Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1131, ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Sayyida Fatima (SA) Hurul’in ce a siffan matayen duniya

-Malam Abdurrahaman Abubakar Yola
Daga Zainab Abdurrahman


Maulid Sayyada Fatima

’Yan uwa mata almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky na Da’irar Adamawa sun gabatar da bikin murnar zagayowar ranar da aka haifi Shugabar Matan Duniya da Lahira, Sayyida Fatima Azzahra (SA) na tsawon kwanaki uku a jere...

Taron, wanda aka fara gudanar da shi daga ranar Juma’a 25 ga Jimada Thani, zuwa ranar 27 ga Jimada Thani, an fara shi ne da Muzahara, a inda ’yan uwa da ke cikin Jimeta, Yola da kewaye suka yi jerin gwano a ranar Juma’a bayan kammala Sallar Juma’a daga masllacin da ke Nasarawo, inda aka bi manyan titunan da ke cikin garin na Jimeta. ’Yan uwa mata, da maza har ma da yara suna ta yabo da taya al’umma muranar zagayowar wannan rana ta haihuwar Shugabar Matan Duniya.

A gefe guda kuma ga wata ’yar takarda (press release) da take kunshe da takaitaccen bayani a kan Sayyida Fatima (AS) da ake rabawa jama’ar gari.

An karkare Muzaharar ne a bakin masallacin Ganye Street, a yayin da Malam Usman Sa’ad ya gabatar da manufar wannan zagaye da aka yi. Sannan ya mika wa Malama Laurat Musa, wacce take wakiltar ’yan uwa mata saboda ta gabatar da takaitaccen jawabi ga al’ummar da suka yi dafifi a wajen taron.

Malama Laurat ta fara ne da godiya ga Allah (S), daga bisani take cewa kamar yadda aka gabatar, mun ji cewa wannan zagaye mun yi shi ne domin mu taya al’umma murna zagayowar wannan rana, a lokacin guda kuma mu tunatar da al’umma wani abu dangane da wacce aka haifa a wannan rana.

Ta ci gaba da cewa; “Ita Sayyida Azzahra (SA), Allah ya yi mata daukaka ta musamman, sannan tana daga cikin wadanda Manzon Allah (S) yake cewa sune Iyalan Gidansa, kuma ya bar wa al’umma amanarsu bayan wafatinsa. Kuma mu yi riko da su domin sune hujjojin Allah (T), kuma wakilansa a doron kasa, kuma tabbas za a tambaye mu a kan wannan amana da aka ba mu”.

Daga nan ta ci gaba da cewa, ai kuwa mun ga wajibinmu ne mu yi farin cikin samuwar wannan baiwar Allah da ta kasance ita ce mahaifiyar biyu daga cikin su, kuma Kakar tara daga cikin su. Sannan matar na farkonsu.

A rana na biyu kuwa (Asabar), rana ce wacce aka kebe wa yara domin ba su dama na yin wasanni daban-daban. An gabatar da shi ne a cikin gidan Zoo da ke garin na Jimeta. Ya kuma samu halartar yara sama da 500. A yayin da aka gabatar masu da wasanni da suka hada da gudun kwai, gudun buhu, canki-canka, fasa balon-balon, shiga taya, dss, ga kuma jaka da abin ci da sha a ciki, musamman ga wadanda suka yi rijistar shiga harabar taron kan N200 kacal.

A gefe guda ga dawakai na hawa sannan ga zamel-zamel, lillo. Sun kuma yi kallon dabbobin da suka hada da birrai, babba da jakan, maciji, kada, barewa, kunkuru, bushiya, agwagin ruwa, ostroach dss. Ana wajen tun daga safe har yamma.

Rana na uku (Lahadi), shi ne ranar rufewa. An gabatar da taro ne a makarantar a dakin taro na Abraham Guest Hall da ke Poly (Adamawa State Polytechnic Yola). An kawata dakin taron da kyallaye daban-daban masu dauke da sunayen Sayyida (SA), Manzon Allah (S), Iman Ali (AS), Iman Hasan (AS), Iman Husaini (AS), da ma sauran A’imma (AS). Ga kuma na su Malam Zakzaky, har ma da na Iman Khomaini (KS) dauke da “labbaika ya Rasulillah” a jiki. Sannan ga kujerar Sayyida (SA) da aka kawata ta da filawowi daban-daban sai kamshi yake tashi, ga kuma ‘Cake’ a gefe guda mai hawa 14 adadin Ma’asumai. Abin ya kayatar, sai wanda ya gani.

Malam Abdurrahman Abubakar Yola, Wakilin ’yan uwa na Da’irar Yola ne ya gabatar da jawabi a taron. Ya fara ne da godiya ga Allah bisa kyauta da ya yi wa Manzo (S) na haihuwar Sayyida Fatima (SA).

Sannan ya kawo yadda haihuwarta ya kasance a lokacin da matayen Makka suka guji Sayyida Khadija, ya zama ba kowa a tare da ita, sai ga wasu mataye sun zo. Ko da ta gan su sai hankalinta ya tashi, amma sai suka ce mata ki kwantar da hankalinki babu wani abu da zai kasance tare da ke. Sai ma suka gabatar da kansu a gare ta.

A nan take daya ta ce ita ce Hasiya matar Fir’auna, Ummu Kulthum ’yar uwar Annabi Musa, Hajara matar Annabi Ibrahim, sai kuma Maryam ’yar Imran, mahaifiyar Annabi Isa (AS); duk sun zo ne saboda su yi mata unguwar zoma, har ma ita Hajara take cewa ita Asiya abokiyar zamanki ce a cikin Aljanna.

Ya ci gaba da cewa Allah ya daukaka matsayi da darajar Sayyida Fatima birbishin dukkanin mata na duniya. Ta zamanto Sayyidatu Nisa’il Alamin na wadanda suke gabanta da wadanda za su zo nan gaba.

Daga bisani Malam Abdulrahaman Abubakar ya ci gaba da bayyana wa al’umma yadda auren Sayyida Fatima (SA) ya kasance da Angonta Imam Ali (AS), kamar yadda ya zo a rayuwa.

Sannan Malamin ya nuna mana matsayi Sayyida (SA) na mahaifiyar da ta yi tarbiyyar yara, kuma ta ba su ilimi. Sun rayu rayuwa mai tsawo bayan Manzon Allah (T) domin sune tsatson Annabi (S) wadanda Allah (T) yake cewa yana so ya tsarake su tsarkakewa, Allah (T) ya yi amfani da yaran nata domin wanzuwar addininsa da Manzon ya zo da shi.

Daga karshe Malamin ya jawo hankali al’umma inda yake cewa, wajibinmu ne mu masoya, kuma masu koyi, mu yi biyayya ga gidan Manzon Allah (T), mu zamanto maso koyar da abin da suke nuna mana, ba kuma aiwatar da ra’ayinmu ba, domin wannan karani da muke ciki karni ne da yake daf da bayyanar Sahibul Asr (AF).

Ya karkare da cewa; “Ko ba komai muna iya ganin yadda kafircin duniya ke fitar da kisisina da makirce-makirce daban-daban domin sun yi wa Musuluncin bakin fenti, bayan a baya suna rayuwa ce ta duhun kai, Musuluncin ya kawo masu wayewa.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron