AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Sakamakon zaben Shugaban Kasa: Atiku ya garzaya kotu

Daga Aliyu Saleh da Haruna Yakunu Abdullahi Usman


Bayan INEC ta sanar da Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasa, jam’iyyar PDP ta yi fatali da sakamakon zaben da aka ba da, wanda ya nuna Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe da gagarumin rinjaye.

Mataimakin Daraktan sashen mulki na kwamitin yaKin neman zaben Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Tanimu Turaki (SAN), ya sanar da haka, kuma tuni Shugaban jam’iyyar na Kasa, Prince Uche Secondus ya sanar da Shugaban Hukumar Zabe ta kasa, Farfesa Mahmood YaKubu wannan Kuduri.

Sun ce gaskiyar magana ba su amince da sakamakon zaben Jihohin Yobe, Zamfara, Nasarawa, Sakkwato da Barno ba, tare da ba da misalin cewa waDanda aka tantance a Jihar Yobe domin zabe su dubu 601,056 ne, amma waDanda suka jefa Kur’a su dubu 775, 449, wanda ya nuna ke nan akwai maguDi a cewar sa.

A Jihar Zamfara gaba Daya ba a kai takardun rubuta sakamakon zabe a dukkanin mazabun Jihar ba, kuma an kama wani a karamar Hukumar Shinkafi yana dangwala wa APC Kuri’u. Ban da wannan ma, an ba da sakamakon Jihar Zamfara yadda Hukumar Zabe da jam’iyyar APC ke buKata ne, kuma hakan aka yi a Jihar Barno.

A Jihar Nasarawa kuwa jam’iyyar PDP ta yi kiran da a gaggauta dawo mata da nasarar da ta samu na Kuri’u dubu 157 da Hukumar Zabe ta soke babu gaira babu dalili, da kuma wasu Kuri’u dubu 79 da aka hana jam’iyyar a Jihar Kogi, haka ma da wasu Kuri’un dubu 27 a birnin Abuja, wanda Hukumar Zabe ba ta saka su a cikin sakamakon jam’iyyar ba.

Jam’iyyar PDP ba ta tsaya nan ba, ta ce an kuma yi mata Kwacen Kuri’u dubu 30 a Jihar Filato, sannan jam’iyyar ta yi kiran a sake sabbin zabuka a Jihohin Borno, Yobe da Zamfara, sannan a dawo masu da nasarar da suka samu a birnin Abuja, Kogi da Nasarawa.

Banda wannan ma jam’iyyar ta yi kiran a sakar mata mutanen ta da aka kama da suka haDa da Buba Galidama da Emeka Okafor.

A wani batun ma Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce, bai amince da sakamakon zaben da aka yi wa Muhammadu Buhari ba.

Atiku ya ce, abin kunya ne 'Mai gaskiya' ya tafka, don haka zai Kalubalanci zaben a kotu, kuma haka ya zama wajibi domin ya ceto dimukraDiyyar Nijeria ta ci gaba da Dorewa.

Atiku ya ce a Karni uku da ya yi yana siyasa, bai taba ganin yadda dimokraDiyyar Nijeriya ta ci baya kamar yadda aka gudanar da zabe a ranar Asabar ba.

Ya Kara da cewar shi Dan siyasa ne, kuma akwai hanyoyi na siyasa da ya kamata a bayyana wa ’yan Kasa gaskiya domin duniya na kallon mu.

Atiku ya ce, ta inda suka san an aikata abin da bai kamata ba shi ne yadda wasu Jihohin da aka yi tashin hankali, musammam waDanda aka tashi bama-bamai a lokacin zabe, sun samu Kuri'u masu rinjaye.

Ya Kara da cewa da akwai wasu Jihohin da PDP ke da rinyaye an samu hatsaniya, inda mahukunta suka sa ido ba su magance rigingimun ba, kamar Jihar Legas da Akwa Ibom da Jihar Rivers.

Jam’iyyar PDP dai sun ce suna da isassun hujjojin da suke nuna yadda aka tafka maguDi lokacin zabukan da suka gabata.

A tsakiyar daren shekaranjiya Laraba ne dai, Shugaban Hukumar Zaben, Farfesa YaKubu Muhoumd, ya bayyana Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari a matsayin wanda lashe babban zaben da aka gudanar ranar Asabar bayan ya doke abokin karawarsa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Farfesa YaKubu ya bayyana cewa Buhari ya kayar da Dan takarar jam’iyyar PDP ne da Kuri’u 15,499,353 da ya samu daga jihohi 19, yayin da Atiku ya tsira da Kuru’i 11,150,746 da ya samu daga Jihohi 17.

Yayin da magoya bayan Buhari suka kwashe tsawon daren suna gudanar da shagulgulan murnar sake lashe zaben a karo na biyu, ita kuwa jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon ne tun a lokacin da aka fara Kirgawa, tana zargin an tafka maguDi.

’Yan takara 79 ne suka fafata da juna a wannan zaben, sai dai ’yan takarar da ke gaba sune, Muhammad Buhari, 76 da Atiku Abubakar, 72, yayin da sauran suke masu rakiya.

Wasu abubuwa da suka faru a zaben nan shi ne kasa dawowar wasu ‘’yan Majalisa sama da 40, ciki har da Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki, yayin da Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara yake cikin waDanda suka dawo duk da neman karya lagonsa da aka yi a Bauchi.

Kazalika akwai rikice-rikicen da aka yi a wasu Jihohin da suka haDa da Lagos da ya jawo hasarar rayuka, kamar yadda Mataimakin Shugaban Sufeto-Janar na ’yan sanda, David Folawiyo, wanda ya sanya ido a kan yadda aka gudanar da zaben a Lagos, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Kasa, NAN.

An samu tutsun da na’urar tantance masu zabe a wasu Jihohi, kamar yadda Mataimakin Daraktan hulDa da jama’a na Hukumar zabe na Jihar Kano, Garba Lawal-Mohammed ya bayyana dalilin jinkirin da aka samu na fitar da sakamakon zaben Jihar ne saboda wasu matsaloli da aka samu a na’urar tantance masu zabe (card readers). “Muna da Cibiyar kula da yadda zaben ke gudana, amma mun samu matsalar na’ura ne,” in ji shi.

Sai dai jam’iyyar PDP a Kano, ta yi zargin da gangan aka haifar da wannan jinkirin don a yi maguDi, don haka ma suka yi watsi da sakamakon.

Wani abu kuma shi ne kasuwar hada-hadar hannun jari ta Kasa ta yi asarar Naira miliyan dubu 150 da Doriya jim kaDan da samun labarin sake zaben Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari a karo na biyu.

Kasuwar dai ta buDe da jarin zambar Naira miliyan dubu sau dubu 14 da Doriya (14.753) wato Tiriliyan 14, amma kafin a rufe ta ta yi asarar Naira miliyan dubu 150, wanda an shekara ba a yi irin wannan asarar ba a rana guda.

Wannan nasarar da aka sanar ta Buhari ta sa magoya bayansa sun gudanar da bukukuwa a wasu garuruwa da ke faDin Kasar nan, waDanda suka jawo hasarar rayuka da kuma dukiyoyi.