AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Abin jiya ya dawo a Katsina, ’Yan bidinga na mamayar garuruwa

Daga Aliyu Saleh da Haruna Yakunu


Tun a tsakiyar shekarar da ta gabata aka samu lafawar hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane domin kar~ar ku]in fansa, musamman a {aramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina, bayan wani zaman sasanci da aka yi tsakanin maharan da kuma gwamnati. Sai dai a ’yan kwanakin nan za a iya cewa abin jiya ya dawo, domin kusan kullum sai an samu labarin hare-haren da mahara ke kaiwa a garuruwa daban-daban na {ananan Hukumomin Jihar Katsina. A ranar 8/4/2020 wasu gungun ~arayin shanu sun yi dirar mikiya a }auyen Batsarin Alhaji, inda suka sace dabbobin garin, bayan sun kwashe tsawon lokaci suna harbe-harben bindigogi a cikin garin. Daga baya dabbobin sun dawo, bayan mutanen yankin sun samu agaji daga wasu dakarun daji masu biyayya ga sasancin da aka yi. A ranar 10/4/2020 maharan sun sake kai hari garin, amma dai ba su samu nasarar tafiya da dukiyar mutane ba. A ranar 15/4/2020 ’yan bindiga sun shiga garin Wagini, inda suka shiga gidan Alhaji Tanimu suka yi awon gaba da matarsa Sa’adatu tare da ]an jinjirinta na goye. Sun nemi ku]in fansa Naira miliyan 15. Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto tana hannunsu. A ranar 19/4/2020 sun je garin Watangadiya, suka kashe mutum ]aya Shehu [an Iya, suka ji wa ]aya rauni. Haka ma a ranar Asabar 2/5/2020 wasu gungun ’yan bindiga sun kai hari wasu gidajen gona da ake kira Gajen-Haro, suka kashe mutum biyu, tare da sace dabbobin garin. A ranar 4/5/2020 wasu ’yan bindiga sun kai hari }auyen Saki Jiki, suka kashe mutum ]aya mai suna Malam Ayuba, suka jikkata ]aya, suka yi garkuwa da mutum ]aya. Daga baya suka nemi ku]in fansa Naira milyan 10. Har zuwa wannan rubutun yana hannunsu. A ranar 5/5/2020 wasu mutum biyu a kan babur da ake zaton ~arayi ne sun sake kai hari garin Wagini, inda suka shiga shagon cajin waya suka sace wayoyin mutane, kana suka harbi mai shagon mai suna A}ilu Baba, yanzu haka yana jinya a babban asibitin Batsari. Duk dai a wannan ranar ta 5/5/2020 maharan sun kai hari garin Sabon Garin Yasore, sun kashe Aminu Ado, suka ji wa mutum hu]u rauni; Sabi’u Adam, Lazi Jikan Shawai, Lurwanu Tako da Musa Abu. Bayan sun yi ]auki-ba-da]i da ~arayin, mutanen }auyen sun yi nasarar }wato dabbobinsu da suka sace. A ranar 6/5/2020 wasu masu garkuwa da mutane sun je }auyen Madaddabi suka yi awon gaba da wata Amarya. Daga baya sun sake ta ba tare da an biya ku]in fansa ba. Hari mafi muni shi ne wanda maharan suka kai a ranar 7/5/2020, wanda suka mamaye garuruwa har 10; Salihawar, [an Alhaji, Goje, Bawo, Sire, Tsugunni, Kurmiyal, ’Yan Gayya, Mai [oriya da Tsalle [aya a dare ]aya, tare da sace Shanu, Tumaki da Awaki sama da 3000, A garin Goje sun kashe mutum ]aya mai suna Malam Kabir,Bawo, sun ji ma mutum hu]u rauni. A garin Watangadiya, a nan sun harbi Malam Yahya, ]an’uwa almajirin Shaikh Zakzaky. Daga bisani ya rasu a babban asibitin Katsina. A ranar 8/5/2020 wasu gungun ~arayin Shanu sun auka wa garuruwan Tsohuwar Ruma, Sabuwar Ruma, Kuka Ukku da Ce]iya, sun kashe mutum biyu; Hamza mai nama da Ididda, sun ji wa biyu rauni a garin Tsohuwar Ruma. Haka