AlmizanAlmizan logo
Jum'a 9 ga Shawwal, 1439 Bugu na 1346 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Shari’ar Shaikh Zakzaky: Abin da ya faru a kotu

Daga Abdullahi Usman


A jiya Alhamis babbar kotun Jihar Kaduna ta 4 da ke gudanar da Shari’ar Shaikh Ibraheem Zakzaky da MaiDakinsa da kuma wasu ’yan’uwa musulmi guda biyu ta sake Dage zamanta zuwa ranar Laraba 11/7/2018.

Tun da sanyin safiyar Alhamis Din ne jam’an tsaro Dauke da muggan makamai suka rufe dukkan hanyoyin da ke isa ga harabar kotu, komai ya tsaya cak a wajen da aka shirya gudanar da shari’ar da kuma cikin garin Kaduna.

Tun da aka shiga kotun, Magatakardar kotun ta bayyana cewa AlKalin kotun Mai Shari’a Gideon Kurada ba zai sami zuwa kotun ba saboda wani babban dalili. Don haka ta nemi Lauyoyin su Dauki wata rana ta daban don ci gaba da wannan shari’a.

Sai dai wata majiya mai tushe ta tsegunta mana cewa, AlKalin bai je kotun ba ne saboda buge shi da mai Keke Napep ya yi a shekaranjiya Laraba.

Wakilinmu da ke harabar kotun ya shaida mana cewa an sami saBanin Daukar rana tsakanin Lauyoyin gwamnatin Jihar Kaduna, KarKashin jagorancin Barista Bayero Dari da kuma na Shaikh Zakzaky, inda aka dakatar da Daukar ranar har sai da aka jira isowar Barista Femi Falana (SAN) kotun, inda suka amince da ranar 11/7/2018 don ci gaba da shari’ar.

Da yake zantawa da manema labarai bayan fitowa daga kotun, Barista Femi Falana (SAN) ya bayyana cewa yau ba a yi komai ba a kotun saboda rashin halartar AlKali. Amma ya ce ba su san dalilin rashin zuwan AlKalin ba.

Falana ya bayyana cewa a shirye suke don kare Shaikh Zakzaky da iyalinsa, kuma za su yi duk abin da ya kamata don ganin hakan ta tabbata.

Falana ya ci gaba da cewa, gwamnatin Jihar Kaduna na tuhumar Shaikh Zakzaky ne da dukkan nau'o’in laifuka, sannan kuma gwamnatin na tursasa wa Malam Din. Ya Kara da cewa za su kasance cikin shiri kafin ranar 11 ga wata da za a dawo kotun.

An dai gabatar da Shaikh Zakzaky da matarsa Malam Zeenatuddeen ne tun a tsakiyar watan jiya, inda ake tuhumar su da laifin tunzurawa, ko kuma kashe wani Soja mai suna Saje YaKubu dan Kaduna a lokacin da sojojin suka kai masa hari a gidansa da ke Gyallesu, Zariya, inda suka kashe almajiransa sama da 1,000, ciki har da ’ya’yansa uku.

Cikin wannan tuhumar akwai Wakilin ’yan’uwa na Katsina, Shaikh YaKubu Yahaya Katsina da kuma na Kano, Dakta Sanusi AbdulKadir koKi.

’Yan sanda sun buDe wuta kan masu Muzahara a Kaduna

Daga Aliyu Saleh

’Yan sanda sun buDe wuta kan masu Muzaharar neman a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky da aka gudanar shekaranjiya Laraba da kuma jiya Alhamis, inda aka jikkata mutane da dama, kuma wasu 'yan sanda suka tafi da su.

Ganau sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun yi amfani da Karfi fiye da kima, inda suka yi ruwan wuta a kan mutane ba tare da sun aikata laifin komai ba. Baya ga harbi da bindiga, sun yi amfani da makamai na gargarjiya irin su gorori da adduna da takkuba kan masu Muzaharar.

