Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 17 ga Rajab 1435, Bugu na 1129, ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Jama’a su daina rike Macuci a matsayin Maceci

In ji Malam Sabo ATC
Daga Abdul Kwanarya


Harisawa

“Duk al'ummar da take ganin maceci a matsayin macuci, babu ranar da za ta gane daidai.” Mal. Sabo A.T.C ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabin Mauldin Sayyida Zahar (as) da 'yan uwa mata a Wagini da ke yankin Karamar Hukumar Batsari ta jihar Katsina, suka shirya a kwanakin baya. ...

Mal. Sabo ya kawo baiwar da Allah ya yi wa Sayyid Zakzaky na tsamar da al'umma, amma sai suke kallon sa a matsayin wani macuci.

Ya ce, ko jama'a da suke nuna kauna ga Shehu Danfudiyo, ai don sun karanta ne a littafai, da rayuwa suka yi a lokacinsa suka gan shi da idonsu, ba za su yarda da shi ba. Kuma irin wannan ne ya sa suke yakar Sayyid Zakzaky, duk kuwa da cewa shi din ne yake yin aikin da Shehun ya yi.

Ya bukaci al'umma da su auna aikin da Manzo ya yi da wanda Sayyid Zakzaky yake yi, don su yi koyi wanda yake yin aiki irin na Annabi.

Da ya koma a kan matsayi da daraja na Manzo da Iyalansa, sai ya ce, duk wani mutum da ka ji an ce masa “Radiyallahu Anhu,” to bai sami wannan ba, sai da ya yi imani da wannan Manzon. Amma sai ka ga Musulmi suna ko-oho da matsayin Manzo a duk lokacin da ake kawo wasu abubuwa da suke tozarta Annabi, kamar yadda suke kawo cewa yana yin fitsari daga tsaye ko kwana da janaba, amma har yanzu ba a sami wani Limamin gari ko wani babban mutum yana koyi da wannan sunnar ba. Amma da an fadi wani abu a kan wani, sai ka ga ana kumfan baki.

Ta fuskacin iyalan gidan Annabi kuwa cewa ya yi, al'ummar Musulmi sun san darajar 'ya'yan Annabi ne kawai ga sa sunayensu, amma da an ce 'ya'yan Annabi sun fi kowa, sai ka ga Musulmi yana kumfan baki.

Sai ya yi kira ga Malaman al'umma da su yi nutso cikin littattafan da ake da su na Hadisai, su fito da Hadisi goma na ruwayar Fatima (as), idan ba su samu ba, to su tambayi kansu me ya sa diyar Annabi da ta rayu shekaru kusan sha tara, amma ba ta da hadisai, sai wadda ba a yi rayuwar Makka da ita ba take da dubbai.

Mal. Sabo ya kawo darajoji da matsayi na Zahara da Maigidanta Amirul Muminina Ali (as), inda ya bukaci Musulmi, musamman 'yan uwa maza da mata da a yi koyi da riko da wannan gida.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA ZAMAN MAULIDIN IMAM ALI (AS) A ZARIYA
  Za a yi zaman maulidin Imam Ali (AS) na bana, wanda za a yi kamar haka:
  Litinin 117 ga Rajab 1435 (12 ga Mayu 2014)

  LOKACI: 4:00 na yamma

  WURI: Hussainiyah
  Don haka ranar babu karatun Nahjul Balagah.


  GAYYATA ZUWA YAUMU SHUHADA A ZARIYA
  Mu'assasatus Shuhada na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi YAUMUS SHUHADA na bana, wanda za a yi kamar haka:
  Asabar 25 ga Rajab 1435 (24 ga Mayu 2014)

  LOKACI: 9:00 na safe

  WURI: Inda aka saba yi
  Don haka kowa ya tabbatar da ya ba da hakkinsa na wannan shekaran.


  GASAR RUBUTU
  ’Yan uwa mata almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky ba Da’irar Kano da kewaye, sun shirya gasar rubutu a kan:
  Hadisai 20 da Sayyida Fatima (SA), ’Yar Manzon Allah (S) ta ruwaito wadanda ta ji daga Mahaifinta.

  Rubutun kar ya wuce kalmomi 1,000. Za a iya yin sa cikin harshen Hausa, Turanci da Larabci.

  RUFE AMSA: Za a rufe amsa ranar 18 ga Mayu, 2014

  Za a iya aika rubutun kai tsaye zuwa gidan rediyon Pyramid, ko ta Email: [email protected] Ko kuma Fudiyya Nursery and Primary School da ke Rijiyar Lemo, Kano.

  KYAUTA:Duk wacce ta ci za ta samu kyautar mota sabuwa fil

  WANNAN GASAR TA KEBANTA NE KAWAI GA MATA