AlmizanAlmizan logo
Jum'a 9 ga Jimada Ula, 1439 Bugu na 1325 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Yadda aka yi jana’izar Shaikh Kasimu Umar Sakkwato

Daga Shehu Mai Burodi da Husaini Baba da Bilal Nasir Umar


A shekaranjiya Laraba ne dubun-dubatar jama’a daga ciki da wajen kasar nan suka halarci jana’izar Shaikh Kasimu Umar Sanda Rinin Tawaye, wanda ya yi shahada ranar Litinin din nan da ta gabata a Asibiti, sakamakon harbin da jami’an tsaro suka yi masa ranar Talata 9/01/2018 a Abuja.

Sallar jana’izar, wacce aka yi ta a filin babban masallacin Juma’a na Abubakar na III da ke cikin garin Sakkwato, dubban jama’a maza da mata ne suka raka shi makwancinsa cike da jimami.

A lokacin da ake tafiya da gawar, wacce Harisawa suke dauke da ita, dubban jama’a sun tako daga inda aka yi masa Sallah da ke da nisan kilomita biyu, suna tafe suna Hailala da salatin Annabi. Jama’a sun yi dafifi a gefen titi cike da alhini suna kallon yadda jama’a ke yi wa Shaikh Kasimu Umar rakiya zuwa makwancinsa da ke Mabera, yayin da iyalai da ’yan uwansa na jini suka yi cincirindo a wajen.

Da muke zantawa da shi bayan kammala jana’izar, Shaikh Saleh Lazare ya bayyana rashin Shaikh Kasimu Umar a matsayin babban rashi, inda ya bayyana cewa jarabawar da Allah yake mana yanzu ta fi karfin imaninmu. “Don haka muke rokon Allah ya tausaya mana.”

Ya ci gaba da cewa jajircewar Shaikh Kasimu Umar a wannan Harka, ta sa wannan babban rabon ya same shi. “Don haka wannan kule ne ga guk wanda ke cikin Harkar nan ya yi iya kokarinsa wajen ganin Jagoranmu ya fito, ta addu’a da kuma ta jiki. Duk sad da ake neman ’yan’uwa wajen ba da jikinsu, to su zamo gaba-gaba kamar yadda Malam Kasimu Umar ya zamo. Muna fatan jinin Malam Kasimu Umar da ya zuba ya zamo sanadiyyar fitar Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky,”, in ji shi.

Shi ma Shaikh Yakubu Yahya, ya bayyana rashin Shaikh Kasimu Umar, wani babban gibi ne a Harkar nan. “Dama muna da gibi a Kaduna, Patiskum, Kano da Zariya, ba a kai ga cike su ba, yanzu kuma ga wannan babban bangon ya fadi.

“Idan muka kalli muhimmancin Shaikh Kasimu Umar a cikin mu ba ya misaltuwa, musamman idan muka dubi inda yake da kuma irin gudummawar da yake bayarwa a Harkar nan. Ko ba komai yana cikin wadanda suka samu tarbiyya daga Malam ta shekaru. Lallai wannan babbar jarabawa ce a gare mu. Ba mu san hikimar Allah ta dauke shi a daidai wannan lokacin da aka fi bukatarsa ba”, in ji shi.

Shi kuwa Shaikh Adamu Tsoho Jas, ya bayyana rashin Malam Kasimu a matsayin babban rashi, wanda kuma cike gurbinsa yana da wuya wajen sadaukarwarsa a cikin wannan Harka. “Ga shi Allah ya saka masa da mafificiyar sakayya ta shahada. Muna fatan Allah ya maida mu danshinsa. Ya kamata Malam Kasimu Umar ya zamo mana madubi abin koyi.”

Shaikh Abdullah Zango ya bayyana cewa shahada babban rabo ne, kuma an kashe Shaikh Kasimu a kan yana cewa a saki Shaikh Zakzaky. Don haka kar azzalumai su dauka sun gama da Malam Kasimu Umar, Muzahara ‘free Zakzaky’ yanzu muka fara. Masu aukar da shahadar su sani Allah ba zai bar su ba. Wallahi sai ya daukar mana fansa.”

Shi ma Malam Sidi Mannir ya bayyana cewa; “Shahada mun saba da ita, amma wannan kam ta girgiza mu matuka. Amma nasara ce gare mu. Muna godiya ga duk wadanda suka zo jana’izar nan daga ko’ina a ciki da waje da wajen kasar nan.”

Muhammad Kasimu Umar (Gwarzo) shi ne babban da ga Shahid Kasimu Umar, ya bayyana cewa; “Allah ya sa jinin Mahaifinmu da ya zuba ya zamo sanadiyyar habakar Harka Islamiyya a Sakkwato da ma kasa baki daya.”

Ya ci gaba da cewa; “Gwamnati ta sani kashe Mahaifinmu babu abin da ya kara mana sai kara dagewa a kan wannnan Harka. Ba za mu fasa abin da muke yi ba, sai mun isko shi da yardar Allah. Irin taron jama’ar da muka gani ya nuna mana Malam yana tare da al’umma. Mun gode wa Allah da kuma duk wanda ya halarci wannnan jana’izar.

Ita kuwa Mahaifiyarsa Hajiya Hawwa’u Umar ta bayyana shahadar Shaikh Kasimu a matsayin wata daukaka a gare shi, don haka ta taya shi farin ciki saboda dacewa da abin da yake nema ya samu. “Domin a duk lokacin da ya yi Sallah, sai ya roki Allah ya datar da shi da shahada, kuma Allah ya cika masa gurinsa. Malam Kasim ya gama lafiya, kowa yana son sa,” in ji ta.

Hajiya Hawwa’u ta yaba kwarai da irin halayen kwarai na yabo da Shaikh Kasimu yake da su, inda ta ce ba ya fada da kowa. “Ko dazu wata mata ta zo tana bayani dangane da shahadar Malam Kasim, inda take cewa; ‘mu muka yi rashi, domin kuwa Malam Kasim ya sa an gyara muna matsalolin ambaliyar ruwan sama da take ta damun mu shekara da shekaru. Duk barayin da ke addabar mu, zuwan Malam Kasim Unguwar nan tamu ya magance muna su, domin kuwa a da ba mu da ikon fita mu je cikin gari, kafin mu dawo an yi mana sata, amma yanzu ko ba mu rufe gida ba, ba abin da zai samu kayanmu.”

Shaikh Kasimu Umar ya yi shahada yana da shekaru 50, ya bar ’ya’ya hudu; Muhammad, Ahmad, Hamid da Fatima.

“Allah ya rahamshe shi, ya karbi shahadarsa,” in ji wani bawan Allah da ya ji labarin shahadarsa.