Wakilinmu ya ga yadda jami’an tsaron suka sari wani Dan’uwa suka shigar da shi mota, yayin da ya hangi wani kwance an yi masa jina-jina, yayin da suka jefa wani cikin motarsu kansa na waje yana lilo, suna tattaka cikinsa da takalmansu. Wasu kuma da raunin harbin bindiga a jikinsu, kuma sun bi gari suna ta ihu da kuma tsorata mutane.

Kasuwa da shaganuna sun kasance a rufe saboda yadda jami’an tsaro suka yi ta yin harbin kan mai uwa-da-wabi a ciki. Jama’a sun tsorota sosai da irin matakin ba sani, ba sabo da suka ga jami’an tsaron sun Dauka.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai, Malam Aliyu Tirzimi, ya yi watsi da zarge-zargen da jami’an tsaro suka yi na cewa ’yan’uwa sun kai masu hare-hare ne a lokacin da suke gudanar da Muzaharar.

Ya ce, kamar yadda suka saba yin tarukansu cikin lumana, wannan haka suka yi shi. Muna cikin gudanar da Muzahararmu domin kira ga gwamnati ta bi umurnin kotu, sai jami’an tsaro suka far mana da harbi, inda suka raunta da dama, suka kuma kama wasu suka tafi da su.

“Mun fito ne domin kira ga gwamnati da kuma isar wa duniya saKon irin halin da ake ciki na ci gaba da tsare Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky duk da hukuncin kotun Tarayyar, wanda gwamnatin ke ci gaba da kunnen uwar shegu da shi. “Lallai ba arangama aka yi ba, an auka mana ne. Kuma kowa ya san cewa mun fito ba mu da ko sanda a hannunmu. Sannan kowa ya shaida mu aka jikkata mana mutane, aka kuma kama wasu. Kuma waDanda aka jikkata hotunansu na nan da iri raunin da aka yi masu.”

“Rundunar ’yan sandan sun yi taron manema labarai, sun kuma yaDa cewa ana zargin mu da yin arangama da su, har an jikkata masu mutane biyu.

“Lallai ba mu san wannan ba, kuma muna nisanta kanmu da wannan zargin. Abin da muka sani, kuma duniya ta shaida shi ne, an auka mana, an kuma jikkata mana mutane da harsasai masu rai, an kuma kama mana wasu daga cikin ’yan’uwanmu.

“Har kullum muna kan bin matakai na shari’a da lumana wajen ci gaba da neman haKKoKinmu da ci gaba da kira da muke yi na gwamnati ta saki Jagoranmu da iyalinsa da dukkan ’yan’uwanmu da ke tsare”, in ji shi.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta Jihar Kaduna, ASP Aliyu Mukhtar, ya tabbatar da kama ’yan’uwa biyar shekarajiya Laraba, yayin da suka kai, inda ya yi zargin an jikkata masu mutane biyu.

Ba mu samu labarin mutane nawa suka kama jiya ba, har ya zuwa lokacin da muka kammala wannan rahoton, sai dai mun samu tabbacin shahadar mutane biyu; Idris Alhasan Unguwar Rimi da kuma Imran Kabir.

Tun daga ranar 8 ga Janairu, 2018 jami’an tsaro sun harbe mutane shida, an tsare da Daruruwa da suka fito Muzaharar neman a saki Shaikh Zakzaky da ake a Abuja da Kaduna. Ana tsare da Shaikh Zakzaky ne tun bayan harin da Sojoji suka kai masa a gida, inda suka harbe shi da maiDakinsa, tare da kashe almajiransa sama da 1,000 da ’ya’yansa uku.

Idan ba a manta ba a ranar 15/5/2018 da ta gabata ne, gwamnatin Jihar Kaduna ta kai Shaikh Ibraheem Zakzaky, maiDakinsa da wasu mutane biyu kotu bisa tuhumar aikatawa, ko ingizawa a aikata kisan kai. A shekarar 2015 ne Hukumar kare haKKin bil’adama ta Musulunci (IHRC) da ke London ta shigar da Kara kan kisan kiyashin da aka yi a Zariya a gaban kotun duniya da ke hukunta manyan laififfuka da ke Hague.

A watan Maris na shekarar 2016, kotun ta buDe aikin bincike kan kan kisan kiyashin da aka yi a watan Disamba, 2015 a Zariya.

A wani labarin kuma a Abuja ma a daren shekaranjiya Laraba da kuma wayewar garin Alhamis, an gudanar da Muzaharori a Asokoro da kuma a gaban ofishin Hukumar kare haKKin bil’adama, inda aka miKa takardar koke game da irin cin zalin Din da jami’an tsaro ke yi wa ’yan’uwa da ke gudanar da Muzaharar lumana.

Kotu ta kori Kara kan ’yan’uwan da aka kama a Abuja

Daga Shehu Al-ja’afaree Kaduna

A shekaranjiya Laraba aka kori Karar da jami’an tsaro suka shigar da ’yan’uwa 19 da suka kama a wajen Muzaharar ‘Free Zakzaky’ da ake yi a Abuja.

AlKalin kotun majistire ta 8 da ke Wuse Zone 6, Abuja ya kori Karar da aka shigar masa ne saboda rashin Kwararan shaidun da zai dogara da su wajen yanke hukunci. Ana jin hakan ne ma ya hana Dan sanda mai gabatar da Kara bayyana a gaban kotun.

Wannan Karar da aka kora dai ita ce ta bakwai cikin Kararraki tara da aka shigar da ’yan’uwa a kotuna daban-daban da ke Abuja.

Ko a kwanakin baya ma wata kotun Majistare da ke Lugbe, Abuja ta kori Karar da ’yan sanda suka shigar a gabanta na wasu yara 10 daga cikin ’yan’uwa 112 da aka kama yayin Muzaharar ‘Free Zakzaky’ ranar Litinin 16/04/2018 bayan sun kwashe kwanaki 40 a tsare.

Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Bello SadiK Abubakar ne ya shigar da Karar ’yan’uwan yana tuhumar su da aikata laifuka guda takwas. Sai dai duk musanta aikatawa. A zaman da kotun ta yi ranar Juma’ar makon jiya, wanda shi ne zama na uku na shari’ar, AlKalin kotun ya yi watsi da Karar saboda rashin kawo Kwararan shaidu da masu Karar suka yi, sannan sai ya dogara da kundin tsarin mulki.

AlKalin ya karanto wani sashi na aikata laifuffuka na ‘penal code’, wanda ya haramta gurfanar da yaran da ba su kai shekara 18 ba, inda ya Kara da cewa, Majalisar kasa ta rubuta takarda zuwa ga Shugaban Gidajen Yari na Kasa a kan tsare yaran da ba su kai shekara 18 ba.

Ya ce bisa da dogaro da dokar da ta haramta tuhuma, ko tsare yaran da ba su kai shekaru 18 ba, ya kori Karar, tare da wanke su. Su kuma sauran manyan ya ce, ba zai Dauki dogon lokaci ba don ci gaba da shara’ar tasu. Yaran da ka saki sun haDa da Isah Muhammad, 16; Mubarak Yusuf, 16; Mahdi Abubakar, 15; Aliyu Muhammad, 17; Adamu Aliyu, 15; Auwal Mustafa Imam, 16; Al-amin Muhammad, 16; Muhammad Idrees, 17; Khadija Ilyasu, 15 da Fatima Muhammad, 15.

A jaya Alhamis ma ’yan’uwa 21 sun bayyana a gaban kotun majistire da ke Wuse Zone 2, inda aka saurari ci gaba da shari’ar da ake yi masu don sun halarci Muzaharar ‘Free Zakzaky’ a Abuja. AlKalin kotun ya Dage shari’ar zuwa ranar 7/8/2018.

A wani labarin kuma, a shekaranjiya Laraba ne aka kai ’yan’uwan da aka kama a harin da Sojoji suka kai Zariya shekaru biyu da suka gabata gaban babbar kotu ta 6 da ke NDA janction, inda AlKalin kotun ya tsayar da ranar 31/7/2018 domin yanke hukunci.

