AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Shekara 40 da shelanta Harkar Musulunci

Daga Saifullahi M. Kabir


gwamna
P>Ranar Lahadin nan da ta gabata 5 ga Afrilun 2020 ne, Da’awar kira zuwa ga komawa tafarkin Allah da Shaikh Ibraheem Zakzaky ke jagoranta ta cika shekara 40 daidai da shelantawa a kidayar Miladiyya.

Shaikh Ibraheem Zakzaky ya shelanta wannan Da’awa, wacce a yanzu aka fi kiran ta da suna Harkar Musulunci ne a yayin wani taron bitar karatu (IVC) da Kungiyar Dalibai Musulmi (MSS) ta shirya garin Funtuwa a ranar 5 ga Afrilu, 1980, wanda ya yi daidai da 20 ga Jimadal Ula, 1400 Hijiri.

Shaikh Zakzaky a matsayinsa na matashin da ya fito daga gidan Malaman addinin Musulunci, bayan shigar sa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) a shekarar 1976, ya iske ana muhawara a tsakanin daliban Jami’a a kan me ya kamata ya zama makomar kasa ne.

A yayin da ya zama akwai kungiyar Kiristoci ta FCS, suna ganin cewa nizamin da ke tafi da kasar nan a wannan lokacin ya wadatar a ci gaba da shi, suna cewa a wajensu addini daban ne, rayuwa daban. Akwai kuma masu ra’ayin Kwaminisanci, da suke ganin dole a samu sauyi domin nizamin da ke iko zalunci yake yi, amma suna ganin nizamin Kwaminisanci ne kawai zai kawo adalci ga kasar nan.

’Yan Kwaminis sun rika sukar addini a kan cewa zalunci ne. Suna ba da hujja da yadda Sarakunan Banu Umayya da Banul Abbas da ma Sarakunan gargajiya suka rika sheka zaluncinsu ga mutane da sunan addini a tarihi. Don haka suna ganin tsarin Kwaminisanci shi ne kawai nizamin da zai kawo adalci ga mutane fiye da komai.

Sai ga Shaikh Zakzaky da tasa matsayar ta daban a karkashin inuwar Kungiyar Dalibai Musulumi ta kasa (MSS) cewa matsayar Kungiyar Musulmi shi ne tabbas duk zargin da bangarori biyun suke jingina wa addinin Musulunci korarre ne, inda ya rika shirya laccoci daban-daban na fadakarwa, da yin martani ga Kwaminisawa da masu ra’ayin Kiristoci a kan cewa addini saukakke ne daga sama, kuma masu aiki da shi suna bambanta, ba komai ba ne idan Musulmi ya yi sunansa Musulunci, saboda haka abubuwan da su Sarakuna da Daulolin suka yi da yawa ya saba wa koyarwar addini, don haka ba shi ne Musulunci ba.

Shaikh Zakzaky ya rika wanke addinin Musulunci da cewa, a kawo inda aka ga zalunci a tarihin gwamnatin da Manzon Allah (S) ya kafa na tsawon shekaru 10 a Madina. Ya kuma rika tabbatarwa da mutanen Jami’a cewa komawa ga addinin Musulunci shi ne kadai mafita wajen samun adalci da wadatuwar arziki da samun aminci. Daga irin haka ne ya fara kira ga komawa ga addinin Musulunci, da yunkurin tabbatar da shi ya yi iko a doron kasa, tun a shekararsa ta farko a Jami’ar.

Shaikh Zakzaky ya rika wannan ne ta hanyar shirya laccoci, da fadakarwa a yayin tarukan IVC na dalibai Musulmi da rubuta ‘articles’ a raba ko a manna su da sauransu.

Tarihi ya nuna cewa tun shekarar farko na Shaikh Zakzaky a Jami’a, a watan Disamba, 1976 an yi wani IVC na MSS garin Gombe, a lokacin sai Shaikh Zakzaky ya fara bijiro da bukatar kowane Musulmi ya je ya yi nazari dangane da me ya kamata ya zama mafita a kasar nan. A lokacin Shaikh Zakzaky ya bijiro da hakan ne ya bar mutane su je su yi wa kansu tunani ba tare da ya fada masu abin da ya kamata su yi ba.

Bayan watanni biyar, da aka koma irin wannan taron na IVC din a watan Afrilu, 1977 a garin Katsina, sai Shaikh Zakzaky ya sake bijiro da batun tattaunawa a kan abin da ya kamata ya zama mafita ga kasar nan. A nan ne har ya kirkiri wani tsari da mutane za su rubuta sunayensu a kan sun amince ya zama an fara kokarin samar da yunkurin samun sauyin addinin Musulunci a kasa tare da su.

Shaikh Zakzaky ya saka wa daidaikun mutanen da suka amsa wannan kiran a lokacin suna External Enlightenment Division (EED). Sai suka kasance bangare ne su na Kungiyar Dalibai Musulmi (MSS), amma sun kara wa kansu da wasu ayyukan na daban. Tun daga wannan lokacin duk sad da aka je taron IVC, bayan an kammala, sai su kebe kansu su yi zama, su tattauna, sannan Shaikh Zakzaky ya gabatar masu da karatu na musamman don kwakkwafe fikira.

A watan Disamba,1978 bayan an kammala taron Kungiyar MSS, wato IVC a garin Potiskum, sai Shaikh Zakzaky tare da membobin wannan EED din da ya tsara suka kara kwanaki biyar, inda suka rika tattaunawa a kan addini ne ya kamata ya zama makomar kasa. Kuma ya kamata ya zama su sun kimtsawa kawo wannan sauyin. Don haka a lokacin suka karanta wani littafi mai suna THE PROCESS OF ISLAMIC REVOLUTION (wato hanyoyin da ake bi wajen kawo sauyin Musulunci) na Shaikh Abul Aala Maududi.

A Disamba, 1978 ne, labarin Marigayi Imam Khumaini, wanda a lokacin yake gudun hijira a Faransa ya gama bin duniya, kuma mutane na ta Muzaharori don neman sauyi a Iran. A wannan lokacin ne su Shaikh Zakzaky su ma suka fara jin labarin Imam Khomaini, wanda a farkon shekarar 1979 kuma sai ga juyin juya-halin Musulunci ya auku a Iran bayan da Imam din ya koma kasar a tsakanin watan Junairu zuwa Fabrairun wannan shekarar.

Juyin Musulunci na Iran ya bai wa Shaikh Zakzaky da wadanda suka amsa kiransa karin kwarin gwiwa a kan cewa ashe Da’awar da suka faro na cewa za a iya komawa tsarin addinin Musulunci mai yiwuwa ne, tunda ga shi a wannan zamanin wani Malamin addini da rawani da farin gemu, ya iya jagorantar hakan.

A littafin tarihin Harkar Musulunci, Shaikh Zakzaky ya ambata cewa: “To, ka ga muna iya cewa shi juyin Musulunci din Iran da yawan mutane sukan ce ko shi ne asalin Harkar Musulunci a Nijeriya, amma kamar yadda na ba da labari a hakika tun kafin sa ne, amma shi da ya auku ya kara ba mu karfin gwiwa ke nan kawai. Ya nuna mana cewa abin da muke kira gare shi zai auku, tunda ga shi ya auku a Iran”.

Shaikh Zakzaky ya ce: “Da can mutane suna ce mana ai wannan abin da kuke kira (na a komawa addini) sam ba zai yiwu ba. Zan iya tunawa a wata shekara, wata lacca da muka taba yi aka sanya mata suna; “The Beginning Of The Beginning”, sai muka kawo tarihin yadda addini ya kafu a duniya da kuma yadda daga baya ‘Colonialists’ (Turawan mulkin-mallaka) suka taso, da yadda suka kawar da karfin addinin Musulunci, da kuma yadda yanzu muke hankoron addinin ya taso.

“Sai mutane suka ta yi mana raddi, har akwai wanda ya ce mana ai dalilin da ya sanya addinin Musulunci ya mallaki duniya don a wancan lokacin kai bai waye ba ne, amma yanzu ina ku ina wannan? To, har ma na san na yi masa raddi, ‘in form of poetry’ (a sigar rubutaccen wake) ya yi, har na yi masa raddin ‘poetry’ din nasa.”

Shaikh Zakzaky ya ci gaba da cewa: “Juyin Musulunci a Iran ya nuna na farko dai abin da muke kira a kai mai yiwuwa ne, tunda ga shi har ya yiwu a wani wajen. Ka san kana kira ga abu, kana tunanin kila ma ba zai yiwu ba, kana dai yi ne kawai; amma yanzu ka tabbatar da kwarin gwiwa, idan ma wani yana ganin zai yi maka kule, ya ce maka ai ba zai yiwu ba. Sai ka ce masa ai ga shi Ayatullah ya yi. To, wannan kuma sai ya mai da tunaninmu cewa lallai to yanzu mun samu ‘symbol’ (alami), mun samu ‘leadership’ (jagoranci), mun samu wani ‘frame of reference’ (abin kafa misali) a wannan lokaci namu.”

Daga wannan lokacin, duk da cewa yanzu Shaikh Zakzaky ba yana mazaunin dalibin Jami’a ba ne, tunda ya kammala karatun Digirinsa a wannan shekarar ta 1979 ne, amma ayyukan Harkar Musulunci sun fara kankama, kuma bai gushe ba yana matsayin mataimakin Shugaban kungiyar ta MSS na kasa kan harkokin kasashen waje. Don haka sai ya ci gaba da amfani da ta’alimomin da yake wa dalibai da kuma tarukan dalibai na IVC wajen ci gaba da karfafa Da’awar kira ga yunkurin tabbatar da addini a doron kasa.

A watan Disamba, 1979 aka yi wani taron IVC a garin Wudil ta Jihar Kano, inda a nan ma bayan kammala taron na IVC, Shaikh Zakzaky ya shiga karatu da kebantattun ’yan’uwan nan da suka saba, inda ya fara karanta masu wani littafin Sayyid Kutub, mai suna Milestone, wanda ke bayani a kan Imani da gwagwarmaya a tafarkin Allah (T), duk a kokarinsa na kwakkwafa tunanin ’yan’uwan.

A karshen watan Junairun 1980 (12/3/1400H), Shaikh Ibraheem Zakzaky ya tafi Jamhuriyar Musulunci ta Iran a karo na farko a karkashin Kungiyar Dalibai Musulmi na kasa (MSS), wanda har a lokacin shi ne Mataimakin Shugaban kungiyar kan harkokin kasashen waje.

Wannan ziyarar da Shaikh Zakzaky ya kai Iran, ta shafe kusan makonni biyu a can, inda ya dawo a ranar 14 ga Fabrairu, 1980 din. Kuma a yayin wannan ziyarar Shaikh Zakzaky ya samu tagomashin ganawa da Jagoran juyin-juya-halin Musulunci na Iran, Ayatullah Imam al-Khomeini (KS), Imam din ya yi masu jawabi, kuma har Shaikh Zakzaky ya dauko a kaset ya yi tsaraba da shi. A yayin ziyarar, Shaikh Zakzaky, ya kuma shaidi bikin cika shekara daya da nasarar juyin Musulunci a Iran, wanda ake gudanarwa a 11 ga Fabrairu.

Bayan dawowar Shaikh Zakzaky daga Iran, ya rika shirya laccoci a manyan Jami’o’in kasar nan da suka hada da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), Jami’ar Jos, Jami’ar Lagos, Jami’ar Bayero Kano (BUK), Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato da sauransu, inda ya rika ba da labari a kan abubuwan da ya gani na ci gaba a jamhuriyyar Musulunci ta Iran a yayin ziyararsa, tare da kunna kaset din jawabin Imam Khomaini da ya dauko yana wa mutane fassara kamar yadda shi ma aka yi masa.

Wannan ya kara farkar da al’umma, musamman ma dalibai Musulmi cewa, Musulunci mai yiwuwa ne a kasar nan, matukar an tashi an yi yunkurin kafuwar sa. Har a lokacin Shaikh Zakzaky na sanar da su cewa, abin da ke kanmu shi ne mu tashi mu yi kiran, idan an amsa shi ke nan, in ba a amsa ba ma akalla zai zama mun samu uzuri a wajen Allah (T) a kan cewa mun ga ana wani abu da ba addininsa ba, mun yi ma wannan abin tawaye, kuma mun tashi mun fadakar da mutane a kan illar bin wannan abin da ba addini ba, amma sun ki su amsa mana a hadu a koma bin addini, har ga shi mun komo gare ka Allah.

Idan mai karatu ya lura, dama a kowane watan Afrilu da Disamba ne ake yin taron kara wa juna sani na kungiyar dalibai Musulmi (IVC), wanda a kan kai shi garuruwa daban-daban. Don haka a watan Afrilu din shekarar 1980, sai aka gabatar da IVC din a garin Funtua.

A ranar 5 ga Afrilun 1980 (daidai da 20 ga Jimadal Ula, 1400H), duk da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky ba yana matsayin dalibi ba ne a lokacin, amma dai har a sannan shi ne mataimakin Shugaban Kungiyar Dalibai Musulmi (MSS) kan harkokin kasashen waje, a wannan taron da kungiyar ta gabatar a Funtua, Shaikh Zakzaky sai ya wakilci Shugaban kungiyar na lokacin wanda bai samu halarta ba, don yin jawabin rufe taro.

Maimakon baya da aka shafe shekaru kusan hudu ana Da’awa ne a sirrance a tsakanin wasu dalibai kawai, a wannan ranar (5/4/1980) Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fara shelanta Da’awar kira zuwa ga tafarkin Allah a gaban dandazon al’ummar Musulmi a garin Funtua da ke Jihar Katsina. Al’amarin da aka ambace shi da ‘Shelar Bara’a a Funtua’ ko “Funtua Declaration” a Turance.

A cikin jawabin, Shaikh Zakzaky ya bayyana ukubar da ke kan Musulmin da ya ga wani Shugaba azzalumi na zalunci a kan bayin Allah, amma ya yi shiru da bakinsa ya kame hannayensa, cewa Allah zai hada su a makoma daya da azzalumin. Ya kuma nuna cewa mu a nan kasar ba kawai mun goyi bayan zalunci ba ne, mu ne ma muke zabar azzaluman.

Sannan ya bayyana tawayensa ga azzalumai da tsarin zalunci da kafircin da ya dora su a kan mulki. Sannan ya nemi shaidar Allah da ta Muminai a kan cewa, ya mika wuya ga Allah da shari’arsa.

Tun daga wannan lokacin Shaikh Ibraheem Zakzaky bai gushe ba a tsawon wadannan shekarun a kan wannan shelar yake, Da’awarsa ba ta gushe ba a kan wannan shelar take gudana, hadafinsa ke nan, manufarsa ke nan. Wato kira ga al’ummar Musulmi kan tawaye ga duk wani tsarin da ya saba wa shari’ar Allah, da kiran su zuwa ga haduwa don yin gwagwarmayar yunkurin tabbatar da addinin Allah da shimfida shari’arsa a doron kasar nan da muke zaune.

Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa mahukuntan kasar nan daban-daban da suke ganin cewa, Shaikh Zakzaky da Da’awarsa na kokarin kawo karshen nizamin da ya mai da su shugabanni ne, suka rika yunkurin kashe shi, ta hanyar kama shi da daure shi da azabtar da shi na tsawon shekaru a tsawon wadannan shekaru 40 din.

Na baya-bayan nan shi ne, wanda gwamnatin nan ta Buhari ta yi na auka wa Shaikh Zakzaky da almajiransa a ranar Asabar 12/12/2015, inda suka kashe mutane sama da 1,000, tare da rushe gida, makaranta, makabartar Shahidai da ta Mahaifiyarsa, Cibiyar taruka ta Fudiyya Islamic Center, bayan sun kama shi da mai dakinsa Malama Zeenah sun tsare tsawon shekaru ba tare da wani dalili ba, duk da raunukan da suka ji masu na harbin bidinga, ba tare da sun bari sun tafi neman magani ba.

Yadda aka yi bikin cika shekaru 40 da Shelar Funtuwa

Daga Husaini Baba

A ranar Lahadi 05/04/2020 ne, shelar Harkar Musulunci da Shaikh Ibraheem Yaqoubu Zakzaky ya yi a makarantar sakandire ta GSS Funtuwa ta cika shekaru 40.

Hakan ya sa ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky na yankin Funtuwa suka gudanar da gagarumin bikin tunawa da wannan shelar, wacce ake kiran ta da ‘Funtua Declaration’ a Fudiyya Shuwaki.

A jawabin da ya gabatar a wajen taron, Shaikh Rabi’u Abdullahi Funtuwa, ya bayyana cewa; “Wannan shelar abar murna ce da alfahari a gare mu ’yan’uwa na Yankin Funtuwa, saboda wannan baiwa da Allah ya albarkaci wannan garin namu na Funtuwa da ita.”

Shaikh Rabi’u Abdullahi, ya bayyna cewa; “Shaikh Zakzaky ya dade yana Da’awarsa, ya kuma bayyana ta ne a wannan gari namu da ya wakilci Shugaban Kungiyar Dalibai Musulmi na MSS. A lokacin shi ne mataimakin Shugaba mai kula da kasashen waje. Da ya zo jawabinsa ya bayyana cewa, ya ji Manzon Allah na cewa, wanda ya ga Shugaba na zalunci kuma ya ki yi masa magana don hana shi zalunci da hannunsa ko da bakinsa, ya rage wa Allah ranar gobe kiyama ya yi masu makoma daya da wannan azzalimi. Don haka ya ce ‘ku shaida ni na yi wa azzaluman shugabanni tawaye’. Ya fadi haka ne ranar 05/04/1980, wanda ya yi daidai da 20 ga Jimada Ula 1400 bayan hijira.”

Ya kara da cewa; “Shelar Funtuwa, shela ce ta ceto al’ummar kasar nan daga mawuyacin halin da ake ciki na zalunci da danniya ga Musulmi da wadanda ma ba Musulmi ba. A kan haka ne shugabanin kasar nan suke ta yunkirin ganin bayan Shaikh Ibraheem Zakzaky, don babu wani Shugaban da bai yi sa’ayi ba na ganin bayan Malam.”

Shaikh Rabi’u Abdullahi ya ci gaba da cewa; “Yanzu haka duniya ta shaida cewa, Shaikh Zakzaky na Allah ne, kuma ba shi da gata sai Allah, duk yunkurin da azzalumai ke yi na ganin sun halaka shi da rushe da’awarsa sun gaza. Don haka muke kira ga ’yan’uwa da su ci gaba da yin biyayya ga Jagora Sayyid Zakzaky. Kuma mu ci gaba da fafutukar ganin Jagoranmu ya samu ’yanci daga hannun azzaluman da ke neman ganin bayansa.”

A wajen wannan bikin wasu daga cikin bangarorin Harka sun bayyana ayyukan da suke gabatarwa al’umma don taimakon su.

A bangaren Harisawa, Ahmad Ibrahim ya bayyana cewa, suna gadanar da ayyukan ci gaban al’umma, kamar aikin gayya da gyaran kwalabatoci da gyaran bohol, wanda a Yankin Funtuwa kadai, Hurras sun gyara bohul sama da 300 kyauta don taimakon al’umma.

A bangaren ISMA masu kula da harkar lafiya kuwa, Malam Kasimu Ibrahim, ya bayyana cewa Shaikh Zakzaky ya koyar da su taimakon al’umma wajen ba da gudummawar jini don sanya wa marasa lafiya da kuma yi wa yara kaciya kyauta.

A karshe Malam Muhammad Ashiru ya mika godiyarsa ga wadanda suka jagoranci shirya wannan gagarumin biki, tare da fatan Allah ya saka masu da alherinsa, kuma ya mai da kowa gidansa lafiya.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron