AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474


Babban Labari

’Yan sanda sun kashe mutum 6 a Kaduna

Wakilinmu/font>


P>A yayin da cutar Koronabairus ba ta kashe ko da mutum guda a jihar Kaduna ba, sai ga shi hadin gambizan jami’an tsaro na Civilian JTF da ya hada da ’yan sandan da ’yan Kato-da-gora da aka tura unguwar Tirkaniya a garin Kaduna don yin sintirin hana jama’a fitowa daga gidajensu sun bindige akalla mutum shida a ranar Litinin da ta gabata.

Wakilinmu ya kalato cewa jama’a ne suka fito cin wata kasuwa a ranar Litinin din da safe. Ba jimawa sai ’yan sintirin suka zo, samari matasa suka kora su. Zuwa can da rana sai ga shi jami’an tsaron sun zo da karfinsu. Da farko suka harba tiya-gas, amma karshe suka yi amfani da harsasai mai rai kan matasan.

Mahaifin Musa Aliyu dan shekara 30 da ya rasa ransa, mai suna Mal. Aliyu da ke titin Dogaje Street a Tirkaniya ya shaida wa ’yan jarida cewa dansa ya fito daga wanka ke nan, ya nufi kofar gida don ganin mai ke faruwa, sai harsashin ’yansanda ya same shi a kirji, wanda ya zama ajalinsa a Asibiti.

Wakilinmu ya ganewa idonsa matasa da dama da al’amarin ya rutsa da su kuma suke karbar magani a wani Asibiti.

Amma a lokacin da aka nemi jami’an ’yan sanda su ce wani abu kan hatsaniyar, sai suka ce ba za su ce komai ba, sai sun gama bincike.