AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Muzaharar Ashura: Jami’an tsaro na shirin zub da jini

Daga Saifullah M. Kabir


Bisa ga dukan alamu jami’an tsaron wasu jihohin kasar nan sun riga sun lashi takobin zubar da jinin jama’ar da suka yi niyyar fitowa don muzaharar lumana ta jajen kisan gillar da aka yi wa Imam Husain, Jikan Ma’aiki, wacce aka shirya yi a duk fadin duniya ranar Lahadin nan mai zuwa, ciki kuwa har da nan kasar Nijeriya.

Rahoton baya-bayan nan da muka samu shi ne na wata takardar sanarwa da Kwamishinan shari’a na jihar Sakkwato Sulaiman Usman ya fitar, inda yake jaddada kudurin gwamnatin jihar ta haramta duk wani jerin gwano da ’yan uwa musulmi na Harkar Musulunci a Nijeriya suka shirya yi a fadin jihar Sakkwato. Bai dai ambaci sunan muzaharar Ashura ba, amma ga dukkan alamu ita yake nufi, don kuwa ita ce muzaharar da ke tafe bayan wannan sanarwar tasa.

“Akwai wasu ayyukan ’yan Shi’a a jihar da za su iya ta da hankali. In ba a dauki mataki ba, zaman lafiyar jihar zai iya tozarta daga wannan kungiya. Don haka mun haramta duk wani taron jama’a a bainar jama’a,” sanarwar ta ce.

Kwamishinan Shari’ar ya sanar da wannan haramcin ne a taron manema labarai da ya yi bayan taron harkar tsaron jihar da wasu jagororin Hukumomin tsaro a jihar suka halarta.

“Don haka ina so in yi amfani da wannan damar don yin kira ga Harkar Musulunci a Nijeriya da ta bi wannan umurni na gwamnati,” ya ce.

Kwamishinan ya kuma yi gargadin cewa, “Duk wanda ya keta wannan doka, to ya zargi kansa, ko ta zargi kanta, kan duk abin da ya biyo baya.”

Shi ma Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Muhammad Abdulkadir ya gargadi ’yan uwa na Harkar Musulunci a kan yin duk wani abu da zai kawo hargitsi ga jama’ar jihar da suke son zaman lafiya.

Abin da ke daure wa manazarta kai don gane da wannan mataki shi ne, to ai irin wannan taron an sha yin sa a baya a birnin na Shehu, kuma a tashi lami lafiya, matukar gwamnati da zauna-gari-banzan da aka yi hayar su ba su kawo hari ba. Don haka meye na haramta irin wannan taron na lumana na jajanta kisan gillar da aka yi wa Jikan Ma’aiki (AS)?

A jihar Kaduna kuwa, tun a makon da ya gabata gwamnatin Elrufa’i ta fitar da makamanciyar wannan sanarwa ta haramta duk wani jerin gwano na jama’a. Kuma har ta tura jami’an tsaronta suka auka wa tarukan ’yan uwa na zaman jajen Ashura a biranen Zariya da Kaduna a ranar Asabar da ta gabata. Kodayake cikin ludufin Allah, ba a rasa rai ba.

Idan ba a manta ba, a bara dai a irin wannan muzaharar ce a Funtuwa, rundunar ’yan sandan jihar suka bude wuta, abin da ya jawo kisan ’yan uwa musulmi 15, tare da tsare da dama na wasu watanni.

“In dai banda neman ta da fitina, me ya kai gwamnati tsoma bakinta kan harkokin addini da har za ta ce ga wanda ta yarda a yi, ga wanda ba ta yarda a yi ba, alhali kasar dungurungum dinta ba ruwanta da addini?” a cewar wani masharhanci.