AlmizanAlmizan logo
Jum'a 3 ga Rabi'ussani, 1439 Bugu na 1319 ISSN 1595-4474


Babban Labari

ABIN TAKAICI DA MAMAKI: Hijabi ya hana ta zama Lauya

Daga Wakilinmu tare da rahoton bbchausa.com


An hana wata 'yar Najeriya da ta kammala karatun lauya zama Lauya - mai iya aiki a kotu - saboda hijabin da ta saka wanda ake ganin ya saba wa dokar tufafin makarantar horar da lauyoyin kasar.

Shugaban makarantar horas da lauyoyi Isa Hayatu Chiroma ya shaida wa BBC cewa, an hana Amasa Firdaus shiga dakin taron yaye lauyoyi ne saboda ba ta sanya tufafin da ya dace ba.

Ta ki ta cire hijabinta, tana mai cewa, dole ta saka hular lauyoyi kan dan-kwalinta, in ji shafin intanet na Nigerianlawyer.com.

Rahotanni sun ce Firdaus ta bayyana matakin a matsayin wani abin da ya keta hakkinta na bil Adama.

Wata mata dai ta wallafa wani sako a shafin sa da zumunta na Instagram, inda ta yi korafin cewa, masu kula da lamurran dokar Najeriya sun yi wa wata "'yar uwa" wariya tana mai amfani da maudu'in #justiceforFirdaus.

Tuni dai 'yan Najeriya suka yi ta tafka muhawara a kotu kan hana mai saka hijabin zama lauya.

Wannan batu dai shi ne ya mamaye kafofin sada zumunta a Nigeria tun daga ranar da wannan abin ya faru.

Misali wasu ma'abota shafukan ‘twitter’ sun yi ta yada hotunan ita wannan daliba da aka hana ta zama cikakkiyar Lauya.

Wasu kuma sun yi ta yada hotunan daya daga cikin 'ya'yan Shugaban Najeriya wacce a bara ta halarci taron tabbatar da ita a matsayin Lauya.

Shi ma Shugaban Kungiyar Lauyoyin, wato A. B Mahmoud ya wallafa wani hoto na 'yarsa a shafinsa na ‘twitter’ inda a hoton ta halarci taron tabbatar da ita a matsayin Lauya a birnin New York na kasar Amurka.

Ya kara da cewa, kungiyar lauyoyi ta Najeriya za ta yi kokarin ganin an kawo karshen wannan batu na hana lauyoyi masu son sanya hijabi.