AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Miliyoyin Iraniyawa sun fito gangamin cika shekaru 40 Da nasarar Juyin-Juya-Halin Musulunci a kasar

Daga Ammar Muhammad Rajab


gwamna

A ranar 22 ga watan Bahman shekara ta 1397 H.SH, wanda ya yi daidai da 11 ga Fabrairun 2019 JMI take cika shekaru 40 cur na nasarar juyin-juya-halin Musulunci karkashin jagorancin Imam Khomaini (K).

Kamar yadda aka saba, a kowace shekara miloyoyin mutanen kasar ne suka fito gangami da jerin gwano na cika shekaru 40 da wannan nasarar a duk fadin kasar.

A Birnin Tehran, Shugaban kasa Hujjatul Islam wal muslimin Dk. Hasan Ruhani ne, ya rufe gangamin da miliyoyin mutane suka yi a dandanlin Azdi da ke tsakiyar birnin Tehran da jawabansa masu muhimmanci.

Da farko Shugaban ya bayyana cewa, kasar Iran ta rasa yankunanta a cikin daruruwan shekarun da suka gabata a hannun Sarakuna masu rauni a gaban manya-manyan kasashen duniya na zamaninsu. Amma bayan nasarar Juyin-juya-halin Musulunci, kasar ta sami ci gaba a dukkanin bangarorin rayuwa da kuma matsayi a duniya da kuma yankin Gabas ta tsakiya, tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Shugaban Ruhani ya tabbatar da cewa, ba don juyin-juya-halin Musulunci a Iran ya kasance na addinin Musulunci ne ba, ba don juyin-juya-halin Musulunci ya kasance na dogaro da Allah Madaukakin Sarki ba, ba don juyin-juya-halin Musulunci ya kasance na bin shari'ar Musulunci da kuma shuwagabanni masu tsari daga iyalan gidan Manzaon Allah (s) ba, da kuwa juyin ba zai sami nasarar da ya samu ya zuwa yanzu ba.

Da juyin da aka yi na ’yan kasanci ne, da kuwa mutanen Iran ba za su iya jure wa takurawar manya-manyan kasashen duniya wadanda a duk tsawon tarihin kasar suna jujjuya kasar ba.

A wani bangaren na jawabinsa, Shugaba Ruhani ya bayyana muhimmacin kasancewar tsarin shugabancin a kasar Iran ya kasance na jumhuriya Islamiyya, don a kowane shekara biyu mutane suna zaben shuwagabanninsu a akwatunan zabe, shuwagabanni kama daga Jagoran juyin-juya-halin Musulucin har zuwa ga Shugaban kasa da sauran zabubbuka na Majalisun kasa da na larduna.

A bangaren makiya kuma, Shugaba Ruhani ya ce, idan an ci gaba da samun hadin kai tsakanin mutane da shuwagabannin kasar, babu abin da manya-manyan kasashen duniya za su iya yi, kuma kasar Iran za ta ci gaba da samun ci gaba da daukaka a duniya.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron