar yadda ya fada da bakinsa, wannan tuhumar ta biyo bayan ganin sa ya je gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky ne domin yi masa ta’aziyyar rasuwar ’ya’yansa uku da da Almajiransa 31 da Sojoji suka kashe ranar Juma’a 28/7/2014. Gwamnan ya kai ziyarar ne ranar 08/08/2014. Nan da nan Malamai (Wahabiyawa), wadanda a cikin hirar ya ce PDP ta ba su miliyoyin Nairori don su bata shi, suka dauki hotonsa tare da Malam suka buga fasta suka yi ta yadawa a garin Kaduna, suna cewa El-Rufa’i ya zama dan Shi’a, don haka kar a zabe shi. Amma sai wannan abin da suka yi ya kara masa farin jini.

A lokacin ni na rubuta labarin buga fastar da kuma yada ta da aka yi a jaridar ALMIZAN. Yayin da muka kai wa Shaikh Zakzaky ziyara bayan jaridar ta fito, ya yi mana fada sosai, ya nuna ba haka ya kamata a rubuta labarin ba. Ga abin da yake cewa; “Aliyu Saleh na karanta labarin da ka rubuta a kan ana zargin Nasiru El-Rufa’i ya zama dan Shi’a. Ba haka ya kamata ka rubuta shi ba. An fada maka mutane na kyamar Shi’a ne? Ai wasu ’yan tsiraru ne ke adawa da ita. Don an danganta wa mutum Shi’a ba bakin jini zai yi ba, sai dai ya kara farin jini”.

Da yake ba duk mutane ne suka san irin taimako da gudummawar da Shaikh Zakzaky ya bai wa Gwamna Nasiru El-Rufa’i ga kai wa ga wannan matsayin ba, bari mu haska su kadan. Bayan zaben, Shaikh Zakzaky ya fada mana baki da baki cewa Mahaifiyar El-Rufa’i ta kwaso danginta na kusa sun zo har gida sun yi masa godiya, saboda sun ji dadin irin gudummawar da ya bayar wajen kaiwar sa ga wannan matsayin na Gwamna a jihar Kaduna.

Kuma dama tun asali Mahaifin Nasiru El-Rufa’i, wanda yake Malamin Gona ne, dan unguwar Kwarbai ne cikin birnin Zariya, kuma abokin Mahaifin su Shaikh Zakzaky ne, kamar yadda Malam Badamasi Yaqoub ya tabbatar mana. “Zan iya cewa Mahifinsa bai da abokin da ya kai Mahaifinmu. Mahaifiyar El-Rufa’i ’yar Sakkwato ce, a can Mahaifinsa ya auro ta lokacin da aka tura shi aiki can, amma ita ma Mahaifanta ’yan Zariya ne”.

Duk da yake ba a Zariya aka haifi Nasiru El-Rufa’i ba, a Daudawa ta jihar Katsina ne, kuma a can ya taso kafin ya shiga makaranta (saboda yanayin aiki da ya kai Mahaifinsu can), amma Barewa College ya yi, daga bisani ya shiga Jami’ar ABU, wanda ya sa yakan ziyarci unguwar Kwarbai, musamman idan guzurinsa ya kare. Daga cikin masu tallafa masa da kudi da kayan abinci har da Mahaifiyar su Shaikh Zakzaky, Malama Salaha (Hari Jimo), musamman da yake ta yi fice a wannan unguwar a lokacin wajen tallafa wa marasa galihu da kuma yi wa mutane addu’a.

Amma aikin farko da Gwamnan ya yi bayan rushe gidajen da ke jikin makarantar ALHUDAHUDA, sai kuma rushe gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky da ke Gyallesu, makarantarsa (Husainiyya Bakiyyatullah), kabarin Mahaifiyarsa da ke Jushi, Jannatud Darur Rahama (inda aka binne wadannan ’ya’ya ukun) da Fudiyya Islamic Center da ke Danmagaji. Daga bisani kuma ya je ya rushe Fudiyya Zariya da ke Babban Dodo, Zariya ba tare da wani dalili ba.

Wannan ya faru ne bayan an harbi Shaikh Zakzaky a idonsa, katare da hannu, bayan an harbe ’ya’yansa uku; Hammad, Ali da Humaid a gabansa da ta kuma dan dan uwansa, Shaikh Abdulkadir, wato Shamsuddeen, tare da kona Yayarsa, Hajiya Fatima (Gogon Kaura) da ranta, bayan an harbe Almajiransa sama da 1,000.

Har yau din nan Nasiru El-Rufa’i ba kawai bai fito ya nuna alhinisa da abin ya faru ba ne, balle ya isar da ta’aziyyarsa ga iyalai da ’yan uwan wadanda aka yi wa kisan gilla aka binne su cikin dare a rami daya, yana daukar duk wasu matakai da yake ganin zai iya dauka ne don ganin ya bice ambaton Shaikh Ibraheem Zakzaky da da’awarsa da ya kwashe shekaru 40 yana yi. Don haka ba mamaki idan har irin wannan mutumin ya yi irin wadannan tuhume-tuhumen.

Za mu ci gaba insha Allah.