AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474


Babban Labari

AYYUKAN DAREN LAILATUL KADARI

Daga Alkazeem M. Al-Hasan


Imam Khumaini
Tun a daren 19 da 21 zuwa goman karshe ake fara neman lailatul kadari, amma daren 23 shi ne mafi ingancin dare da Hadisai suka yi nuni da cewa shi ne ma daren Lailatul Kadari. A cikin sa ne ake zartar da dukkan al’amari. A wannan daren akwai ayyuka masu yawa: Daga Fatima Hussaini Rahamawa
Akwai karanta Suratul Ankabut da Rum. An ruwaito daga Imam Sadik (AS) cewa, wanda ya karanta wadannan surorin a wannan daren zai kasance cikin ’yan Aljannah. Na biyu, karanta Suratul Dukhan. Na uku, akwai karanta Inna anzalnahu sau 1000. Lokaci ne na karanta Addu’ar “Allahumma kun liwaliyyika…” Akwai Salla raka’a 100. A kowace raka’a a karanta Fatiha 1, Kulhuwallahu 10. Akwai falala mai yawan gaske ga wanda ya yi wannan Sallar, ya kuma raya daren da ibada. An ruwaito daga Abi Basir ya ce; Imam Sadik (AS) ya ce da shi, yi salla a daren da ake kadarta Lailatul Kadari, kowace raka’a Kulhuwallahu 10, sai ya ce; in zamo fansa gare ka, in ba zan iya yi a tsaye ba fa? Ka sallace ta a zaune. In ba zan iya ba fa? Sai ya ce, yi ta da ishara. An ruwaito cewa, Manzon Allah (S) ya kasance yakan bar shimfidarsa ya ja mizar dinsa don ibada a kwanaki goman karshe na Ramadan. Ya kasance yakan tashi iyalansa a daren 23, sai su sa ruwa a fuskarsu don kar su yi barci a wannan daren. Sayyida Fatima ta kasance ba ta barin iyalanta su yi barci a daren. Takan umurce su da cin abinci dan kadan, sai ta umurce su da su yi barci da rana don kar barci ya yi galaba a kansu a daren. A wannan dare ana yin muhimmiyar addu’ar nan ta Tawassuli da Alkur’ani kamar haka; za ka dauki Alkur’ani ka shimfida shi a tafukan hannayenka, sai ka ce; “Allahumma inniy as’aluka bi kitabika almunazzali wa ma fihi wa fihi ismukal akbaru wa asma’ukal husna, wa ma yukhafu wa yurja, antaj’alaniy min utaka’ika minan naar.” (Sai a roki bukata). Sai a dora Alkur’ani a kai. A fada; “Allahumma bi hakki hazal kur’an wa bi hakki man arsaltahu bihee, wa bi hakki kulli mu’uminin madahtahu fihi, wabi hakkika minka.” Sai ka fada sau 10 “Bika Ya Allahu sau 10, bi Muhammadin (AS) sau 10, bi Aliyyin (AS) sau 10, bi Fadimata (AS) sau 10, bil Hasani (AS) sau 10, bil Husaini (AS) sau 10, bi Aliyyi bn Husaini (AS) sau 10, bi Muhammad bn Aliy (AS) sau 10, bi Ja’afar bn Muhammad (AS) sau 10, bi Musa bn Ja’afar (AS) sau 10, bi Aliyyi bn Musa (AS) sau 10, bi Muhammad bn Aliy (AS) sau 10, bi Aliyyi bn Muhammad (AS) sau 10, bil Hasani bn Aliy (AS) sau 10, bil Hujjati (AS) sau goma. Sai ka roki bukatunka na alheri. Ziyarar Imam Husaini (AS) a cikin Hadisi ya kasance a daren Lailatul Kadari mai kira zai yi kira a sama ta 7 a karkashin Al’arshi, sai ya ce; Allah ya yi gafara ga wanda ya ziyarci kabarin Imam Husain (AS). Su wadannan ayyukan an so a yi a ne a daren19-21-23. Da fatan ba za mu manta da Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah ba. Allah ya kara masu lafiya, ya gaggauta kubuto mana su daga hannun azzalumai. Daga Mafatihul Jinan shafi na 261- 266. Karin bayani a duba littafin Babul Ijaba.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron