AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Harkar Musulunci ga Jami’an Tsaro: Kar ku yi amfani da sunanmu ku ta da hankali

In ji Imam Awwal As-Sudani


Harkar Musulunci a Nijeriya ta samu wasu sahihan rahotannin da suka nuna cewa, an ga wasu mutane da ba a san su ba dauke da muggan makamai a ranar Alhamis, 07/02/2019 a wasu sassan Zariya, jihar Kaduna, musamman a yankin Sabon gari.

Ya zama tilas cikin gaggawa mu faɗakar da jama'a sakamakon ganin takardun sirri da Hukumar tsaron kasa na farin kaya, DSS da kuma fadar Shugaban kasa suka fitar na zargin ƙarya cewa Harkar Musulunci na shirin kawo tashin hankali kafin babban zabe da ke tafe a ’yan makonnin nan.

Muna so mu sake maimaita matsayinmu da aka sani cewa, Harkar Musuluncin nan tana kyamar tashin hankali ta kowane irin siga aka zo da shi. Don haka muna so mu nisanta kanmu daga duk wani makircin kawo rikice-rikice, wanda muka yi imanin jami'an tsaro sun nace sai sun tayar, ta hanyar aiwatar da su da sunanmu.

Muna so mu tabbatar wa jama'a da sauran al'ummomin duniya game da dukufar da muka yi na samar da zaman lafiya a tsakanin mutane mabambantan addini, yanki da kuma kabila, kamar yadda Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky ya dora mu a kai.

Muna so mu sake amfani da wannan damar don neman 'yancin Jagoranmu Shaikh Ibraheem Yaquob Zakzaky da matarsa da daruruwan ’yan'uwanmu wadanda har yanzu suke a tsare tun watan Disamba, 2015.

Sa Hannun

Ibrahim Musa

Shugaban Dandalin Yada Labarai Na Harkar Musulinci.

Fassarar Sani Hamisu.

Skype: Ibrahim.musa42

08/02/2019