AlmizanAlmizan logo
Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1133 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Ziyarar ’yan uwa na Da’irar Kano da Zamfara ga Shaikh Zakzaky

Daga Muhammad Isa


Maulid Hussain

Wasu wakilan ’yan uwa musulmi na Da’irorin Kano da Zamfara a karkashin Mal. Muhammad M. Turi da Mal. Abubakar Nuhu Talatan Mafara, a ran Talata 19 ga Sha’aban 1435 (17/6/2014), suka ziyarci Shaikh Ibraheem Zakzaky a Husainiyya Bakiyatullah...

Mal. Muhammad Turi ya isar da gaisuwar ’yan uwa musulmi ga Shaikh Zakzaky, wanda domin neman albarkarsa suka kawo ziyarar.

Yayin jawabin su Shaikh Zakzaky, ya yi murna da ziyarar, wadda ’yan uwa kan dage suna son zuwa lokaci bayan lokaci.

Daga nan ya kara karfafan ’yan uwa wajen dagewa ga ibadojin wadannan watanni masu alfarma Rajab, Sha’aban da kuma Ramadan mai zuwa. Yana mai karfafan mu a wannan makaranta ta takawa, wanda ake fatan bayan Ramadan za a zarce da takawar da aka samu.

Haka nan Shaikh Zakzaky ya kara nuna taikaicin halin da ake ciki na kunci, talauci, zalunci a kasar nan, wanda maganar kenan a kasar ana mai fama da kisa, fyade ga mata, satan mutane, korar mutane daga muhallansu, banda mamaye tare da satar dukiya da ma’adinai. Mutane na ta wai! wai!! wai!!! ina mafita?

Sannan ya ambaci cewa lallai mu muna da mafita! Muna da mafita domin muna da Shugaba wato Imam Mahdi (AF), wanda a yanzu mataimakansa ne ke tare da mu. Allah (T) na fada mana a kowane zamani akwai Shugaba, “duk wanda ya mutu ba ya da igiyar mubaya’a, ya yi mutuwar jahiliya”. Shi shugaba, jagorar al’umma yake yi izuwa ga Allah (T). Kuma yayin da Shugaba ba ya nan an shar’anta da’awa wadanda su ne mataimakan shugaba. Sauyi da ake samu, sakamakon Shugaba yana da Mataimaka ne, wadanda mataimaka ba lalle ya zama kowa da kowa ba. Rashin mataimaka ya sanya Imaman shiriya (AS) suka wahala wajen kiran al’umma su koma ga Allah (T). Ko nan muna iya ganin kafin a samu sauyi a jamhuriya ta Iran sai da akalla Malamai suka yi gwagwarmayar akalla shekara 100.

Daga nan Shaikh Zakzaky ya yi wa ’yan uwa nasiha da su karfafa zukatansu wajen bin tafarkin Allah (T), su zama masu tabbata a tafarki, suna masu zama daban da wadanda ba su damu da tsayawa a tafarki ba, su kasance mataimaka.

Daga nan ya yi addu’a, yana mai rokon Allah (T) Ya ji tausayin mu, Ya karfafe mu a tafarkinSa, Ya karfafa cire raunin da ke cikin mu, Ya sanya mu a mataimaka Shugaba (AF), Ya sanya sauyi ya zo mana ba da dadewa ba.

Haka nan Sayyid (H) ya kara mana tsokaci da cewa Musulunci bai takaitu a salla da azkar ba, yana mai fassarar ayar “fawailul lil musallin……”, Musulunci dukkan ayyukan rayuwa ne, ka kasance mai aikata dukkan ayyukan alheri.

Bayan addu’a daga Shaikh Ibraheem Zakzaky maziyartan suka koma jihohinsu.

ANA CI GABA DA TAFSIRIN WATAN AZUMIN BANA
Imam KhomeiniAna sanar da dukkan ’yan uwa cewa ana gudanar da Tafsirin watan Ramadan na bana kamar yadda aka saba yi:

Rana:
Daga Laraba 27 ga Sha'aban, 1435

Lokaci:
4:30 ny

Mai Tafsiri:
Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

Wuri:
Hussainiyyah Bakiyatullah
Allah ya ba da ikon halarta

Kuma ana iya sauraron tafsirin a gidajen rediyo ko a kalla a gidajen talabijin da dama daban-daban a fadin kasar nan.

Sai dai mun sami labarin canza lokaci da ake sa tafsirin a gidan talabijin na AIT da ke Kaduna, daga 4:30 na asuba zuwa karfe 11:00 na dare. Sai a kula a duba a sabon lokacin.


Labarai cikin hotuna

Daga manasabobi daban-daban

 • Faretin HarisawaHotunan Gasar faretin Harisawa
 • Faretin HarisawaMalam Zakzaky yana karbar fareti
 • Faretin HarisawaMalam Zakzaky yana zaga sahun Harisawa
 • Faretin HarisawaSashen Harisawa na fareti
 • Faretin HarisawaSashen Harisawa na fareti
 • Faretin HarisawaSashen Harisawa na fareti
 • Faretin HarisawaSashen Harisawa na fareti
 • Faretin HarisawaSashen Harisawa na fareti
 • Faretin HarisawaSashen Harisawa na fareti
 • Faretin HarisawaSashen Harisawa na fareti
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaHotunan bukin yaye daliban Fudiyya Zariya
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaMalam Zakzaky tare da dalibai
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaMalam Zakzaky yana jawabi a wurin taron
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaSashen 'Yan makarantar Fudiyya Zariya
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaMalam Zakzaky a wurin bukin
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaSashen 'Yan uwa a wurin bukin yaye dalibai
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaMalaman Fudiyya Zariya na gwada dalibai
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaSashen 'Yan uwa mata dalibai
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaMalam Zakzaky wurin raba kyaututuka
 • Bukin yaye daliban Fudiyya ZariyaSashen 'Yan uwa mata a wurin bukin
 • Yaumul Mab'asHotunan Yaumul Mab'as
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
 • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
Leka rumbun hotuna ka ga karin hotuna