AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Shahadar Shahid Abdulkadir ‘Escort’


Maulid Sayyada Fatima

> ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!’ Ya masu karatu! Hakika ranekun 12 zuwa 14 ga watan Disambar 2015 na daga cikin kwanakin da tunanin al’amuransu ba za su taba iya gushewa a zuciyata ba har karshen numfashina. Saboda a wadannan ranekun ne muka rasa 'yan’uwa na imani, ’yan’uwa na Wilaya, ’yan’uwa na gwagwarmayar Harka Islamiyya a karkashin jagorancin kiran Sayyid Zakzaky (H) sama da mutane dubu (1000+) a matsayin zababbun shaidu (Shahidai) da za su zama shaida a gaban Allah (T), a tarihin nasarar Harka Islamiyya a kasar nan, nan gaba insha Allahu.

Khadimin Sayyid Zakzaky (H), Shahid Abdulkadir Muhammad (Tekon), sunansa na kabila "Nma". Iyayensa biyu mutanen cikin garin Bida ne, wanda a sakamakon aiki, Allah ya mai da mahaifinsa da zama a garin Minna, babban birnin Jihar Neja. An haifi Hadimi Shahid Abdulkadir Muhammad a ranar 15 ga Yuli, 1974. Ya yi karatun Firamarensa a Makarantar Kuyambana Firamare a shekaran 1981-1986.

Ita ce makarantar da Sayyid Zakzaky ya gabatar da wa’azin dare a Minna a 2003. Daga nan ya sami ci gaba da karatun Sakandarensa, a Makarantar Je-ka-ka-dawo ta Unguwar Maitumbi da ke cikin garin Minna, a shekarar 1987-1994.

Ni, tun a shekarar 1994 ne, Allah ya hada shakuwata da Hadimi Shahid Abdulkadir. A lokacin da ya yi ta kokarin neman gurbin ci gaba da karatun gaba da Sakandare. Na rike shi a matsayin daya daga cikin dan’uwana mai jin harshen Hausa (tunda ni cikin kasar Hausa na girma), kuma wanda ya fahimci kiran su Sayyid (H). In na je Minna, a dakinsa nake sauka har zuwa 1995 da na san dakinsa ya zo ya zama Markaz din farko a Minna. Na kara shakuwa da Shahid Abdulkadir, a sakamakon kwazonsa na wasanin motsa jiki ta Karet da Tekondo. Mukan je gidan wasa na ‘123 quarters’ da ke nan Minna. Baya ga haka muka zo muka yi aikin Harisanci tare.

Tun daga 1995, duk wanda ya ga Shahid Abdulkadir a Zariya, za ya gan mu a tare. In daga Minna ne zai je Zariya, sai ya biya min ta Markaz din Suleja, mu je tare. In kuma ni, daga Bida na taso na je na same shi a Minna, to, mukan bi jirgin kasa ne zuwa Kaduna, sannan mu bi gidan dangi don neman guzurin yadda za mu je mu rayu a Zariya. Bayan fitowar Sayyid daga kamun Abaca, Shahid yakan je ya yi kwanaki a Zariya, lokaci bayan lokaci don horas da Harrisawa wasannin motsa jiki, saboda ya kai matakin "Black belt," duk da dan tsohon Shugaban kasa IBB, ta hannun wasu abokanensa sun nemi alfarmar Shahid da ya zama ‘body guard’ din Muhammad din IBB.

A shekarar 2000, da aka assasa ‘Medical Team’, mun kasance cikin Harrisawan da aka assasa ‘Medical team’ (Isma), da suke ba da gudummawa ta janibin kula da kiwon lafiya, a yayin Muzaharori da sauran tarukan Harka Islamiyya.

YA FUSKANCI JARABAWOWI

Daga cikin jarabawar da Shaihid Abdulkadir, ya fuskanta ta hada da kuncin tsadar rayuwa, tsangwamar dangin iyaye (saboda mahaifinsa ya rasu tun yana dan matashi) da kamu kamar yadda na ambata a sama cewa, dakunan gadonsa, ciki da falo da ke wajen gidan, su ne cibiya da masaukin baki na farko a Da’irar Minna (MARKAZ). Tun bayan wata Ijtima da aka yi a unguwar Chanchagan Minna, bayan tawayiyya, wadda a kullum duk da babu, yakan yi kokarin ganin ya fita kunya a kan dan abin da zai dinga karrama baki na abinci. Har na zo na ba shi shawara, ya fi mai da hankali a kan sababbin fuskar baki, a kan wadanda su sana'a ta kawo su kawai.

Wani abin da ba zan manta ba da Markaz din Shahid Abdulkadir, shi ne, wani da ya ce ya Musulunta kuma ya nuna yanà da sha'awar Harka, ana ta zaman ibada tare da shi dare da safiya, an saki jiki da shi, kwatsam, wata rana bakin ’yan’uwa da suka zo kasuwanci, ya tattara dukkanin kayan kudin kasuwancinsu da wasu muhimman kayan dakin, ya kara gaba abinsa, har yau .

A kullum dangin mahaifi da mahaifiyarsa cikin tsangwamar sa suke a kan yadda yake ta tara sababbin fuskokin baki a dakinsa kullum. Amma ko kulawa ba ya yi. Don shi daga cikin dabi’arsa yana da sanyin jiki wajen magana (a wasu lokutan ni nake zame masa kakakin magana a cikin dangi). Na tsaya masa a wajen neman aure har sau uku, Allah bai nufa ba. Amma duk da yawan matsin lamba bai sa ya kariya ba, don har ya zuwa rubuta wannan rubutun akwai ’yan’uwan da ke zama a cikin gidan tare da iyayensa.

A shekara 21 da suka wuce, lokacin waki'ar Abaca, lallai Jahiliyya sun sa wa gidan ido sosan gaske, kuma cikin ikon Allah, Allah ya dinga tseratar da shi har zuwa lokacin da aka yi yunkurin kama Almizan a Minna. Amma, shi Shahid Abdulkadir da wani marigayi Mal Abdullahi unguwar Daji, jami'an tsaron farin kaya na SSS sun sami tafiya da su. A daidai lokacin wannan rubutun na waiwayi Editanmu don ya kara tuna min wasu lamurran gudummawar Shahid Abdulkadir a 1996. Shi ma ya yi ajiyar zuciya, ya mika ni ga Amininsa, Mal. Umar Ciroma ta waya.

Ya yi min matashiya dangane da irin gudummawar da Shahid Abdulkadir, ya bai wa Harkar nan a bangaren Almizan. "Ai, a 1996-1997, duk wata Almizan da aka buga, kashi casa'in na nasarar fitowar jaridar izuwa harhada ta, tare da rarraba ta zuwa fadin garuruwan kasar nan, duk tsayuwar kokarin gudummawar Shahid Abdulkadir ne." Mal Umar Ciroma ya kara da cewa, "a lokacin da jami'an tsaro suka gano mu a Minna, sun tara dukkanin masu kamfanin Madabba'ar buga takardu suka ja kunnensu da cewa, duk Madaba'ar da aka rutsa da sunan buga wa Almizan jarida, za su kama su tare da rufe Madabba'ar. Amma, da taimakon Allah da basirar Shahid Abdulkadir, a kan sanayyar wasu aka mai da buga jaridar karkashin kulawar ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Neja. Su jami'an tsaro sun hana masu aikin Madabba'a kasuwanci, kuma kasuwancin ya koma fadar Gwamnatin Jihar Neja".

Sai kamun sa na biyu, sakamakon yadda na ce yakan yawaita zuwa Zariya a kai, a kai don horar da ’yan’uwa Harisawa wasanin motsa jiki, a daidai lokacin ne aka yi wata waki'a da ’yan’uwan yankin Makarfi a shekarar 2000, wadda su Sayyid suka tura Mal. Haruna Abbas zuwa garin don ya je ya binciko, shi kuma Mal Haruna Abbas sai ya ce, Shahid Abdulkadir, ya zo ya raka shi. To, daga shiga garin, jami'an tsaro suka cafke su, sai gidan yarin Kaduna. A wannan lokacin ne wayata ta fako da su Sayyid Zakzaky (H).

Da na ji labara, a lokacin ina tsaron dakin shan magani na Kantin Sauki da ke Suleja, "Batula Chemist." Akwai waya a shagon, sai na kira lambar gidan Sayyid a Gyallesu don na ji cikakken labara, saboda in san me zan gaya wa Mamansa idan ta tambaye ni? Ina ko bugawa, sai ko su Sayyid suka dauka. Suka tambaye ni, da wa nake son na yi magana? Na gabatar da kaina da dangantakata da Shahid don na samu yadda zan wa iyayenmu bayani. Sai na ji su Sayyid sun ce, "haka ne, kana magana ne da Ibraheem Zakzaky."

Sai na yi sauri na mai da kan wayar, ina ajiyar zuci! Can bayan ’yan mintuna, sai na yanke shawarar na kara kira. Ina kira sai Sayyid ya ce, "Me ya sa ka ajiye kan wayar? Ai ni ma ina jiran kira ne shi ya sa na dauka". Daga nan su Sayyid suka yi min bayanin yadda waki'ar ta auku da yadda aka tafi da su Mal. Haruna Abbas da Shahid Abdulkadir gidan yari. Wanda a nan gidan yarin ne Allah ya kara hada jinin Shahid Abdulkadir da Mal. Haruna Abbas. Duk da Mal. Haruna ba Bakatsine ne ba, amma akwai shi da wasa da mu. Don yana yawan tambayar mu kulikuli!

CI GABA DA ZAMAN ZARIYA

Shahid Abdulkadir Muhammad, ya bar garin Minna ta Jihar Neja ne, bayan kammala taron kara wa juna sani na kasa (Mu'utamar Am) da ’yan’uwa na garin Minna suka karbi nauyin bakuncin shiriyawa a shekarar 2003. Sannu a hankali har ya zama Abdulkadirin gidan Malam (Tekon) har zuwa ranar fitar ransa. Shahid Abdulkadir, ya sa natsuwa da kulawa sosan gaske dangane da manufar abin da ya sa ya yi sallama da Iyaye, Dangi, Abokane, da duk wasu jin dadin rayuwar duniya, ya tare, ya zama mazaunin Zariya don jininsa da ransa su zama fansa wajen karewa, kula da ba da kariya ga ran Jagoransa, Sayyid Zakzaky (H).

Allahu Akbar! Kamar yadda ’yan’uwan da numfashinsu suka kasance na karshe a gaban kofar gidan Sayyid (H), sun tabbatar da cewa Shahid Abdulkadir ne, mutumin karshe da ya kulle kofar gidan Sayyid. Ya Allah! Sayyidah Suhaila Zakzaky (H), ta tabbatar wa duniya a zantawarta da Aliyu Sale, cewa, "bayan an karar da duk wadanda suke ba da kariya a gaban gidan Abba, har sun kai ga shigowa tare da sanya wa gidan wuta. A lokacin mu muna zauren Abba, mu 11, Mal. Abdulkadir ne suka fara harbewa a kirji don shi ne na karshen barin zauren da za mu canza daki. Har sai da muka ji fadowar kayayyaki da hotunan da ke jikin bango sun zubo." Ya Salam! Amma, a wannan yanayin bayan harbin Shahid Abdulkadir, Ubangiji ya makantar da su, ba su kutsa su ga su waye Shahid Abdulkadir ke tare da su ba. Kuma na kara samun yakini cewa a nan zauren su Sayyid ne wuta ta cinye Shahid Abdulkadir. Hmmnn! Ya subhanallah!

Shahid Abdulkadir, na daga cikin Shahidai 3, da Allah ya daukaka Da’irar garin Minna da su. Kuma 2 daga cikin 'yan kabilar Nufawa da Allah ya daukaka da wannan daukakar darajar da muke alfahari da ita. Ya yi shahada ya bar ’ya’ya 7 kamar haka:- Muhammad, Fatima, Zainab, Sukaina, Rukayya, Ma'asuma da Najima, wadanda a yanzun suke Katsina.

Ya Hadimin Sayyid! Ya Shahid!! Ya Amin!!! Lalle tafiyarka a tafarkin da ka tafi, ba abin bakin ciki ne a gare ni ba. Bakin cikina da fargaban tashin hankalina a rayuwata shi ne yaya ni ma zan koma ga Mahaliccina da irin kyakkyawar daukakar makoma da Allah ya daukake da ita?!