ma a Ce]iya sun kashe Malam Lawal, sun kuma yi awon gaba da dukiyar mutane. Kodayake jami’an tsaro sun kai ]aukin gaggawa, inda suka yi ta musayar wuta da ~arayin, amma dai duk da haka sun arce da dabbobin da suka kwaso. Haka ma a Salihawa da ke kusa da garin Bugaje, ~arayi sun kashe mutum uku. A Doga ma an kashe mutum biyu. Sai Maka]a Duma, can ma sun kashe mutum ]aya. A ranar 9/5/2020 maharan sun sake mamaye }auyen Mai [oriya a karo na biyu ]auke da miyagun makamai, inda suka ri}a bi gida-gida suna kar~e duk wani abu mai amfani, kama daga dabbobi, abinci, kayan masarufi da kayan sawa, har da zannuwan gado, tare da dukan mata da kuma zargin sun yi wa wasu fya]e. Bayan sun gama aika-aikar tasu, a kan hanyarsu ta ficewa daga garin, sun }ona wasu daga cikin kayan da suka sato, musamman akwatuna da ke ]auke da kayan sawa. Daga nan suka wuce wasu }auyuka kamar su Tsaunin Goriba, Nasarawa da Kimbitsawa, inda suka yi awon gaba da dabbobi masu ]imbin yawa. Rundunar ’yan sanda ta Jihar Kasina, ta bakin Kakinta, SP Isah Gambo ya tabbatar da korar maharan, tare da ku~utar da wasu mutane da suka sace a jerin hare-haren da jami’ansa suka kai masu. A cikin wata sanarwa da ya fitar, SP Gambo, ya ce sun yi nasarar samun wasu makamai masu tarin yawa da maharan suka gudu suka bari, tare da wasu mashina a hare-hare daban-daban da suka kai masu a }auyakun [ankar da ke Batsari da [orawa, Sabon Layi, Kaguwa da Morawa a {aramar Hukumar Kurfi. Hoto: Hajiya Huraira Alh. Murnai, 60, da Hadiza Alh. Murnai, 50 da jami’an tsaro suka ceto a hannun ~arayin shanu …Za mu zare hannunmu a ya}i da Korona a Kano Shugaban }ungiyar shugabannin {ananan Hukumomi na Jihar Kano, Hon. Lamin Sani, ya yi barazanar za su zare hannunsu a ya}in da ake yi da cutar Korona, muddin ba a daina zargin suna karkatar da tallafin da ake bayarwa ba. Hon. Sani ya bayyana haka ne ranar Litinin a taron da ya yi da manema labarai, inda ya ce za su zare hannunsu su bar Dagatai da masu Unguwanni su jagoranci abin, saboda zargin da ake masu na suna bai wa ’yan siyasa domin su huta da irin }orafin da ake masu. Ya nuna rashin jin da]insa da Hukumar da ke ya}i da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta yi wa Shugaban {aramar Hukumar Kumbotso Hon. Panshekara, bisa zargin da ake yi masa da karkatar da kayayyakin agajin da aka tanada don tallafa wa jama’a. Hon. Lamin Sani ya bayyana cewa Ciyamomi da Kansiloli ba za su }ara tsoma baki a cikin harkar raba tallafin da ya shafi Covid-19 a Jihar Kano ba, in dai ba wani mataki aka ]auka na wanke sunansu ba. Ya kashe ma}wabcinsa saboda ya hana shi kallon fim Wani mutum da ke zaune a layin Taiwo, Mafoluku, a yankin Oshodi, Lagos, ya gamu da ajalinsa bayan ya kori wasu ma}wabtansa da suka shiga gidansa domin su kalli fim a yayin da ake cikin kulle saboda tsoron ya]uwar cutar Koronabairus. Mutumin mai suna Taiwo Eluyemi, ya gamu ajalinsa ne awa 24 bayan nan, inda Habeeb ya yi masa kwanton ~auna ya kashe shi, saboda jin haushin abin da ya yi masu. Kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito, Taiwo Eluyemi, ya yi fice a tsakanin ma}wabtansa, saboda yadda ya gyara gidansa, ya zuba kayan kallo iri-iri, kuma ake samun abin lasawa, abin da yake }ara jan hankalin mutane suke taruwa a gidansa kusan kowane lokaci. Sai dai saboda ~ullar cutar Koronabairus sai ya canza taku. Habeeb, wanda shi ma yake da zama a Laiyun Taiwo, sun je gidan Eluyemi ne tare da abokansa kamar yadda suka saba ranar Laraba domin su kalli wani fim, sai dai bai bar su sun shiga ba, saboda dokar nisantar juna da aka sanya a Jihar da nufin da}ile ya]uwar cutar Korona. Matakin da ya ]auka ya fusata Habeeb, inda ya lashi takobin koya masa darasi, abin da ya jawo sanadiyyar kashe shi da ya yi. Wani mazaunin unguwar, Tope Akande, ya shaida wa majiyar tamu cewa, sune suka shiga tsakanin Habeen da Eluyemi sakamakon kai ruwa rana da suka fara yi bayan ya hana su shiga gidan nasa kallon fim ]in. “Mun ]auka kowa ya ha}ura bayan mun raba su, ashe da sauran rina a kaba”, in ji shi. Ya }ara da cewa Taiwo Eluyemi ya gamu ajalinsa ne a lokacin da yake dawowa daga coci tare da ]ansa, Habeeb ya yi masa kwanton ~auna ya sare shi da adda a baya da kuma hannunsa, abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Ya ce; “Rashin jituwar ta shiga tsakanin Eluyemi da Habeen ne ranar Talata. Habeeb da abokansa sun zo gidan mutumin don su kalli fim, amma sai ya nuna rashin amincewarsa saboda tsarin nisantar juna da aka ~ullo da shi don da}ile ya]uwar cutar Koronabairus. “Ya nemi su bar kallon, abin da ya haifar ta}addama a tsakanin su, amma daga baya an daidaita sun fahimci juna. Taiwo Eluyemi ya tafi ya ]auko ]ansa a coci washegari, ashe bai sani ba, Habeeb ya ]ana masa tarko yana jiran sa. Sai ya fito daga inda ya ~oya auka masa, ya sara masa adda a bayansa, ya sare shi kuma a hannunsa na haggu. Ya zubar da jini sosai. Nan take ya rasu. Tuni dai an kama wanda ake zargi an mi}a shi ofishin ’yan sanda na Makinde.” Majiyarmu ta tabbatar da cewa dama an ta~a samun rashin jituwa a tsakanin Habeeb da Eluyemi a baya, sai dai a wannan ranar Larabar ne tura ta kai bango. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike. “Wanda ake zargi yana tsare da hannunmu, tare da wasu abokansa biyu da suke wajen lokacin da rashin jituwar ta auku. Muna ci gaba da bincike don gano abin da ya haddasa kisan.” An kori ’yan sandan da suka ba hammata iska a bainar jama’a Rundunar ’yan sanda ta Jihar Edo ta tabbatar da korar biyu daga cikin jami’anta, saboda ‘abin kunyar’ da suka aikata na bai wa hammata isa a tsakanin su a bainar jama’a. Wani bidiyo da ya ri}a yawo a dandalin sada zumunta na zamani, ya nuna yadda Kofur Ozimende Aidonojie da Kwastabal Salubi Stephen suka daku da juna a titi jama’a na kallo suna yi masu ihu. A faifen bidiyon an ga yadda ’yan sanda suka gurji bakin juna a }asa, yayin da jama’a da suka yi cincirdo a wajen suka yi ta }o}arin raba su, amma abin ya ci tura. A cikin bidiyon an ji wata murya, wacce ake tsammanin ta wanda ya ]auke shi ne tana cewa; “Ku kalli jami’an ’yan sandan Nijeriya suna bai wa hannata isa. Wannan abin kunya ne”. Duk da yake ba a san dalilin da ya haddasa dakuwar da ’yan sandan suka yi da juna ba, amma dai rundunar ’yan sanda a shafinta na Twitter @PoliceNG a ranar Talata ta yi al}awarin gudanar da bincike don gano dalilin wannan ‘abin kunyar’ da ya sa mai dokar barci ya ~uge da gyangya]i. Rundunar ta ruwaito cewa ’yan sanda biyu Ozimende Aidonojie (F/NO 41112) Salubi Stephen (F/NO 516384) da aka gane a cikin bidiyon suna fa]a da juna, an kama su an tsare a hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Jihar Edo, kuma za a gudanar da bincike don ]aukar matakan da suka dace a kansu. A ranar Juma’a kuma sai rundunar ta sanar da korar ’yan sandan daga aiki saboda ‘abin kunyar’ da suka aikata. “Kofur Ozimende Aidonojie and PC Salubi Stephen da aka ]auka a bidiyo suna fa]a da juna a kunyace a Jihar Edo, an tuhume su, kuma sun amince da laifin da suka aikata. An kore su daga aikin ]an sanda,” in ji sanarwar. A wani labarin kuma, wani ]an sanda ya harbe wata abokiyar aikinsa Lovender Elekwachi da ke aiki a ofishinsu da ke Eneka a Fatakwal hedikwatar Jihar Rivers har lahira, kamar yadda mai magana da yawun rundunar, Nnamdi Omoni ya tabbata. Kamar yadda sanarwar ta nuna, Bitrus Osaiah ne da ke aikin a rundunar tar-ta-kwana ta Jihar Rivers ne ya harbe ta a lokacin da take gudanar da aikinta na ba da hannu a shataletalen Eneka. Rundunar ba ta ba da }arin harske ba a kan dalilin kisan. Kwamishinan ’yan sanda na Jihar, Joseph Mukan ya ba da umarnin a gudanar da bincike don gano dalilin kisan. Ya}ar Koronabairus da }aruwar magungunan bogi Daga www.bbchausa.com A fa]in duniya, mutane na siyen magunguna suna jibgewa. Amma, yayin da manyan }asashen da ke samar da magunguna a duniya - China da Indiya- suka dakatar da duk wasu ayyuka a cikin su, bu}atar magungunan a yanzu ta fi yawan yadda ake samar da shi, kuma siyar da magungunan bogi na }aruwa. A makon da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ayyana Koronabairus a matsayin annobar duniya, Operation Pangea, wani ~angare na jami’an tsaro na }asa da }asa da ke ya}i da laifukan siyarwa da samar da magunguna, ya kama mutane 121 a }asashe 90 a cikin kwanaki bakwai. Sanadiyyar haka, an }wace miyagun }wayoyi da ku]insu ya kai sama da Dala miliyan 14. Daga Malaysia zuwa Mozambique, ’yan sanda sun }wace dubban takunkuman fuska na bogi da magungunan bogi, da yawa daga cikin su kuma na cewa suna maganin Koronabairus. “Saye da sayar da magunguna ba a bisa }a’ida ba a wannan yanayi na annoba na nuna rashin ganin kimar rayuwar ]an’adam,” in ji Sakatare Janar na jami’an tsaro na }asa da }asa, Jurgen Stock. A cewar WHO, kasuwar magungunan bogi, wadda ta }unshi magungunan da ka iya zama gur~atattu ko kuma wa]anda suke ]auke da sinadaren da ba su dace ba ko sinadaren da suka lalace, ta kai Dala biliyan 30 a }asashe masu }aranci da matsakaicin tattalin arzi}i. “Idan aka sha magungunan bogi, ba lallai su magance cutar da ake so a kawar ba”, in ji Pernette Bourdillion Esteve, jami’ar WHO da ke aiki da magungunan bogi. Haka kuma, suna iya janyo illa saboda akwai yiwuwar suna ]auke da wata guba”, in ji shi. YADDA AKE SA MAGUNGUNAN A KASUWA Jerin matakan samar da magungunan suna da yawa kama daga masu sarrafawa a wurare kamar China da India, zuwa inda ake sa shi a kwalaye ko kwalabe a Turai da Amurka ta Kudu ko Asiya, zuwa ’yan kasuwa da ke aika magungunan zuwa kowace }asa ta duniya. “Ana iya cewa babu abin da ya kai magunguna ha]a kan duniya”, in ji Esteve. Sai dai yayin da duniyar ta tsaya cik, jerin matakan samar da magunguna sun fara watsewa. Kamfanonin samar da magunguna da yawa a India sun shaida