AlmizanAlmizan logo
Jum'a 27 ga Shawwal, 1438. Bugu na 1298 ISSN 1595-4474


Babban Labari

El-Rufa’i ya rusa komai a Kaduna - In ji Jiga-jigan APC


Wasu ’yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar Kaduna da suke kiran kansu APC Akida sun nuna damuwa kan yadda al’amura ke gudana a jihar.

’Yan akidar da suka hada da wasu gaggan jam’iyyar a jihar na cewa gwamnati a karkashin Elrufa’i na yin wani irin salon mulki da ya saba da manufofin jam’iyyar APC. Sai dai gwamnati ta musanta dukkan zarge-zargen.

A wani taron manema labarai da ya samu halartar wasu gaggan jam’iyyar APC Akida ta jihar Kaduna, Mista Mataimaki Tom Maiyashi, wanda shi ne Shugaban wannan bangaren a jihar ya ce, “Malam Nasiru Elrufa’i, wanda shi ne Gwamnanmu gaba daya ya jinginar da akidar canji. In banda musgunawa mutane da kuntatawa al’umma. Muna da sanin cewa kamar yadda ake masa kirari da cewa Rusau, to komai ma ya rusa! Ya rusa gidajen mutane.”

Ya kuma kara da cewa, “A takaice babu wata manufa ta wannan gwamnati, wanda yake an nemi ra’ayin mutane don a ji, a san yadda mutane suke ji kafin a aiwatar. Misali an saukar da dukkan Hakimai na jihar Kaduna da kuma Dagatai su kusan 4400. Wannan abu zai kawo hadari kwarai da gaske, domin wadannan shugabanni namu sune suke tattalin zaman lafiya a dukkan unguwanninmu da garuruwanmu da kauyukanmu. Amma an saukar da su, wai saboda babu kudin da za a biya su albashi. Dagaci din nan fa tsanani bai kai mafi karancn albashi ban a N18,000. Sannan Hakimi wanda tsanani N50,000 ba, sai a ce wai wadannan kudade su suka sa aka rusa su.”

Sannan ya ci gaba da cewa, “Nufinsa da ya gama da wadannan Hakimai da Dagatai, iyayenmu Sarakuna su zai tasar musu. To, muna masa kashedi. Kada ya ma fara. Idan ya fara za mu yake shi.”

Mataimaki Tom Maiyashi ya kara da cewa, “Kuma a karshe mun yanke kauna da shi. Daga yau ba mu yi ‘recognising’ dinsa a matsayin Gwamnanmu ba, don ya ci amanar jam’iyya, ya ci amanar al’umma. Ba za mu sake wani hulda da shi ba. Kuma duk wata manufa da ya fitar, wanda kuma mun san cewa ba zai yi abin da zai kawo salama ba, don walwalar al’ummarmu, za mu yake shi.”