AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474


Babban Labari

KU KYAUTATA WA MAMATAN KU (1)

Daga Alkazeem M. Al-Hasan


Imam Khumaini
An ruwaito Hadisi daga wasu cikin Sahabban Annabi (S) suka ce; Manzon Allah (S) yana cewa: “Ku bayar da kyauta ga mamatanku”. Sai muka ce; Ya Manzon Allah (S) ta yaya ne za mu yi kyauta ga mamatanmu?
Sai ya ce: “Yin sadaka da Addu’a”. Sannan ya ce: “Rayukan Muminai suna zuwa a kowace ranar Juma’a zuwa saman duniya, da takalman matsayinsu da gidajensu, kowane dayansu zai yi kira da sauti na bakin ciki (cikin damuwa) yana kuka, yana fadin ‘ya ku iyalaina! Ya ku ’ya’yana! Ya Babana! Ya Ummata da makusantana! Ku tausaya gare mu, Allah ya yi rahama gare ku. Da abubuwan da muka bari a hannayenku (na dukiya) narkon azaba da hisabi a kanmu, amfani kuma ga waninmu’. Sai kowane dayansu ya kira makusantansa, ku tausa yamana, ko da Darhami ne, ko ma abin da bai kai hakan ba, ko da wasu tufafi ne, Allah ya tufatar da ku tufafin Aljanna. Sai Annabi (S) ya fashe da kuka, muka yi kuka tare da shi, har sai da ya kai ba ma jin abin da yake fada, saboda yawan kuka. Sai mai tsira da aminci ya ci gaba da cewa: wadannan fa su ne ’yan uwanku a addini, an mayar da su kasa, rududugaggu bayan jukkunansu, da jin dadi, suna kiran kaiconsu, da tabewa, ga kawunansu. Suna cewa: ya kaiconmu, da mun sani da mun sanya a idanunmu bin Allah da neman yardarsa. Da ya zamo kwalliya gare mu. Da ba mu zo da bakin cikin a hasararsu ba, da kuma da na sani, suna yin kirana a gangaro musu da sadaka su matattun”. Mafatihul Jinan Fasalina 10 shafi 593.

Don karin bayani a duba littafin Babul Ijaba.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron