AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Me ya sa Hadisan Ahlul Baiti (AS) suka karanta?

- Malam Kasimu Umar ya ba da amsa
Daga Sulaiman Musa Bodinga


Malam Kasim

“Sanannen abu ne cewa Hadisan Ahlul Baiti (AS) sun karanta a cikin littaffan Hadisai na Ahlus Sunna, wanda hakan ya nuna akwai dalilai da suka sa hakan. Tabbas siyasoshi da kuma gwamnatocin da aka yi bayan wafatin Manzon Allah ne suka sabbabar da yanayin ta hanyar kau-da-kai da kuma daukar matakin dakile wanzuwar ilimin Gidan Manzon Allah a duniya, wanda su ta nasu bangare sun yi hakan ne don cikar burin rayuwarsu ta duniya”...

Malam Kasimu Umar, wakilin ’yan uwa na Sakkwato ne ya yi wadannan bayanai a wurin Maulidin Sayyidah Fatimah Az-Zahra (AS), wanda ’yan uwa na Da'irar Bodinga a jihar Sakkwato suka gabatar, ranar waccan Lahadi da ta gabata.

Malam Kasimu ya ci gaba cewa, gidan Manzon Allah (SAWA) ya shiga wani hali, jim kadan da wafatinsa. Ya ce, Sayyidah Fatimah (AS) da Mijinta Ali (AS) da ’Ya'yansu Hasan da Husani (AS), bayan saka su cikin kunci da takura masu da aka dinga yi, haka ma an kange su, ba a karbar magana daga wajen su.

Ya ce, Sayyidah (AS), duk da gaskiyarta da kusancinta da Mahaifinta, Manzon Allah (SAWA), amma wai ba ta ji komai daga bakin Mahaifinta ba. Abin mamaki, wasu da dama da ba su kai matsayinta da kusanci ga Annabi (SAWA) ba, ga Hadisansu nan birjik a litattafai. Wannan har kullum shi yake tabbatar mana da cewa, an juya wa Gidan Manzon Allah (SAWA) baya, in ji shi.

Malamin ya ce, duk da kau da -kai da takura masu da aka yi da mabiyansu, bai hana su taskace ilimin addinin Musulunci ba, da kuma bayyana hakikanin koyarwar Manzon Allah (SAWA) ga al'umma.

Malamin haka ma, ya yi bayani kan yadda sarakunan da aka yi bayan wafatin Manzon Allah (SAWA), musamman sarakunan Banu Umayyah suka yi amfani da damarsu wajen canza wasu abubuwa da suke Sunna, tare kuma da shigo da wasu abubuwa na bidi'a a matsayin addini.

A cewarsa, “sun yi hakan ne da manufar ganin sun canza addinin Manzon Allah (SAWA) gaba daya.”

Tun da farko, Malamin ya yi gamsasshen bayani kan rayuwar Sayyidah Zahra (AS), tun kan haihuwarta, matsayinta, ilminta da kuma dimbin darajojin da Allah Ya yi mata. Haka ma ya tunatar dangane da Wasiyyar da Manzon Allah (SAWA) ya yi ga al'umma cewa bayan wucewarsa, su bi Littafin Allah (Alkur'ani) da Iyalan gidansa. Ya ce, Alkur'ani shi ne littafin da aka zabar mana mu bi mu gudanar da rayuwarmu a kai, yayin da su kuma Ahlul Baiti (AS) an nasabta mana bin su, domin su fassara mana Alkur'ani.

Malam Kasimu har ila yau, ya bada amsa ga masu ganin rashin dacewar binciken tarihin magabata, ya ce ana binciken tarihin addini ne don waki'o’in da suka wakana a san masu gaskiya, a kasance tare da su, kamar yadda Allah (T) Ya yi umurni cewa a kasance tare da masu gaskiya.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron