AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Yadda aka yi Maulidan ’Yar Manzon Allah (S) a Maiduguri

Daga Hasan Ibrahim Maiduguri 08069558570 (hibarnawy@yahoo.com)


Sayyada Fatima

Lallai ’yan uwa mata, almajiran Malam Ibraheem Zakzaky na garin Maiduguri sun nuna su masoyan Manzon Allah (SAWA) ne da kuma ‘Yarsa Fatimah (SA) kan yadda suka gudanar da bukukkuwan Maulidin a Halkance da kuma na hatama da suka gudanar ranar Talatar karshen watan na Jimada Sani...

Ranar Talata, ’yan uwa mata na Da’irar ta Maiduguri, karkashin jagoranchin Wakiliyarsu, Malama Hawwa’u suka gudanar da nasu Maulidin a Halkance a nan kofar gidan Wakilin ’yan uwa, wato Markaz.

Yadda suka kayata wurin, abin sai wanda ya gani, suka kuma gayyato shahararrun mawakan nan, Malam Basiru Maiduguri da Muhammad Sakafa daga Gashuwa.

Bayan gama sauraron wakoki daga mawakan, su ma daliban Fudiyya sun kawata bikin da faretin da suka yi, domin taya iyayensu mata murnar wannan biki. Daga nan sai aka saurari jawabi daga bakin Malam Bala (Yahaya) Sa’idu, Wakilin ’yan uwa na Maiduguri.

Mahalarta Maulidin sun yaba wa ’yan uwa matan sosai, saboda yadda suka fito manyansu da kananansu suka nuna soyayyarsu ga ’Yar Manzon Allan (SAWA) a aikace. An ce ba a taba Maulidi irin sa ba.

Ranar Talatar karshen watan ne, ’yan uwa matan suka shirya Maulidin na hatama a filin da ake kira da Filin Bakin Dogo, inda suka tsara filin da rumfa da kujeri, ga kuma mumbari, abin gwanin ban sha’awa. Sun burge kowa ta fuskacin tsara wuri da kawata shi, sun doke mafi yawan ’yan uwa a fagen ado da kwalliya. Kuma sune suka fi tara manyan baki daga wajen Harka. Yayin da zuwan babban bakon da suka gayyato, Malam Bala Sa’idu ya kara kawata wajen. Kafin nan kuma, majalisin mawaka da kuma faretin da daliban Fudiyya suka gudanar dai, sun fi gaban labari, sai wanda ya gani da idonsa.

’Yan uwa matan sun samu yabo da jinjina, ganin irin wannnan namijin kokari da suka yi na shirya wadannan bukukuwa, kuma sun yi sa’ar samun cikakke kuma gamsashen bayani a kan rayuwar ‘Yar ta Manzon Allah (SAWA). Sai dai kuma abin ban sha’awa shi ne yadda jama’ar gari suka gamsu da yadda almajiran Malam Zakzaky suka shirya irin wannan Maulidi, kamar yadda wasu suka shaida wa Wakilinmu a Maiduguri.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron