AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Yadda Maulidin hatama na Imam Ali ya gudana a Kano

Daga Muhammad Isa Ahmad (muhd1389@gmail.com) da Ahmad Sa’eed da Muhammad Sakafa, Kano


Maulid Sayyada Fatima

Bayan Maulidan Amirul Mu’uminin da matasan Harka Islamiyya na Da’irar Kano suka jagoranta a wannan wata mai alfarma na Rajab a unguwanni da garuruwa na Halkoki da shiyyoyi, a ranar Asabar 2 ga Sha’aban 1435 (31/5/2014) aka gabatar da hatamar Maulidin a cikin kwaryar Kano a masallacin Juma’a na Arewa da gidan Sarkin Kano...

Al’umma da dama masoya Amirul Muminin (AS) sun halarci hatamar, wanda Shaikh Muhammad M. Turi ya kasance babban bako. Cikin bakin da suka halarta akwai Sharif Khidir, Sharif Shubuli, Malama Baraka, Malam Habibullahi Ali Alkali, Malam Nura Kasim Rimin Kebe.

Shaikh Muhammad M. Turi, a jawabin da ya gabatar ya yi waiwaye ga takaitaccen tarihin Imam Ali (AS), yana mai jaddada daukaka, girma da darajar da Allah ya yi masa tun daga haihuwarsa zuwa ga komawa ga rahamar Allah (T). Imam Ali (AS) ya kasance wanda aka haifa a daki mai alfarma (Ka’abah), kuma ya koma wa Allah yana Shahidin da ya yi shahada a masallaci yana mai sujada.

Malamin ya kara nuni ga yadda Manzon Rahma (S) ya yi nuni da riko da shi da bin sa, yana mai karanto ayoyi da Hadisai. Ya kara jaddada cewa bin tafarkinsu ita ce kawai mafita ga dukkanin Musulmi da al’umma, kamar yadda Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ke kara nunasshe mu.

Malamin wahada, Malam Nura Kasim a jawabin nasa ya yi nuni da daraja da daukakar Imam Ali (AS).

Taron har ila yau ya sami halartar matashin Malami daga Darikar Kadiriyya, Malam Muhammad Nura Alkadiri, inda ya yi ta bayani dangane da martabobin Imam Ali (a.s).

Malam Nura ya jaddada cewa, lalle duk sahabbai babu mai ilimin Imam Ali. “Shi ne ya fi kowa sani a cikin Sahabban Ma’aiki (S), saboda shi ne wanda Manzon Allah (s) ya ce shi ne birnin ilimi, Ali kuma kofar birnin.”

Malam Nura ya ci gaba da kawo hadisai dangane da Imam Ali, inda ya ce, in banda Manzon Allah (S) babu wanda ya kai Ali dan Abu Dalibi bayar da gudummawa a wannan addinin. Ya kara da cewa Manzon Allah (s) ne ya bar wa al’ummarsa wasiyyar cewa lalle a bayansa su yi riko da Imam Ali.

A wajen gasar da aka gabatar na Maulidai a tsakanin Shiyyoyi da Halkoki da ake da su, Malam Hafizu Dauda, ya nuna shi dai wannan Maulidin matasa sun fuskantar da koyi ne ga kyautata wa al’umma ta janibi daban-daban, kuma wadanda suka zo na daya zuwa na uku, su suka yi zarra a kan hakan, yana mai karfafa a kan wannan ne dukkanin matasa na Harka na kasa za su fuskantar da Maulidansu.

Malam Sunusi ya ayyana makin kowane Zone da kuma Halka, a inda kowace Zone na da Halka da aka hada su, kuma a bana Halkan Kawo da Zone na Gumel suka kasance na uku, Halkar Na’ibawa da Kura Zone suka kasance na biyu, yayin da Halkar Gwammaja da Zone din Kazaure suka zamo na daya.

Shaikh Turi ya raba Satifiket ga Wakilan kowane Zone da Halka, kuma aka bai wa na daya zuwa na uku kofunan gasa. An karrama Malam Sani Malfa da namijin kokari da yake gabatarwa.

Sharif Khidir ya karbi kofi a madadin Da’irar Kano bisa ga wannan muhimmin aiki da Da’irar ta sanya a gaba.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron