AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. JBugu na 1288 ISSN 1595-4474

Rahotanni

Halin da na ga Shaikh Zakzaky ya kara min karfin gwiwa -Dakta Isma’ila Hasan

Daga Aliyu Saleh


soji

A makon jiya ne wani bangare na iyalan Shaikh Ibraheem Zakzaky da wani sashe na Almajiransa suka ziyarce shi a wajen da ake tsare da su. Dakta Isma’ila Hasan na cikin maziyartan. Bayan sun dawo, Aliyu Saleh da Ishak Muhammad Kerau sun ziyarce shi a gida, inda suka tattauna da shi don jin halin da suka samu su Malam a ciki. Ga abin da ya shaida masu.

ALMIZAN: Kun samu ziyartar Shaikh Ibraheem Zakzaky a inda ake tsare da shi, za mu so mu ji yadda ziyarar ta kasance?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Lallai haka ne mun samu ziyartar su Sayyid Zakzaky a inda ake tsare da shi. Mu uku ne muka tafi daga nan. Wani dan uwa Malam Saleh, matarsa, sai kuma ni. Mun hadu da su Malam Badamasi, Hajiya Maimuna da wasu Sisoci da suka taho daga Zariya a wata mota ta daban.

Da yake ka san Malama Zeenat tana fama da ciwon kafa ana neman wata Sista da za ta dan duba ta. Dama tun kafin waki’ar nan akwai wata Sista babbar Likita ce (Consultant) da take dan duba lafiyar kafar Malama din. Akwai ’yar wajena, Fatima, yanzu tana Digirinta na biyu a Iran, da yake ita ma kamar ’ya ce a wajen Malama din, ta zauna a wajenta. Lokacin da Malama ta tuntube ta tana bukata ganin Likitar, sai Fatima ta sanar da ni, ni kuma sai na nemi mijinta, shi ne aka hada tafiyar.

Bayan nan sai muka yi magana da Sayyid Muhammad dangane da tsara yadda za a yi tafiyar, domin shi ne zai jagorance mu. Sai suka ba mu lokaci cewa a mako mai zuwa za a je. Ni dai ba a sake tuntuba ta a kan maganar ba, sai bayan wata biyu. Duk na kosa lokacin zuwan ya yi. Kawai ranar Litinin din da ta gabata, sai Sayyid Muhammad ya fada min cewa sun sake ba da lokacin tafiyar ko Laraba ko Alhamis, don haka mu zauna cikin shiri. Mun zabi ranar Alhamis din. Ka ji yadda tafiyar ta kasance. Wannan shi ne dalilin da ya sa na samu wannan tagomashin.

ALMIZAN: Wato da kai da Likitar da kuma mijinta kuka tafi ke nan?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Haka ne, sai kuma Malam Sa’idu, yaron wajen Hajiya Maimuna din, wato kanwar Malam ke nan. Shi kuma Sayyid Muhammad mun same shi a can ne. Akwai kuma su Malam Badamasi da sauran abokan tafiyarsu.

ALMIZAN: Wannan shi ne karon farko da ka ga Malam tun bayan harin da Sojoji suka kai masa a Zariya, ya ka ji a ranka?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Haba! Ai kar ka tona farin ciki da jin dadi. Ai tun lokacin da aka ce ni ma a sa ni cikin masu zuwan, sai addu’a nake yi, Allah ya tabbatar. Ina ta addu’ar kar a sake dagawa irin na farko. Ba karamin farin ciki na ji ba, wallahi.

ALMIZAN: A karon farko ka ga Malam bayan wannan waki’ar, ya za ka kwatanta mana yadda ka gan shi?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Gaskiya ni dai a yadda na ga Malam ba wani canji, ko ta maganarsa, ko tafiyarsa, ko yanayinsa. Gaskiya Malam, Malam ne. In ba fuskarsa ka kalla ba, ba za ka san wani abu ya faru da shi ba.

ALMIZAN: Da yake ka san Malam fiye da shekaru 30 da suka gabata, ka ce ba ka ga wani canji ba a kan yadda ka sani shi?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Kafin waki’ar nan da na gan shi yanzu ba wani canji. A dai yadda yake da kuma maganarsa. Ka san in Malam yana bayani na daban ne. Da yake yi mana jawabi, ni dai ina ta kallon sa ne ina shan mamakin yadda ya san abubuwan da ke faruwa a ciki da wajen kasar nan, duk da kuwa yana tsare fiye da shekara guda. Abin da na gani, a raina na ce wannan Aya ce gaskiya. Alhamdullahi. Na kara samun karfin gwiwa kwarai.

Akwai lokacin da yake yi mana bayani a kana bin da ya faru a Gyallesu kafin su harbe su, na daure ne da na yi kwalla. Yana yi mana bayani sanka, sanka, hankalinsa a kwance, kamar babu wata damuwa a tare da shi.

A cikin bayanin nasa ya fada mana cewa lokacin da aka harbe shi a kafar dama (kamar yadda Malam Badamasi ya fada mana a farkon zuwan su), Sojojin sun harbi kafar sun lalata ta, ga rami, hannu zai iya shiga, amma abin mamaki, kashin da ya gitta a tsakani bai karye ba.

Aya ta biyu kuma ita ce; sun bar shi har jininsa ya tsiyaye gabaki daya, amma yana da rai. Har wani Likita yake cewa wannan abin mamaki ne. Sai Malam yake ce masa, ikon Allah ne. Da aka yi masa aiki, sun yi masa ‘Popi’, da suka zo suka farke, sai suka ga wajen ya hade. Suka tsaya suna mamaki. Abin da suka gani ya sha bamban da yadda suka saba aiki nesa ba kusa ba. Abubuwan suna da yawa.

ALMIZAN: Wane bayani Malam ya yi maku game da ita wannan waki’ar?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Bayanin dai irin daya ne da irin wanda ya yi wa mutanen da suka ziyarce shi kafin mu je. Da yake ya sha bayani a kai, bai yi mana dogon bayani ba a wannan janibin. Amma ya ce mana bayan sun harbe shi, sai ya zama yana kiran waya, yana magana da wasu ’yan uwa da ke waje.

Daga baya da suka fahimci kamar sun kashe Malam din, sai suka kira wayarsa, sai ya amsa, sai su ce Kanar Wane yana son magana ne da kai, in ya dauka sai su yi shiru, sai ya ajiye. Ashe suna so ne su ji ko ya rasu, ko kuma yana nan da rai. Sai ya daina dauka in sun bugo.

Can da suka sake bugowa, sai Malama ta dauka ta ce masu bayan kun kashe mutum, kuna kiran wayarsa? Sai suka ce da gaske? Sai suka fara sowa, suna murna. Dama sun zo ne suna so su kashe shi, kuma sun kashe shi din.

Mafi yawan harbin da suka yi wa Malama a ciki ne, amma Allah cikin ikonsa, sai harsasan suna komawa gefe. Lallai sun ga Ayoyi da kudurar Ubangiji sosai.

ALMIZAN: Kai ya za ka bayyana ita wannan waki’a din da ya zama su Malam sun tsira duk da kuwa sun zo da nufin su kashe su ne?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Lallai wannan abin al’ajabi ne matuka. Na farko dai kamar yadda shi Malam ya sha bayani, wannan wani abu ne da aka dade da shiryawa. Kuma kamar yadda Malam ya bayyana mana, su ba wai suna fada da Shi’a ba ne, suna fada da Harka Islamiyya ne da kuma Jagoranta, wato shi suke nema su kashe. Suna ganin ita Harka Islamiyya kamar tana taka masu birki a kan yadda suke kwasar dukiyar kasar nan suna fita da ita.

Zan iya tunawa ma a cikin jawabin da Malam yake mana yake cewa su Turawan sun gano cewa a tarihi akwai Mansa Musa na Mali, wanda ya je da dukiya mai yawa aikin Hajji, har suka yi mamakin inda ya same ta. Da suka gano wajen sai suka tura masu ’yan ta’adda din nan. Duk inda suka gano akwai arziki sai su tura masu ’yan ta’adda domin a yi rikici a wajen. Har yake cewa akwai Central Africa da suke kai masu rikici saboda Diamond din da suke da shi. Mu ma nan kasar, musamman a Arewa akwai ma’adanai kala daban-daban, sannan kuma can Neja-Delta akwai mai. Duk inda ka ga sun je sun kai masu rikici, to akwai arziki ne.

Jagoran Harka Islamiyya ne kawai ke fadakar da mutane a kan irin kwasar arzikin da suke yi. Suna ganin in ya ci gaba da wanzuwa jama’a za su gano su. Shi ya sa suke so su yi maganin abin. Kuma da yake ta Allah ba tasu ba, sun samu bawan Allah, sai Allah ya kare kayansa. Gaskiya bayanin da ya yi mana, Allah ne kawai ya kare shi ba su kashe shi ba.

ALMIZAN: Da yake sun yi wadannan kashe-kashe din ne don su kawo karshen Harka Islamiyya da kuma Jagoranta, sai kuma ga shi hakarsu ba ta cimma ruwa ba, me wannan ke nunawa?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Na farko dai zan ce gaskiya ’yan uwa sun karbi tarbiyyar Malam kwarai da gaske. Gaskiya yadda aka dake aka ci gaba da gudanar da abubuwa ba wanda ya gudu, wannan abin mamaki ne. Hatta su makiyan, wannan ya ba su mamaki. Ai mai hankali zai gane cewa in ba karfin imani da kuma sakankancewa da abin da suke yi ba, ba za su tsaya su ci gaba da yin Harka Islamiyya ba ganin yadda ake kashe su kowane lokaci.

Mai hankali ya kamata ya gane wannan Harka ba a bar wasa ba ce. Kuma ya kamata ya gane cewa yadda abubuwan suke tafiya lallai lamarin Allah ne. Kuma ja da Allah ta hanyar cutar da bayinsa, tabbas ba abin wasa ba ne.

Wannan waki’ar ta fito da abubuwa da yawa. Na farko sun ce ’yan uwa ba su bin doka, nan take sai suka fara nuna cewa sune marasa bin doka. Ai a kundin tsarin mulkin kasar nan ya nuna hanyar da ake bi a hukunta mai laifi. Idan kun ce wasu sun tare maku hanya, ba sai ku kira ’yan sanda ba? Amma sai suka bude wuta. A mataki na farko kun karya doka kuna kashe mutane, wanda doka ba ta yarda da wannan ba. Suka sake dawowa suka yi barnar da ta fi wacce suka yi da farko. Ka ga sun karya doka ba kawai ta Nijeriya ba, har ma ta duniya baki daya. Wato dokar ’yancin rayuwa. Shi ya sa ake hukunta mutane a kotun duniya in ya kashe rai kisan gilla irin wannan da suka yi. Shi ne maganar kiyaye ’yancin bil’adam. Sai ga shi masu da’awar suna bin doka, sun taka dokarsu da ta duniya baki daya.

Wannan bai ishe su ba, suka zama kotun kansu, suka kama shi suka tafi da su suka tsare ba tuhuma ba komai, babu dokar da ta ce haka. Karya doka har yanzu. Wato sun karya dokar walwala. Da yake ba su kai shi kotu ba, sai Malam ya je kotu ya ce a ba shi ’yancinsa na walwala. Kotu kuma ta ce, lalla kuwa an zalunce shi, a sake shi a biya shi diyya, kuma a gina masa gida. Suka sake karya doka, suka ki sakin sa, suka ki biyan sa diyya, suka ki gina masa gida, kamar yadda kotu ta yi umurni. Don Allah waye mai karya doka?

Ka ga in suna da hankali wannan waki’ar koma-baya ce sosai a gare su. Suna cewa mune ba mu bin doka, alhali sune kuma ba su bin doka. Duniya kuma ta gane su a haka. Wani ma bai taba ganin ’yan uwa ba, balle ya ga dokar da ake cewa sun taka. Su kuwa ga shi duniya tana ganin suna taka dokoki kala-kala. Lallai wannan abu ya zamo masu tonon asiri, babban koma-baya ne a gare su. Idan ma suna ganin kamar sun yi wannan abin da suka yi don su cimma wani buri, to akasinsa suka samu.

ALMIZAN: Akwai wani abu da Malam ya fada maku, ko kuma wani abu da ya faru da ba za ka manta da shi ba a yayin wannan ziyarar?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Abubuwa da yawa. Ka san na ce ba komai zan fada maku ba (dariya). To akwai dai wani albishir da ya yi mana na kokarin da ake yi na fitowarsu nan kusa insha Allah. Wadanda suke tsare da su suna ta kai-komo don ganin sun samu wani mutum da zai shiga tsakani don a warware maganar. Ka san da yake burin kowane dan uwa shi ne ya ga Malam ya fito, wannan maganar ba zan iya mantawa da ita ba. Mu ci gaba da addu’a, hakarmu ta kusa cimma ruwa insha Allah.

ALMIZAN: Akwai wani abu da Malam ya fada, wanda ka rike shi, wanda kuma kake ganin ya dace a sanar da ’yan uwa?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Sakon bai wuce abin da ya saba fada ba, na kara kaimi wajen neman kusanci da Allah, musaman ma a ci gaba da gudanar da abubuwan da ake yi. Akwai wata Sista cikin wadanda muka tafi din take cewa, akwai shirin da ake yi na gudanar da taron Nisfu Sha’aban. Malam ya ji dadin wannan sosai.

Abubuwan suna da yawa, saboda shauki da shagaltuwa da kallon Malam din ya sa ban iya rike duk abin da na ji ba. Da ya shigo inda muke, bayan ya gaisa da kowa, kuma sai ya rungume ka cike da shauki. Akwai sakon littafi, turba da tasbi da Malam Muhammad Sulaiman ya ban in kai masa, kuma na ba shi hannu da hannu.

ALMIZAN: Ya batun lafiyar jikinsa?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Jikin kam daga yadda na gan shi da sauki. Alhamdullahi, ko tafiyarsa ka gani ba za ka ga wata alama ba, in ba fuskar ka kalla ba, ba wani abu da za ka gani. In ba ka matso kusa ne ba, ba za ka san wani abu ya same shi ba. Ga rawani, ga alkyabba, ga kuma shiga ta kamala irin wacce ya saba yi a waje. Balle kuma ka ji maganarsa. Abubuwan ban mamaki da yake fada, ba abin da ya canza. Idan yana mana magana ya lura mun shiga damuwa, sai ya shigar da wani abu da zai sa a yi raha, don ya kwantar mana da hankali, irin dai yadda ya saba yana yin din nan a waje. Mun ji dadin ziyarar, ba mu so rabuwa ba, sai ya ce mu tashi mu tafi kar mu yi tafiyar dare.

ALMIZAN: Daga karshe akwai wani sako da kake da shi ga ’yan uwa?

DAKTA ISMA’ILA HASAN: ’Yan uwa a dage da addu’a, saboda gaskiya ana ganin tasirinta sosai. Kuma a dage a ci gaba da gudanar da abubuwan da aka saba yi. Kuma a ci gaba da girmama juna, kowa da irin gudummawar da zai bayar wajen kai wa ga cimma hadafi. Allah ya taimaka.

ALMIZAN: Mun gode.

DAKTA ISMA’ILA HASAN: Ni ma na gode.