AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Shaikh Zakzaky ya je Kano ta’aziyyar rasuwar Dk. Batsari

Daga Aliyu Saleh


Ta'aziya

A ranar Lahadin nan da ta gabata 2 ga watan Yuni ne da yamma, Shaikh Ibraheem Yaquob Zakzaky ya isa birnin Kano don gabatar da ta’aziyya ga iyalan Marigayi Dk. Abubakar Salihu Batsari, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Asabar 24 ga Mayu, 2014, bayan doguwar jinya da ya yi a babban Asibitin Malam Aminu da ke cikin birnin Kano...

A yayin wannan ziyarar, Shaikh Zakzaky ya yi wa mamacin addu’a, tare da yi wa iyalansa nasiha. Ya kuma jawo hankalinsu a kan kula da zumuncin da yake sadarwa a lokacin rayuwarsa da kuma yi masa addu’a.

Ya bayyana cewa shi mamaci kodayake bai tare da mu a gangar jiki, amma yana tare da mu a kowane lokaci, kuma yana zuwa gidansa duk ranar Juma’a. Don haka ya jawo hankalinsu a kan su lura da irin ayyukan alherin da ya dora su a kai tun lokacin rayuwarsa.

Iyalan Mamacin sun bayyana matukar farin ciki da jin dadinsu da wannan ziyara da Shaikh Zakzaky ya kawo masu. Malama Raliya Adamu, ita ce Mahaifiyarsa, ta bayyana cewa; “Gaskiya mun ji dadi, mun gode da wannan ziyarar da ya kawo mana”.

Malam Salihu, 80, shi ne Mahaifin Marigayin, ya bayyana wannan ziyara da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kawo masu a matsayin abar alfahari a gare su. “Mun gode kwarai da gaske. Allah ya yi masa albarka. Abin da yake yi wa jama’a, Allah ya mai da masa. Wannan ziyarar ta ishe mu abar alfahari. Na yi mamakin zuwansa. Dubi dai irin girman Allah da ya yi wa Malam, ban yi zaton zai zo nan gidan ba. Kwanana takwas a nan gidan, jiya zan koma, amma da aka fada min Malam zai zo, sai na fasa tafiyar na jira zuwansa ko zai kai kwana nawa. Ban taba ganin sa ba, sai yau. Na gode, Allah ya yi masa albarka”.

Shi kuwa Haruna Abubakar, wanda yake shi ne babban dan Marigayin, ya bayyana matukar farin cikinsa dangane da wannan ziyarar. “Muna matukar farin ciki da wannan ziyarar ta’aziyyar da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kawo mana.”

Marigayin dai ya rasu yana da shekaru 48 a duniya, kuma ya bar Mahaifansa, matan aure biyu da ’ya’ya 11.

Daga cikin wadanda suka rufo wa Shaikh Zakzaky baya a yayin wannan ziyarar akwai; Malama Zeenatuddeen Ibrahim, Sayyid Hammad Ibraheem, Shaikh Muhammad Turi, Dk. Abdullahi Danladi, Malama Maryam Sani, Malama Maryam Abdullahi da sauran su.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron