AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Mu’assasar Abul Fadl Abbas sun yi Maulidin Imam Husaini (AS)

Daga Ammar Muhammad Rajab


Maulid Hussain

A ranar Lahadin nan da ta gabata ne aka gabatar da Maulidin Imam Husaini (AS), wanda Mu’assatus Abul Fadl Abbas ta shirya a Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya...

Da yammacin ranar 3 ga watan Sha’aban (1/6/2014), bayan Zaharadden Kode, ya kammala haske wajen da waken Ahlul Baiti, sai Malam Awwal Hanwa ya gabatar da jawabi a Muhallin.

A cikin jawabinsa, Malamin ya fara ne da taya Manzon Allah (S), Imam Ali (AS), Sayyida Zahra (SA), Sayyida Khadija (SA) da Imam Hasan (AS) da sauran A’imma (AS), murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Husain (AS).

Sannan ya ci gaba da cewa shi Imam Husain (AS) tun a Aljanna Manzon Allah (S) ya fara ganin Imam Husain (AS) a lokacin da ya je Mi’iraji. “A lokacin da Manzon Allah ya je Mi’iraji an nuna masa wata baiwar Allah da take kan wani gadon sarauta. Aka tambayi Manzon Allah, ka san wace ce? Ya ce; a’a. Aka ce; Sayyida Zahra ce. Ya ce; Hulan da ke kanta yana alamta mijinta Imam Ali (AS) ne. ’Yan kunnayen da kake gani, na damanta danta ne Imam Hasan. Na hagunta Imam Husain (AS) ne”.

Malamin ya jaddada cewa; Tarihin Imam Husain yana farawa tun daga ainihin Aljanna. Ya ce; dama daga can suke. Kayan gadonsu ne. Ya yi addu’ar Allah ya sa mu kasance a cikin masoyansu.

Har ila yau cikin jawabinsa, ya kawo wani Hadisi mai tsawo wanda ya dan takaita shi. Yake cewa; wata rana Manzon Allah (S) yana dauke da Imam Hasan da Imam Husain a kafadarsa, sai ya umurci Bilal ya kira Sallah. Bayan ya kira Sallah, da ma idan mutane suka ji kiran Sallah a Masallacin Annabi (S), kuma ba lokacin Sallah ba, sun san sako ne muhimmi. Sai mutane suka taru. Sai ya ce; “Ba zan shiryar da ku ga wanda suke daga mafifitan Kaka, Uba da Uwa ba? Suke daga Mafifitan Dan uwan Uba da dan uwan Uwa”. Ya ce Hadisin na da tsawo.

Sai ya ci gaba da cewa; sune mafiya kowa a cikin al’umma. Sun fi kowa Kaka mafi falala. Sune suke da mafifitan iyaye. Sannan kuma sune suke da mafifitan ’yan uwan Uba. Ga su shugabbanin Samarin Aljanna.

Sai Manzon ya ce; Ya Allah ina rokon ka, ka sani dukkan su daga Aljanna suke. Allah ka sanya masoyansu su zama ’yan Aljanna.

Malam Abdulhamid Bello ma ya gabatar da jawabi a wannan Maulidin. A cikin jawabinsa, ya nuna yadda sauran al’umma ke ganin Imam Husaini kawai a matsayin dan ’yar Manzon Allah (S) ne, wato shi Jikan Manzan Allah (S) ne kawai.

Tabbas Imam Husain (AS) da dan uwansa da iyayensa da kakansa, daga haske daya aka halicce su. Ya jaddada cewa; “Tushe daya ne daga Manzon Allah”. Sai ya ce; “Ya zo a Hadisi cewa; Husaini daga gare ni yake, ni ma daga gare shi nake”. Ya ce; “Wannan ya nuna maka cewa Manzon Allah da Imam Husain (AS) daya suke, ba bambanci”.

Ya jaddada cewa, an haifi Imam Husain (AS) a ranar 3 ga watan Sha’aban. Kuma mahaifansa sune; Imam Ali (AS) da Sayyida Fatima Zahra (AS).

Har ila yau Malam Abdulhamid Bello ya tabo magana game da wasu daga cikin darajojin Imamu Husaini, inda ya kawo Ayar Mubahala da sauran Ayoyi da suka yi magana game da shi Imam Hussaini (AS) da sauran Ahlul Bait (AS).


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron