AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474


Babban Labari

JINGIR YA JINGINE BARA'ARSA

Daga Bilal Nasir Umar


apc

Shaikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, kamar yadda ake kiran sa, ya yi amai ya lashe a cikin satuka biyu da suka gabata. Ba kasafe dattijo ke wannan abin kunya ba, ko da a ce dattijon Ukari ne.

Alkawari da cikawa sune bambanci tsakanin Tsoho da Dattijo. Kwanaki kadan kafin Juma'ar da ta gabaci wacce ya lashe aman da ya yi, an ji shi ya rantse cewa babu dan sanda ko Sojan da zai hana shi Sallar Juma'a. Ga fikihu wannan rantsuwa da ya yi ana ce mata ‘yaminul-birri.’ Saba mata yana tilasta kaffara.

Lokacin da Jingir ya ci laya a gaban dan jarida, sai ’yan kasa suka rika shaukin Allah ya kawo ranar Juma'a su ga fada da cikawa. Rana ba ta karya, kamar yadda Hausawa suka ce. Kafin ka ce Isma'ila Idris shi ne ya assasa Izala, sai ga Juma'a ta bawa babbar rana ta zagayo. Da safe sai ga jami'an tsaro sun je farautarsa har gida. Ba a san ta ina ya fita ba. Watakila ya tuna da lakabin kaka da kakanni. Tabbas bai isa ya ce kakaninsa ba su yi ta'ammuli da layu ba, domin kuwa su ba ’yan Izala ba ne.

Ba a ankara ba, sai ga Malam a masallaci. Amma kafin ya isa masallacin, sai da Lauyan kungiyarsa da aka fi sani da Isma'iliyya tsantsa, ya share masa hanya a gun jami'an tsaron da suka isa masallacin a cikin shirin ko ta kwana.

Yana isa, sai ya yi huduba ’yar guntuwa. Ka san shi, da mutanensa, ba su saba sallah a gaban haunayen Najeriya ’yan ina-da-kisa ba. Bayan huduba ya harba ’yan raka'o’i biyunsa na Juma'a, kamar yadda aka saba. Da yake ’yan lelen Buhari ne, ba a bude musu wuta ba. Ganin ya sussuka, ya samu tsaba, sai ya kara wata huduba gajeruwa da kowa zai kira bidi’a. Ya ce shi da irin nasa mutane masu tunani irin nasa, ba su yarda da cutar Korona ba. Wannan 'jarunta' ta burge yaran da suka je sallar tare da shi. Ka san in kida yayi dadi, ana rawa ba wando. Har yara suka raka shi gida. Kafin su watse suka kara wata sabuwar 'bidi’a ko in ce 'haramiya.' Suka rera wata waka mai dadi, amma ba dadadawa.

"Malam ya ce babu Korana, mu ma mun ce babu!" Wannan ita ce amshin wakar. Washe kare aka gayyace shi gidan gwamnati ko ofishin haunayen Buhari, DSS kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito. Babu labarin abin da ya gudana a tsakanin Jingir da Gwamna Lalong ko DSS. Sai dai wannan ganawa ta canza matsayar Jingir cikin gaggawa. Ba da jimawa ba takardar manema labarai ta fito daga ofishin Izala Bajasiya da Jingir ke jagoranta. Shaikh Nasiru Abdul Muhiy, Shugaban kungiyar, shi ne ya sanya hannu a kan takardar. Abin da ke cikin takardar shi ne sanar wa duniya cewa, sun ba da kai bori ya hau. Sun rufe makarantu da duk wani abu makamancin haka. Kamar kullum, takardar ta yaba wa gwamnatin Tarayya da ta jiha kan namijin kokarinsu na hana yaduwar cutar Korona.

Ashe wuya, ko da magani ba dadi. Tambaya a nan ita ce dama gaban kai kawai Jingir ya yi, bai tuntubi shugabannin kungiyarsa ba? Duk da haka jama'a ba su sakankance cewa sabon jarumi Jingir ya aminta da matsayar kungiyarsa ba, sai da Juma'a ta sake dawowa, aka ga wani sabon salon da, da wuya a kira shi sallar Juma'a a hakikanin ma'anarta a masallacinsa.

Sai dai wannan magana biyu daga Jingir tabbas za ta bar baya da kura, hatta a gun mabiyansa, imma ba ta canza sunansa daga Dattijo zuwa Tsoho ba. Tsohon ma na Najadu. Ko ta canza masa suna yanzu, babu wani abu sabo. Da dadewa sunansa ya canza daga Malami mai fadar gaskiya zuwa Malami mai fadin abin da ba shi da tabbaci a kai. Wannan gare mu ’yan Shi'a da ’yan’uwanmu Sufaye ke nan.

Jingir ya taba zuka wata karya, inda ya ce, wai an samu ‘Condom’ kwando- kwando a wata makaranta a garin Kura ta Kano, inda masu tattakinmu suka kwana a hanyarsu ta zuwa Zariya daga Kano. Kafin nan kazafi ga Shi'a da Shi'awa ya zama kamar cin abinci a gare shi. Karyar yau daban da ta gobe. Ga ’yan’uwanmu Sufaye, sai dai a ce su kara hakuri. An yi yayin musu sharri shekaru aru-aru har yanzu ba a gaji ba.

Ganin bara'ar da Jingir ya yi na fito-na-fito da gwamnati ya sa wasu suka zaci cewa bara'a ta fara shiga daftarin Izala Bajasiya. Ina! Ana zare masa ido, sai ya yi ladab. Wannan ya tabbatar da maganar da ke cewa bara'a tana tafiya kafada da kafada da wilaya. In babu wilaya a zuciyar mai bara'a, tabbas bara'a ba ta da gurbin zama a gun mai zuciyar.

Bara'a ba kayan wanda ke faganninya a dajin wahabiyanci ba ne. Bara'a aikin shiryayyu ne masu rike da shiryayyun da Manzon Allah ya tabbatar da shiriyarsu. Wannan shi ne sirrin bara'ar Shaikh Zakzaky da mabiyansa. Gashin bakin dansanda ko Soja sunyi kadan su sa Shaikh Zakzaky ya fasa abin da ya rantse zai yi. Yanzu ya kamata Jingir ya yi karatun ta natsu a nan gaba. Ya gane cewa, ba duk kamar maza ka maza ba. Ya fahinci cewa rundunar Aliyu bn Abu Talib ne kawai suke bara'a da jure wa wahalar da bara'a za ta jawo musu. Ba mabiya Sarakunan farko da Malumansu ba.

Wannan shi ne dalilin da ya sa masu rawunna uku ne kacal da mabiyansu suka rike wa Yahudu da Nasara wuya a duniyarmu ta yau. Dukkanin su jinin Imam Ali ta hanyar ’yar Manzon tsira, Muhammad, iyayena su zama fansa ga kurar takalmansa.

Ba mai hankalin da zai zaci cewa farangaitacciyar bara'ar Jingir za ta dore. Da ma burga ce, a haka kuma ta kare. Ba a shuka rake a samu dabino, kamar yadda ba a matsa gyada a samu nono a cikinta! Haka ma kare ba zai yi farautar kura ba. Tabbas Jingir da makamantansa bayin hukuma ne, ko sun ki ko sun so. Hukumar kuma ko wacce musulmi ko kafiri ke wa jagoranci, duk daya ne a gare su, balle a ce hukumar na ba da Naira.

Fatanmu ga Jingir da ire-irensa shi ne shiriya, domin mu gudu tare, mu tsira tare. Kodayake abin da wuya, wai dan daudu da wasa da maciji. In haka ba ta samu ba, dole a yi ta maimaita abin da ya faru a baya na kaffara a sakamakon ‘yaminul birri.’ A yi ta baganniya a dajin dimuwa har mai kira ya yi kira. Allah ne ya san gaibi. Yanzu kam za mu yi wa Jingir gori, ba sharri kamar yadda ya yi mana ba. Gorin shi ne. JINGIR YA JINGINE BARA'ARSA! YA JI TSORO A BA SHI KUNUN MADACI!!