Su dai waDannan ’yan’uwa su 160, inda a kotu ta 6 akwai 87, ta 11 kuma akwai 73, an kai su gaban AlKali ne a cikin motar ’yan sanda da ake kira shiga-ba-biya, fuskokinsu cikin haske da al’amun rashin damuwa.

TAKARDAR MANEMA LABARAI

Tuhumar Shaikh Zakzaky rashin adalci ne

Shari’ar da ke jan hankali wacce ake yin ta bisa wata mummunar manufa da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar a kan Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky da wasu bayin Allah uku, an ci gaba da ta a babbar kotun Kaduna jiya Alhamis 21 ga Yuni, 2018.

Baya ga cewa gwamnatin jihar Kaduna ta fito da wasu Kagaggun tuhume-tuhume a kan Shaikh Zakzaky, matarsa da wasu biyu, akwai alamu da ke nuna cewa za a yi shari’ar ne a cikin sirri don a samu damar yanke wa Shehin Malamin hukuncin ba bisa adalci ba.

Don a fahimci yadda shari’ar take, dole a ambato cewa, ranar 12 ga Disamban 2015 da dare, wasu sojoji Dauke da muggan makamai bisa odar Manjo-Janar Oyebade a wancan lokacin, sun nufi gidan Shehin Malamin da mummunar aniyar kisan kai. Kuma bayan wasu kwanaki biyu suna ta harbin jama’a, sun kashe sama da mutum 1,000 da suka haDa da mata da yara Kanana, cikin su har da ragowar ’ya’yan Shaikh Zakzaky uku da Yayarsa. Gidan ma aka Kona shi, daga baya aka rusa shi gaba Daya. Shaikh Zakzaky da matarsa aka hahharbe su a wurare da dama, aka bar su cikin jini, daga baya aka ja su a kan gawawwakin ’ya’yansu, aka je aka tsare su a Boye.

Ba ma sai an ambata cewa Shaikh Zakzaky da maiDakinsa sun samu gagarumar nasara a babbar kotun Tarayya, wacce ta tabbatar da ’yancinsu na ’yan’adamtaka ba, amma gwamnatin Tarayya saboda raina kotu ta yi watsi da umurnin da aka ba ta na sakin su tun watanni 18 baya.

Kwanan nan ne kuma gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa ita ta ba da kwangilar wannan kisan kiyashi mai ban tsoro, wanda yanzu haka yake matakin bincike a kotun duniya da take birnin Hague. A bisa waDannan al’amura ne gwamnatin jihar Kaduna ta fito da wasu tuhume-tuhume na wauta a kan Shaikh Zakzaky, matarsa da wasu bayin Allah biyu.

Muna Allah wadai da wannan shari’ar saboda yadda aka Dora ta a kan zalunci. Sannan kuma muna matuKar adawa da duk wani shiri na yin ta a asirce ta hanyar fakewa da ma kowane irin dalili ne.

Wannan shari’a ta ja hankalin masu sa ido na cikin gida da wajen Kasar nan. Don haka gudanar da shari’ar a bisa ganin idon duniya shi ne mafi Karancin abin da ake buKata. Dole a Kyale ’yan jarida na cikin gida da waje da suke da sha’awa su halarci zaman kotun. Haka nan kuma Kungiyoyin kare haKKin Dan’adam na cikin gida da waje da suke so su sa ido kan shari’ar, dole a ba su dama, haka ma duk wani mutum da yake da sha’awar bin kadin shari’ar.

Duk wani abu saBanin wannan, to yi wa adalci karan tsaye ne, wanda aka ruwaito Shugaba Muhammadu Buhari kwanan nan a kafafen yaDa labarai yana cewa, ba za su sake ‘amincewa’ da shi ba. Kamar yadda ake yawan faDi, shi fa adalci, ba kawai dole a yi shi ba ne, dole a gani a sarari cewa lallai an yi shi ne.

SA HANNU:

IBRAHIM MUSA

SHUGABAN DANDALIN YAdA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA

Skype: Ibrahim.musa42

20/06/18