Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1131, ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Hatsarin mota a Ranar Shuhada’u: ’Yan uwa mata 2 sun rasu


Harisawa

Da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar Asabar 25/Rajab/1435 (24/5/2014) ,`yan uwa musulmi almajiran Shaikh Zakzaky na Alkaleri ta Jihar Bauci suka yi hadarin mota a kan hanyarsu ta zuwa Zariya domin halartan taron Yaumus Shuhada (Ranar Shahidai)...

Hatsarin ya auku ne sanadiyyar fashewar taya a wani mummunan kwana a wajen kauyen Zalau kusa da garin Gumau da ke Karamar Hukumar Toro ta jihar Bauci.

Motar, kirar Seana tana dauke ne da mutum goma, ta yi ta mirginawa har sau biyar, inda ta yi sanadin rasuwar `yan uwa mata 2, tare da jikkata mutum 6, ciki har da direban motar, wanda har lokacin hada wannan rahoto bai gama farfadowa ba a gadon asibiti.

A’isha Muhammad, matar dan uwa Muhammad Usman (Yawale) ita ce ta rasu nan take. Ita kuwa A’isha Muhammad, matar dan uwa Isah Abbati (Haris), ta cika ne daga bisani a asibitin Gumau.

Daga cikin wadanda suka jikkata, baya ga direban babu wanda ya kai A’isha matar Malam Yakubu Gajin Duguri jin jiki, domin duk cinyoyinta sun karye, kodayake sauran masu jinyar ma mata ne, kowacce da karaya tare da ita.

Da yake ana tafiyar a tawaga ne, motar Alkaleri ne ta fara isowa wajen, sai daga baya motocin `Yan uwa na Bauci suka iso, duk aka taimaka aka kai na asibiti, aka wuce da wadanda suka rasu zuwa Husainiyyah a Zariya.

Kafin su bar gida an ga wacce ta fara rasuwar ta yi sallah raka biyu, ta yi kuma addu`ar Allah ya ba ta shahada. Kuma ta fadi ma mutanen gidan su cewa, “za ku ganni da sababbin sutura nan ba da jimawa ba.”

Ita kuwa ta biyun cewa ta yi, “zan so a ce na biya hakkin Shuhada kafin in je Zariya.”

Shaikh Zakzaky ne ya jagoranci sallar janazarsu tare da wata yarinya `yar shekara 2 wacce ta rasu sakamakon ciwon sankarau a asibitin Shika Zariya. Yarinyar `yar Malamadori ce da ke jihar Jigawa.

Janazar ta samu halartar dubun-dubatan al`ummar musulmi a filin Polo kusa da Husainiyya Bakiyyatillah Zariya.

Malam Ahmad Yusuf Yashi ne ya jagoranci kai su makwancin su da ke makabartar shahidai da ke Dembo (Zariya). Kuma an yi bison ne tare da iyayen wadanda suka rasun.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron