AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474


Babban Labari

An yi zanga-zangar neman a saki Deji Adeyanju daga kurkuku

Ammar Muhammad Rajab


apc

Wata gamayyar kungiyoyin kare hakkin bi’adama sun yi zanga-zangar nuna kin jinin ci gaba da tsare dan rajin kare hakkin bi’adaman nan, Yarima Deji Adeyanju a kurkukun Kano bisa umurnin gwamnati.

Masu zanga-zangar sun ce, Adeyanju ya zuwa lokacin zanga-zangar ya shafe kwanaki 58 ke nan a tsare bisa zargin wani laifi da aka wanke shi tare da sallamar sa a babbar kotun jihar Kano a shekarar 2009.

Yayin da suke yin tir da abin da suka bayyana da rashin adalci ga abokin aikinsu, masu rajin kare hakkin dan Adam din, sun daddaga kwalaye suna kiran a sake shi nan take.

Masu zanga-zangar sun hada da Ariyo-Dare Atoye na ‘Coalition in defence of Nigerian Democracy and Constitution’ da Raphel Adebayo na ‘Free Nigeria Movement’ da Mose Paul na ‘MADConnect’ da Isiah Umude na ‘Proper Africa Initiative.’

Gamayyar masu zanga-zangar sun nuna damuwarsu kan rayuwar Adeyanju, suna masu ankarar da cewa, Mahaifiyarsa dattijuwa ma ta damu da halin lafiya da tsaron danta.

Atoye ya ce, Adeyanju, wanda shi ne Shugaban Concerned Nigerians, ba a karya kwarin gwiwarsa ba, duk da wahalhalun da yake fuskanta, yana nan da himmarsa, bai mika wuya ga zalunci ba.

Ya ce, “Yau Lahadi ita ce kwana ta 58 tun lokacin da dan’uwanmu, abokin aikinmu, Deji Adeyanju, yake tsare a wani mugun wuri bisa umurnin gwamnatin Buhari a jihar Kano.

“Duk da cewa a yanzu yana tsare a cikin wani mummunan yanayi wanda ba wani dan Adam da zai so ya kasance a cikinsa, yana so ma’abota fadar Aso Rock su sani cewa, ba su karya masa kwarin gwiwarsa ba, yana nan tsaye a jajirce.”

A wani labarin, a ranar Talatar da ta gabata, an gabatar da Deji a kotun jihar Kano, amma aka dage zuwa Laraba 13/02/2019.

To, a ranar Larabar, Mai shari’a Rabi’u A. Sadik ya saurari Lauoyin masu kara da masu kare wanda ake kara kan dacewar ba da belin Deji, inda bayan doguwar muhawara, sai Alkalin ya aje ranar 18 ga Fabrairu, 2019 don ya yi hukunci a kan neman belin wanda ake zargi.

Kafin nan za a ci gaba da tsare Deji Adeyanju a kurkuku.