AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Mu’assasatus Shuhada ta ziyarci Mahaifar Shahidin farko


Shuhada

A ranar waccan Juma’ar da ta gabata ne, wakilan Mu’assasatus Shuhada’u ta Harkar Musulunci suka kai ziyara mahaifar Shahidin farko a Harkar Musulunci a Nijeriya, Shahid Muhammad Bello a garin su na Kolori da ke a Karamar Hukumar Gamawa ta jihar Bauci...

Tawagar maziyartan ta isa garin ne da misalin karfe 5:00 na yamma, karkashin jagorancin Wakilin ’yan uwa na garin Gamawa, Malam Muhammad Gamawa.

Bayan bude taro da addu’a, sai Malam Magaji Manu Potiskum ya gabatar da makasudin zuwansu wannan ziyarar, inda daga nan ne sai Malam Ibrahim Potiskum, a madadin Shugaban Mu’assasatus Shuhada’u ya mika sakon ta’aziyyar su Sayyid Zakzay (H) ga ’yan uwan Shahid Muhammad Bello a madadin Harkar Musulinci.

Malamin ya ci gaba da kawo tarihin wannan Mu’assasar da manufofinta, daga nan kuma Malamin ya shaida wa ’yan uwan Shahid Muhammad Bello cewa: “Ba mu manta da shi ba, kuma ba za mu manta da shi ba, don haka ne ma muka kawo maku wannan ziyara ta sada zumunci. Kuma in Allah Ya yarda za mu ci gaba da raya ambaton su. Kuma wadanda suka aukar da kisan, su ma ba mu manta da su ba, kuma ba za mu manta da su ba, muna bin su bashi, za kuma su biya. In Allah Ya yarda za mu ci gaba da kawo irin wannan ziyara lokaci bayan lokaci”, in ji shi.

Shi dai Shahid Muhammad Bello ya yi shahada ne sakamakon bude wuta da jami’an tsaro suka yi a wajen kammala taron Kwas na Musulunci na Lokutan Hutu (IVC) da aka yi a garin Bauci a 1982.

Malam Abubakar (Pharmacy) Azare, abokinsa ne kuma ajinsu daya, dakinsu daya a wancan lokacin, inda ya shaida mana cewa, kullum fatansa kenan Shahada. “Maganarmu da shi ta karshe ita ce kai (da yake ba ya kiran sunana, sai dai ya ce kai) mun tafi, lokacin muna cikin sahu za mu shiga wajen taron. Bayan an yi harbe-harbe ne sai ban gan shi ba, sai daga baya ne muka sami gawarsa a mutuware”, in ji babban abokinsa.

Malam Shehu Musa Kolori, shi ne babban yayansa, wanda yanzu haka yake zaune a garin Kolori. Ya nuna matukar jin dadinsa da wannan ziyara da aka kawo masa, kuma ya ce in Allah Ya yarda za a ci gaba da wannan zumunci. Ya kuma yi rokon Allah Ya saka wa wannan Malami naku.

Daga karshe, an yi addu’a an kuma mika kyauta ga dan uwan Shahidin.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron