AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Ban yi tsammanin zan tsira da rai a Gyallesu ba - In ji Mal. Muhammad Sani Bachirawa


Maulid Sayyada Fatima

Mai karatu wannan ita ce hirar da muka yi da Malam Muhammad Sani Bachirawa daya daga cikin ’yan uwa da suka tsira da rai a lokacin da rundunar Sojin Nijeriya ta kai hari kan Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) a gidansa da ke Gyallesu a ranar 12/12/2015. Umar Babagoro Dukku ne ya dauko hirar, kuma ya rubuta. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN: Za mo so ka fara da gabatar da kanka ga masu karatu.

MUHAMMAD SANI BACHIRAWA: Sunana Muhammad Sani Alhasan Bacirawa, Kano.

ALMIZAN: Kasantuwar kana cikin wadanda waki'ar Zariya ta 12/12/2015 ta rutsa da su, za mu so ka ba mu labarin abubuwan da suka faru da kai. Amma fa farko ta yaya ka fara jin labarinta?

MUHAMMAD SANI BACHIRAWA: Da yake ni ma’abocin ta’ammuli ne da Social Media, to a wannan ranar ta Asabar 12/12/2015, misalin karfe 12:00 da mintoci na hau Internet ko Sakar Sama ina duba zaurukan WhatsApp, sai na ga an turo sakon a halin yanzu ana sauke Sojoji a bakin Husainiyya, to sai muka kira can Zariya din, sai aka ce mana eh haka ne, amma wai an tambaye su sun ce ba komai, wai ana bikin yake sabbin Sojoji ne. Ni kuma na san a wannan ranar akwai bikin sanya tutar Maulidi a Husainiyya Bakiyyatullah, amma na san mutane ba sa yawa a bikin sanya tuta, kuma ma sai can da yamma za a yi, kamar 5:30ny za a yi taron. Kafin nan sun gama taronsu sun tafi.

To, bayan karfe 12 ta wuce sai na sake hawa WhatsApp, sai na ga an sake turo sakon cewa Sojoji sun fara harbi sama. Su ma sai na ga an sake turo wani sakon sun fara harbin ’yan uwa. To, daga nan sai na tashi don in tafi Zariya tunda na san akwai bikin saka tuta da jana’izar Shahidan Gabarin, kuma dai ya zama an yi komai a kan idona. Da yake ina bibiyar abin da ke faruwa, to kafin ma in karasa tashar mota, sai na ga an turo cewa sun shahadantar da wasu (’yan uwa), kuma suna kwashe gawawwakin.

To, bayan kafe 3:00 sai na ga mutane suna ta kwafowa daga shafin BBC suna watsawa wai an tare wa Shugaban Sojoji Tukur Yusuf Buratai hanya. Sai na ce, to meye ya kawo maganar Buratai kuma a ciki? Ai mun yi Tattaki ma ba mu tare hanya ba!

To, a nan cikin motar sai wani ya yi waya can Zariya yana tambayar halin da ake ciki, wai ya ji an ce ’yan Shi’a sun tare wa Buratai hanya. Sai aka ce masa ai yanzu ma Sojoji suna nan sun kewaye Husainiyyar tasu. To, bayan sun gama zancensu, wasu a motar sun yi sharhi. Sai na ce masu gaskiya ba ku da adalci! Ni dan Shi’a ne, kuma yanzu ma can zan tafi, ai tun kafin 1:00 Sojoji suke kashe mana ’yan uwa, amma ku yanzu aka gaya maku, kuma har kun yarda. To, sai suka yi tsitt! To, sai ya zama motar tana tafiya tana debi zubar. Don haka ban iso Zariya ba har sai gab da Magariba.

ALMIZAN: To, daga nan sai meye ya biyo baya? Muna so ne ka kwashe duk labarin abin da ka gani ya faru a waki'ar ja ba mu.

MUHAMMAD SANI BACHIRAWA: Gaskiya ita wannan waki'ar ta fi karfin ka iya fadar ta gaba daya, don wani abin, sai kana wani abu, sai ka tuna kaza ma ya faru! Kuma ni abubuwan da na gani din, ina mamakin kaina da ya zama har yanzu ban haukace ba!

To, bayan mun isa Zariya sai Direba ya sauke mu a wani gidan mai, tun da ya ji labarin babu hanyar zuwa PZ. To, sai na tare mai babur na ce ya kai ni PZ, don ina zaton ko zai bi hanyar Husainiyya. Amma sai ya ratsa da ni wasu lunguna har muka je wata mahadar hanyoyi (junction), sai ya sauke ni ya ce mini “ga PZ can ka karasa, ni ba zan karisa ba, Sojoji ne a gurin”. To, ni kuma bako ne ban san gari ba. Kuma dole nan PZ din zan bi, don ta nan kadai na sani. Sai na yanke shawarar kawai in tunkare su.

To, ina tafiya sai na hangi wasu samari sun tunkari gurin da Sojojin suke (su gidajen sune a gurin), to suna zuwa sai na ga Sojoji sun sa su sun durkusa, to ashe a gurin sun tara mutane da yawa suna daddaurewa suna jefawa a mota, ga shi a gurin sun tara igwa-igwa, ina ta addu'a na wuce ba su ce min komai ba. Sai na iso PZ na tari mai babur na ce masa Gyallesu, sai ya yi banza da ni. To, sai na kira Awwal K/Mashi na ce masa na tare mai babur na ce masa Gyallesu, amma ya yi banza da ni ya ja babur dinsa ya yi gaba. Sai K/Mashi ya ce mini; “Amma dai duk yadda za a yi ka taho Gyallesu”. Sai na yi ta tafiya a kasa, sad da na zo titin shiga Gyallesu ta bangaren Kongo, nan ma sai na ga an jibge Sojoji ba sa barin mota ta bi gurin sai sun caje ta. To, sai na mike na bi tsakiyar su na wuce.

Bayan na dan yi nisa sai na sake kiran K/Mashi na ce masa fa babu hanyar shiga Gyallesu. Sai ya kara jaddada mini lallai duk yadda zan yi in yi in shigo Gyallesu. To, sai na ratsa cikin lunguna ina tafiya sai na bulla wani wuri, a wurin akwai masu A-dai-daita-sahu (KEKE NAPE) suna cewa “Gyallesu-Gyallesu”. Sai na shiga na zauna, sai na ga su ma suna ta waige-waige. Lokacin da muka iso Gyallesu, sai na ga ’yan uwa suna ta addu’a! Rabona da abinci tun karin kumallo! To, sai na sayi kosai na Naira 50, amma mu shida muka kasa cinye shi saboda ba mu da natsuwa.

To, muna tsaye a kofar gidan Malam (Zakzaky), sai aka zo aka ce mana kowane gari su ware guri guda, to bayan mun ware sai mai jawabin ya ce mana; “To fa duk wanda ya zo nan ba lallai ba ne ya koma! Don za mu tsayu ne ba za a taba Shugabanmu ba har sai idan ba ma raye kamar yadda Sahabban Imam Husaini (AS) suka yi”. Can sai aka zo aka rarraba mu za mu yi 'duty', mu 7 sai aka tura mu Gabas da gidan Sayyid Zakzaky (H), wato can gaban wannan tranfomer idan ka mike har kan wani junction.

To, wanda ya kai mu yana yi mana jawabi kafin ya juya ya bar gurin, sai muka ji an fara ruwan wuta ratatatata har kan rufin da muke ciki! Lokacin bai fi karfe 10:15nd ba, sai suka dan tsagaita harbin karo na farko.

A haka muka kwana a wannan wuri muna ta jin ruwan wuta a can Banadin, sannan muna jin tashin bama-bamai da gurneti a can Husainiyya. Kamar misalin karfe 3:00nd Malam Kabiru Alkanawi ya zo ya tambaye mu shin akwai abin da ya faru a nan inda muke? Muka ce masa babu. Duk da ma dai muna ganin Sojojin suna hasko mu da wasu manyan fitilu. Bayan mun yi Sallar Asubahi, ranar Lahadi kenan sai muka ga mutane suna ta tafiya gidan Malam, to sai muka bi su. A lokacin da na je gidan Malam Zakzaky (H) na samu gawawwakin Shahidai sun fi 100, ban da masu raunuka, kuma sai dauko gawawwaki da masu raunuka ake ta yi.

Akwai abin da na manta ban fada maka ba, wato lokacin da ’yan uwa suke bugo mini waya daga garuruwa daban-daban Sojojin sun daina harbi, aka ce mini duk garuruwa an fara Muzahara tsakar dare sai daga baya suka ci gaba. To, haka lokacin Sallar Asubahi nan ma sun dan tsagaita wuta, amma a nan suna jiran a karo masu Sojoji ne, don lokacin da na je Banadin na samu sun ajiye wasu Sojoji da igwa dinsu ta lalace, Soja daya yana tsaye a kanta, sauran suna zazzaune.

Lokacin da suka koma barin wuta gadan-gadan, sai na hangi wasu ’yan uwa sun dauko wani wanda aka harba kuma dukkan su babu mai karfi, sai na zo na ce masu su dire min shi a gadon bayana, na sa shi a kafada ta ina tafiya, sai ga Sojoji sun bullo suna ta ruwan wuta, sai ana ce mini in kauce-in-kauce, to ba zan iya kaucewa ba! Saboda nauyin mutumin! Allah da ikonsa har na sha kwana harbin bai same ni ba. Duk dan uwa da ka gani ya gaji! Ga yunwa, ga kishirwa! Muna ta daukowa har ya zama na dauko wani sai na ji ba zan iya kai shi ba! Sai na roki wasu ’yan uwa su taimaka su karbe ni! Sai muka hadu mu hudu maka dauke shi! Ni tun a lokacin ban iya sake daukar wani ba.

Wani abin mamaki shi ne akwai alamar sun yi amfani da makamai masu guba, don za ka ga ’yan uwa ba kuzari! Jikinsu a mace, kawai dai sai karfin zuciya, yin kabbarorin ma ya gagara saboda tsananin bushewar makogoro, kuma ga shi nan mu da Sojojin muna kallon juna har ma wani lokacin suna yi mana dakuwa. Sai ka ga Soja ya koma bayan mota ya sake dura alburusai ya dawo. Sojojin sun yi ta kokarin su haura kan wani gida sai su harbo mu tun da muna kwace ne a kasa, amma sai suka kasa. To, ni sai na koma kofar gidan Sayyid Zakzaky (H) don in nemo wadanda za su iya yin kabbara. Sai Malam Mukhtar Sahabi ya zo ya ce; “A ware mutane 20-20 sai su zagaya bayan Sojojin su taho suna kabbara ko za mu samu mu dauke hankalinsu”. To idan an ware 20, sai ya zama babu wasu 20 din! Ana cikin haka sai Shaikh Turi ya fito ya nufi hanyar, a lokacin sai na yi kwalla saboda na san babu yadda za a yi mutum ya je gurin ba a harbe shi ba! Amma na dan yi farin ciki saboda na dauka abin ya zo karshe tunda mutane sun dunguma sun bi Shaikh Turi.

Sojojin sun yi mana wayo! Mu daga wanda ya zauna yana yin addu'a sai wanda yake jefa dutse, muna jefa duwatsu har duwatsun suka kare, ga shi kuma ko ka yi jifan ma ba ya isa wajen da Sojojin suke, wani lokacin ma za ka wurga dutse kana gani ya je ya fadi a kan gawawwakin Shahidai, sannan kuma ba ka da damar ka dauko dutsen. Su kuma Sojoji idan sun yi harbi, sun yi harbi sai su koma su zauna.

Ana cikin haka sai muka ga zugar Sojoji sun fi 200, kuma ta kowace hanya sun tinkaro mu suna ta harbi! Sai suka harbe duk ’yan uwan da suke gaban transformer, sai ya zama mu muna ta Gabas da gidan Shaikh Zakzaky (H), kuma babu damar mutum ya tsallaka ta gaban transformer ya koma kofar gidan Shaikh Zakzaky (H) din.

To, a layin sai na ga Shahid Hafiz Dauda da harbi a jikinsa, amma an daure masa. Sai ya ce mana; “Kar mu kuskura mu ja baya, don Sojojin nan Malam suke nufi”. A gurin babu damar mutum ya koma kofar gidan Sayyid Zakzaky (H), ko lekawa wani ya yi sai dai mu ga an harbe shi. A gurin akwai Malam Abdullahi Abbas yana tare da wani abokinsa, to abokin nasa ya leka ke nan sai aka harbe shi a ka, sai Malam Abdullahi Abbas ya ce; “Subhanallahi! An harbe shi”. Sai ya je gurin abokin nasa ya sunkuya zai dauke shi ke nan shi ma sai muka ga ya fada kan abokin nasa, shi ma sun harbe shi.

A lokacin sai Sojojin suka bullo nan gab da transformer sai suka rinka ruwan wuta a kanmu, a lokacin kuma wasu Sojojin sun bullo ta gabanmu. Mu sun saka mu a tsakiya, ga wasu Sojoji a gefen transformer suna bude mana wuta, ga wasu a gabanmu su ma suna tahowa suna ruwan wuta, sai muka kwanta! Wasu kam kafin su kwanta an riga an harbe su. Kamar Malam Hafiz Dauda a lokacin zai yi mana magana, sai na ga a harbe shi a kirji! Sai ya fada cikin kwata! To, muna kwance a bayan wata mota, sai wani Soja ya kwanta a kasa ya yi ta harbin mu. To, ni sai na yi rarrafe har na tsallaka hanya.

Ina cikin rarrafen sai wani dan uwa wanda aka harba ya kama kafa ta ya rike gam-gam! Yana cewa; “Don Allah ka taimaka ka dauke ni an harbe ni!” To hanjinsa suna waje, kuma babu damar in tashi, babu yadda na iya, dole na wuce shi! To, na tashi ina gudu sai ina ganin harbi yana wuce ni yana huda gini, a haka na yi ta haura gidaje suna ta harbi ina ta tsallaka gidaje har na samu na buya a wani lungu. To, da na ji sun tsagaita harbi sai na fito ina gudu zan koma kofar gidan Malam Zakzaky (H), sai suka gan ni saboda a gurin ba za ka ga kowa ba sai Sojojin. Nan ma sai suka bi ni da harbi, Allah da ikonsa ba su same ni ba har na koma kofar gidan Sayyid Zakzaky (H).

Na dawo na samu ’yan uwa suna tsaye kowa ya rasa abin da zai yi. To sai muka yanke shawarar tunda Sojojin suna nan har jikin katangar gidan Malam gurin transformer za su iya wurga wani abu cikin gidan, don haka mu kama hannayen juna sai mu tinkare su! Su kashe na kashewa sauran ’yan uwa kuma sai su kama su! To sai muka rabu gida biyu, akalla wadanda suka yi gaba sun kai mutum 30, to sai suka kama hannun juna suka tunkari Sojojin suna kabbara, suna yanko kwana sai Sojojin suka bude masu wuta, sauran mu!

To, akwai wani dan uwa a can yana gaya mana mu zo mu danna su, shi a lokacin ya leko da kansa kawai sai gani muka yi ya fadi kas! Kansa ya zama kamar an fafe kwarya! Kwallon kansa ya zama kamar an cire hula ne kawai, ga kwakwalwarsa tana zuba, mu ma bai fi jan numfashi ba, sai muka ji ana ta bude mana wuta, har na kwance harbewa suke yi, to ni a lokacin kamar na suma ne! Da na farka sai na yi sauri na zare kaina a cikin mutanen da suka daddanne ni a cikin jini.

A daidai lokacin sai na ga wata Sista da wani saurayi sun tashi sun tsaya, Sistar duk ta jike da jini! Suka yi kabbara sai Sojojin suka bude musu wuta! Sannan akwai wasu matasa guda biyu suna tsaye a karamar kofar shiga gidan Malam sun ki su bar kofar sun rike kirjinsu kamar sun yi kabalu, su ma a haka aka bude masu wuta. Da na fahimci ba a harbe ni ba, sai na rinka jan jiki har na fada cikin dan karamin magudanar ruwa. A nan karkashin wannan dakalin da ake kasa littattafai a kofar gidan Sayyid din.

A gurin ina ganin kamar ba mu kai 20 muka rage ba! To akwai wata mota, muna neman mai ita ya zo ya bude mu tura ta mu bi bayanta sai wani mutum ya zo da sauri ya bude motar ya shiga, Sojojin suna kallo, to ya yi key motar ta ki tashi sai muka tura ta, tana tashi sai ya fincike ta ya yi cikin Sojojin, to sai suka watse ya bi tsakani su ya karya kwana, to sai suka harba masa gurneti suka tarwatsa motar. Daga wannan lokacin muka gane ba mu da sauran dabara.

Ana cikin haka sai Sojojin suka fara harbe duk wanda suke ganin yana motsi a kofar gidan Sayyid Zakzaky (H). To, amma ba su karasa isowa kofar gidan ba, to ni sai na gudu na bi ta gefen masallacin nan. A gurin akwai wata katangar bulo sai na haura na zauna a kan katangar. To, cikin gidan sai na ga wani dan uwa yana kira na yana so in taimaka masa an harbe shi a ciki har hanjinsa sun fito. Sai na ce masa ya yi hakuri ya daure gurin da rigarsa don babu hanyar fita da shi.

Ina kallo wani Soja mai dauke da babbar bindigar harba gurneti ya zo yana kwankwasa gidan Shaikh Zakzaky, sai ya juya ya tafi bai kallo inda nake ba. Sai wasu Sojoji suka zo ina kan gini ina kallon su suka gama suka juya. To wani Soja ya zo ya kalli inda nake, muna hada ido sai ya daga bindiga, amma kafin ya harba na dira cikin wannan gidan, sai na kara tsallakawa wani gida. To sai na fito ta wani lungu a nan Yamma da gidan Sayyid (H) kafin ka iso wannan babban jujin, na sami mutane masu yawa a tsattsaye, sai kallo na ake yi saboda duk na jike da jini, na ga kamar akwai ’yan uwa a ciki, to sai wani ya zo ya tare ni sai na ce masa dama kuna nan ake mana wannan zaluncin? Sai ya ce min; “Ka lura yawanci a nan SSS da jami’an tsaro ne a cikin farin kaya”. Don haka sai na zauna a daidai kofar gidan.

To, a lokacin sai na fara jin yunwa da kishirwa! Idan na tashi jiri ne yake diba ta, makogorona kamar zai tsage saboda gubar da muka shaka! Na sake tashi sai na ga mutane suna gudu, to sai na dan kara gaba kadan, sai na yi sallama a kofar wani gida sai suka bude wata ta leko sai na roke su ruwa, sai suka miko min suka sake rufe gidansu. To ina shan ruwan sai wani ya zo yace min; “Ni ma dan uwa ne, don Allah ka taimaka min da ruwan nan.” Sai ya ce min kar in bi ta can akwai Sojoji a kwance cikin rake suna harbe mutane. Sai na ce masa to don Allah tunda kai dan gari ne ka taimaka ka fid da ni Unguwar sai ya ce mini yana zuwa. To shiru ban sake ganin sa ba. Sai na fara tafiya zan bar Unguwar. Sai na ga duk takalmana sun yi guda-gudan jinin Shahidai kamar na shiga mayanka. Sai na ce mutanen wannan gidan su kara mini ruwa sai na samu na wanke takalman. Sannan na cire rigar da tafi jikewa da jini na saka ta a aljihu, sai na kama hanya ina tafiya mutane sai kauce min suke yi.

Bayan na haura wannan katon jujin sai na tari mai babur na ce ya kai ni PZ, sai ya ce ba a zuwa PZ. Sai na ce to ya kai ni inda zan samu motar Kano. Duk ta inda muka bi sai mu ga Sojoji suna kama ’yan uwa, su harbe wasu, wasu kuma su daure da igiya. Can sai na ga mun bulla Kofar Doka, nan ma Sojoji sun sanya shinge suna kama ’yan uwa musamman masu bakin kaya. Kawai sai nace masa mu ratsa su! Allah da ikonsa sai muka wuce ba su tsai da mu ba.

Akwai abin da na manta ban gaya maka ba, kafin isowar Sojoji kofar gidan Malam (H) na shiga gidan da ake ajiye Shahidai da masu raunuka, lokacin da na kai wani Shahidi Nasir Mafara, wanda aka yi jana’izarsa bayan kwana 40 da waki'ar. Da na kai shi sai na zaro kamara zan dauki hotuna, sai na tuna ni ma bai fi mintoci ne suka rage in yi shahada ba, duk da cewa ni ma dan Media ne, amma sai na juya ban dauki hotuna ba, saboda tunanina ban yi tsammanin zan tsira da rai a Gyallesu ba!

Bayan na iso Dan Magaji sai aka turo min kati (rechage card) don in sayar in sami na motar komawa, amma duk inda na je sai a ce min ba a sayan kati. Duk da na so in bad da sawu, amma ina! Ta ko’ina kallo na ake yi! Bayan na gaji da yawon sayar da kati sai na hadu da wani dan uwa Dayyib Dan Fulani shi ma daga Kano. Ya ce yana da 1,000 in zo mu je ko za ta kai mu Kano.

ALMIZAN: Me ya fi ba ka tausayi cikin abubuwan da ka gani?

MUHAMMAD SANI BACHIRAWA: Kai suna da yawa. Daga cikin su akwai wani saurayi wanda ya tunkari Sojoji yana kabbara lokacin da Sojojin suka iso transformer. Sai Sojojin suka bar shi yana matso su, har ya karya kwana sai wani ya harbe shi! Sai ya juya yana dawowa ta baya a sunkuye! Ya rike inda aka harbe shi, har ya kusan isowa sai muka ga ya tsaya a sunkuye ya dungura cikin kwatomi. Tsakaninmu bai fi taku 10 ba, amma babu halin dauko shi! Sai kuma Sistar da ta tashi cikin jini ta mike, amma Sojoji suka yi mata ruwan wuta, ta yi daga-daga-daga!

ALMIZAN: To akwai abin da ya biyo baya, bayan ka dawo gida?

MUHAMMAD SANI BACHIRAWA: Ina dawowa gida sai wata ’yata ta motsa kujera sai na yi ta cewa; Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Matata ta ce mini lafiya kuwa? Sai na ce mata kin ji harbe-harben nan, nan ma an fara! Sai ta ce min ’yata ce ta motsa kujera. To, a haka na shafe wata biyu duk abin da ya yi kara, to karar bindiga ne zan ji, har na zaci kunne na zai tafi a haka.

ALMIZAN: To meye kiranka ga wannan gwamnati?

MUHAMMAD SANI BACHIRAWA: Kirana ga wannan gwamnati, kira ne wanda ba za ta ji shi ba! Saboda akwai jinainen al’umma da yawa a kanta, kuma mutumin da ya yi zalunci, amma zaluncin da ya yi din shi gani yake ya yi addini ne, wane kira za ka yi masa? Ko ba ka ga an bude masa Dakin Ka’abah ya shiga ba saboda a karrama shi bisa wannan aikin da ya yi? Amma idan shawara zan ba su, sai in ce su bi umurnin kotu su saki Shaikh Zakzaky (H), sannan su nemi afuwar sa.

ALMIZAN: A bangaren ’yan uwa kuma akwai wata shawara da za ka ba su?

MUHAMMAD SANI BACHIRAWA: Shawarata ga ’yan uwa ita ce duk sanda ake ce maka wani abu na waki'a yana faruwa a Zariya, to kar ka yarda wani ya ce maka wai babu hanya, kawai ka kama hanya.

ALMIZAN: To mun gode.

MUHAMMAD SANI BACHIRAWA: Ni ma na gode.