wa BBC cewa yanzu suna yin kashi 50-60 cikin 100 ne kawai na ayyukansu. Yayin da kamfanonin India ke samar da kashi 20 cikin 100 na duk magungunan a nahiyar Afrika, lamarin zai matu}ar shafar }asashen Afrika. Ephraim Phiri, wani }wararre kan harha]a magunguna a Lusaka, Zambia ya ce ya fara ganin haka. “'Magunguna sun fara }arewa, kuma ba ma iya samun wa]anda za su maye gurbinsu. Ba yadda za mu yi. Da matu}ar wahala samun magunguna, musamman magunguna masu muhimmanci kamar magungunan maleriya.” Masu samarwa da manyan ’yan kasuwa na fama saboda abubuwan da ake bu}ata wajen samar da magungunan sun yi tsada yanzu, wasu kamfanonin ma ba su da ku]in siyen kayan. Wani mai samar da magunguna a Pakistan ya ce, a baya yana siyen kayan ha]a magungunan wani maganin maleriya mai suna Hydroxychloroquine kan kusan Dala 100 duk kilo. Amma yanzu, ya ce ku]in kayan ya kai Dala 1150 kan kowane kilo. Yayin da yawan }asashen da ke dakatar da ayyuka cik ke }aruwa, ba raguwar samar da magungunan ce kawai matsala ba, bu}atar magungunan za ta }aru, yayin da mutane a fa]in duniya ke ta rububin siyen magungunan yau da kullum suna jibgewa. Wannan yanayin ne na ragi a samar da magungunan da kuma }aruwar bu}atarsu, WHO ta yi garga]in kan }aruwar samarwa da siyar da magungunan bogi. “Idan samarwar ta gaza cimma yawan bu}atar”, in ji Esteve; “Tana iya haifar da wani yanayi inda magungunan bogi za su yi tasiri wajen cimma wannan bu}ata.” Da muka yi magana da masu sarrafa magunguna da kamfanonin da ke samar da magunguna a fa]in duniya, samar da magungunan maleriya a fa]in duniya na fuskantar barazana yanzu. Tun da Shugaba Trump ya fara magana kan yiwuwar Chloroquine da Hydroxychloroquine na maganin Koronabairus a tarukan manema labarai a fadar White House, an samu }aruwar bu}atar magungunan a fa]in duniya, wanda aka saba sha don magance zazza~in maleriya. WHO ta sha ambaton cewa babu wata takamaimiyar shaida da ke nuna cewa Chloroquine ko Hydroxychloroquine na iya kawar da }wayar cutar da ke janyo Covid-19. Sai dai a wani taro na kwanan nan, a lokacin da yake maganar wa]annan magungunan na maleriya, Shugaba Trump ya ce; “Me zai hana ba za a gwada ba? A gwada.” Yayin da bu}atar magungunan ke }aruwa, BBC ta gano cewa akwai Chloroquine na bogi sosai a kasuwa a Jamhuriyar Demokura]iyyar Congo da Kamaru. An saba siyar da robarsa guda mai ]auke }wayoyi 1000 kusan Dala 40, amma a shagunan siyar da magunguna a Jamhuriyar Demokra]iiyar Congo an gano suna siyar da Chloroquine har Dala 250. An samar da maganin da ake siyarwar ne a Belgium, a wani kamfani mai suna Browb and Burk Pharmaceutical Limited. Amma da muka nemi jin ta bakin kamfanin, wanda aka yi wa rajista a Birtaniya, sai suka ce ba su da “hannu a samar da maganin. Ba mu muke samar da wannan maganin ba, na bogi ne.” Yayin da annobar Koronabairus ke ci gaba, Farfesa Paul Newton, wani }wararre a ~angaren magungunan bogi a Jami’ar Oxford, ya yi garga]in cewa siyar da magungunan bogi zai ci gaba har sai gwamnatoci sun ha]a kai don ya}i da shi. “Akwai ha]arin aukawa wata annobar, ta magungunan bogi idan har ba mu tabbatar da cewa mun samar da wani tsari na ya}i da shi ba a fa]in duniya. Idan ba haka ba kuwa za a yi asarar amfanin ilimin kiwon lafiya na zamani.”