AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa: Cacar baki ko yaki?

Ammar Muhammad Rajab


apc

Babban jami'in diflomasiyya na Koriya ta Arewa ya ce jawabin da Shugaba Donald Trump ya yi a Majalisar Dinkin Duniya, ''haushin kare ne.''

Da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba, Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce, zai lalata Koriya ta Arewa gaba daya idan ta zame wa Amurka ko kawayenta barazana.

Maganganun da Ministan Harkokin Wajen Koriya Ta Arewan, Ri Yong-ho ya yi, sune kalamai na farko kan mayar da martani ga jawabin Trump.

Koriya ta Arewa ta ci gaba da shirye-shiryen makaman nukiliyarta, duk kuwa da haramcin hakan da Majalisar Dinkin Duniya ta yi mata.

Mista Ri ya fada wa manema labarai a kusa da hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya a New York cewa, ''Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi."

“Idan (Trump) yana tunanin cewa zai iya ba mu mamaki da balokokon da yake yi ne, to lallai gara ya san cewa mafarki yake yi,” in ji shi.

Da yake magana game da Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, Mista Trump ya fada wa Majalisar Dinkin Duniya cewa, ''Mai makaman roka yana son yin kunar bakin wake ne."

Lokacin da aka tambaye shi abin da yake tunani game da kiran Kim Jung-un da 'mai makaman roka,' sai Mr Ri ya ce: "Ina jin tausayin mataimakansa."

Mista Ri ya shirya ba da jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'a.

Haka kuma a ranar Alhamis, Koriya ta Kudu ta ce, za ta aika sabon taimakon jin kai ga Koriya Ta Arewa a karo na farko a kusan shekara biyu.

Ma’aikatar hadin kai a Seoul na shirin samar da Dala miliyan takwas ta hanyar shirin Majalisar Dinkin Duniya don taimakon yara da mata masu ciki da kuma da inganta kayayyakin kiwon lafiya.

Wannan mataki ya zo kwanaki bayan Majalisar Dinkin Duniya ta amince da sabbin takunkumai a kan Pyongyang, na hana shiga da fitar da man fetur da kayayyaki - wani yunkuri na sanya Koriya Ta Arewa cikin halin yunwa.

Takunkumin na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne a matsayin martani kan gwajin nukiliyar da Arewata yi a ranar 3 ga watan Satumba.

Masana sun ce Koriya ta Arewa ta yi matukar ci gaba a kera makamai masu linzami da makaman nukiliya.