Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1131, ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Dandalin Matasa ya shirya Maulidin Imam Ali (AS) a Rigasa, Kaduna

Daga Wakiliyarmu


Imam Aliy

A jerin gasar da ake yi da ’yan uwa na Dandalin Matasa ke gudanarwa na Mauludin Imamu Ali, Halkar Imam Mahdi su ma sun shirya gagarumin Maulidin, wanda aka yi shi ranar Asabar din da ta gabata a Rigasa, Kaduna...

Taron Mauludin an fara shi ne da misalin karfe 2:00 daidai, yayin da aka fara bude taro da addu’a, sai karatun Alkur’ani, da ziyara, tare da jawabin maraba suka biyo baya.

Takaitaccen jawabi a kan Imam Ali ya fito ne daga bakin daya daga cikin ’yan Dandalin Matasan, hakan kuwa an bullo da shi ne don karawa juna karfin gwiwa wajen bincike da kuma iya magana a gaban jama’a.

Da yake jawabi a wajen, Wakilin Halkar, Malam Awwal Hayi, ya fara ne da taya mahalarta murna a kan wannan rana da ake tunawa da haihuwar wanda babu kamar sa bayan Annabi (S).

A cikin jawabinsa, babban bako mai jawabi a taron, Sharif Isa Ikon Allah Zariya, ya ce magana a kan Imam Ali (S) ba abu ne na wasa ba, kuma da a ce mutane 50 za su yi magana a kansa, za su yi maganganu mabambanta. “To wannan ba zai isa ba mu sani cewa daga Allah babu wani, sai Manzon Allah, sai kuma Imam Ali?”

Ya kara da cewa, Manzon Allah ya ce Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki. “To kun san ko waye wannan haske? Ali ne da sauran A’immatu Ahlul Bait. Mu duba mu gani, ko da Manzon Allah zai tafi Mubahala, bai tafi da kowa ba, sai Ali da Fatima da Hasan da Husaini. Kuma ya ce babu wanda zai yi Mubahala da wadannan hasaken face ya halaka”.

Sharif Isa ya kara da cewa La ilaha Illallahu ba ta cika ba sai ka sa Muhammadu Rasulullahi, sannan ka sanya Aliyu Waliyyullah. Kuma ambaton Ali zikiri ne, lada ake rubutawa mutum idan ya ambaci sunan Ali. Ya zo a zamanin Annabi idan an haifi yaro, kuma ana kokwanto a kan halaccin yaron, to ana kai shi ga Imam Ali ne, idan Ali ya miko hannu yaron ya je ga Ali, to wannan yaron dan halal ne. Amma idan ya ki zuwa ya tabbata ba dan halal ba ne. Haka ma a manyan mutane, ana gane imanin mutum ne idan yana son Ali, sannan ana gane munafuncinsa idan yana kin Ali”.

A karshe ya yi godiya ga Allah da ya nufa aka zabo shi cikin wadanda ake ganin suna cikin mabiya Ali, har aka ce ya zo ya yi jawabi a wannan majalisi mai albarka. “Duk da na ji kun kira ni da Malami, ai duk fadin Afrika Malami guda daya ne, kuma ba za a kuma irin sa ba, wanda ku Shi’a dama kun yarda, mu ma Tijjanawa mun sani mun yarda, kai har ma masu kiran kansu Sunni su ma sun sani, fada ne kawai ba za su yi ba. Wannan Malamin shi ne Sayyid Ibraheem Zakzaky”.

Bayan kare jawabinsa ne aka bukaci manyan baki su taso zuwa ga wani wuri da aka gina rijiyoyi guda uku, wadanda ke alamta rijiyar da Imam Ali ya gina da hannunsa, kuma ’yan uwan sun yi matuka kokari wajen samo ruwan rijiyar na ainihi tun daga Najaf ta kasar Iran aka zuba a cikin wadannan rijiyoyin da aka gina, mutane sun sha sun yi tawassul, sun roki Allah bukatunsu. Sannan aka yanka ‘Cake’, tare da sauran nau’in abincin da Imam Ali ke ci, irin su dabino, nono da gurasa.

Daga karshe an raba kyaututtuka ga wadansu bayin Allah, daga ciki har da kyautar mashin wanda aka bai wa Wakilin ’yan uwa na Rigasa, Malam Awwal Hayi. Daga nan sai jawabin godiya, tare da rufe taro da addu’a.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron