AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Harkar Musulunci ba kungiyar ’yan bindiga ba ce - In ji Daraktan Kungiyar MURIC

Ammar Muhammad Rajab


apc

Farfesa Ishaq Akintola, Daraktan Kungiyar kare hakkin Musulmi, wato Muslim Rights Concern (MURIC) ya bayyana rashin jin dadin kungiyarsu kan matakin da Gwamnan jihar Kaduna, Elrufai ya dauka na bayyana Harkar Musulunci a Nijeriya (IMN) da Shaikh Ibraheem Zakzaky ke wa jagoranci a matsayin kungiyar yan bindiga.

MURIC tana Allah wadai da wannan sabon suna da aka yi wa kungiyar da aka san ba ta dauke da makamai. Wannan shela ba komai ba ne face bai wa kare mummunan suna don rataye shi. Gwamnatin Kaduna kawai tana tankware gaskiya ne, tana kashe kuda da guduma da kuma nuna danniyar masu mulki kan raunana, a takardar da Daraktan ya sa wa hannu, aka raba wa manema labarai a ranar Talatar da ta gabata.

Har ila yau Kungiyar ta ce, wannan mataki yana da hadarin gaske. Ganin cewa shelar ta fito ne ba jimawa da wata kotun da ta dace ta ba da umurnin a saki Shugaban Harkar ta Musulunci, don haka wannan suna ta kyama wani kokari ne na riga-Malam masallaci. Wannan shelar ta gaza yin daidaito, ta nutse cikin rashin adalci. Amma zai yi kyau mu tuna da gargadin da Martin Luther King ya yi da ya ce, rashin adalci a koina barazana ne ga adalci a koina.

Gwamnatin jihar Kaduna cike take da duk wasu alamomin muggan tadodin da Chamberlain ya yi magana a kan su, irin su, mugun karfi, hikidu, rashin adalci, danniya da tursasawa. Me ya sa wai abin da kawai mutane suke koyo daga tarihi shi ne ba sa koyon komai daga tarihi? Kaduna ba ta koyi komai ba daga matsalar Boko Haram. Kaduna ta zabi kawai ta gaskata Hegel da Karl Marx da suka hakikance cewa, tarihi yana maimaita kansa ne kawai koyaushe, in ji MURIC.

A don haka MURIC na kira ga dukkan masu fada-a-ji da su ji gargadin da Allah (T) ya yi a Alkurani mai girma inda ya ce a sura ta 8:25 Ku ji tsoron fitinar da in ta tashi ba kawai tana shafar wadanda aka zalunta ba ne daga cikin ku.. Ba da haka matsalar Boko Haram ta taso ba? Ketar yan sanda da kisa ba bisa doka ba da aka yi wa Shugaban kungiyar shi ya ingiza kungiyar ta zama wani injin taaddanci a kasa. Amma yan sanda ne kawai ke fama da sakamakon haka? in ji takardar menema labaran.

Sannan MURIC ta yi kira ga masu yi wa Nijeriya fata na gari da su fito fili su yi magana kan wannan mummunan mataki da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka. Babban Gwarzo Mujaddadi Shehu Usmanu bin Fodiyo ne fa ya ce, a alummar da ake rashin adalci, shiru fa babban laifi ne.., don haka mu fito mu yi magana tun kan wuri ya kure mana, in ji Farfesa Ishaq Akintola.

Har ila yau MURIC ta yi kira ga Harkar Musulunci a Nijeriya da ta sake dubi ga yadda take gudanar da harkokinta na addini, ganin yadda aka samu mutane da dama suna kuka dangane da ayyukansu. Ta ce, “ba zai yiwu a ce dukkan masu koken nan karya suke yi ba.”

Sannan ta yaba wa Majalisar koli ta Harkokin addinin Musulunci kan yadda take bin matakan diflomasiyya tsakanin gwamnati da IMN, don ganin an shawo kan matsalar da ke tsakani.