AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Buhari bai dauko hanyar gyara matsalolin Nijeriya ba -Sarkin Kano


Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari bisa yadda take karbar bashi daga Babban Bankin Nijeriya ba bisa ka’ida ba, sannan kuma ba ta tanadi wasu manufofi da za su fitar da kasar nan daga yanayin kunci da take ciki a halin yanzu ba.

Sarkin ya yi wannan ikirarin ne a Abuja a wajen taro, inda ya nuna cewa tun hawan mulkin Buhari, gwamnatinsa ta karbi bashin sama da Naira Tiriliyan 4.5 daga Babban Bankin Nijeriya, wanda a cewarsa hakan ya saba dokar da ta kafa Bankin.

Ya ce matakan da gwamnati za ta bi wajen farfado da tattalin arziki shi ne na bayar da tallafi ga kamfanoni masu zaman kansu, ta yadda za a samu masu zuba jari daga waje, sai kuma batun tsarin musayar kudade, wanda a cewarsa ya kamata gwamnati ta sassauta. Ya kuma nuna cewa Nijeriya ba ta bukatar sake ciwo bashi a cikin wannan yanayi.

Ya ce kuskure ne gwamnati ta ce za ta ciwo bashin kusan Dala biliyan 30 a kan cewa za ta biya bashin a cikin shekaru biyu.

Ya ce ciwo bashin, abu ne mai kyau, amma idan har gwamnatin za ta samu sassauci a yarjejeniyar bashin, sannan kuma a yi amfani da kudin wajen bunkasa bangaren makamashi, da lantarki da gina hanyoyi.

Sai dai Sarkin ya ce, ba ya tunanin abu ne mai yiwuwa gwamnatin Nijeriyar ta iya samo bashin Dala biliyan 30 din a cikin shekaru biyun da suka rage mata, tun da har ta kasa samo Dala biliyan biyu a shekaru biyu.

Ya ce bisa alkaluman tattalin arzikin Nijeriya na yanzu, mawuyaci ne gwamnatin Tarayya ta iya samo bashin kudin da take so, ko da a ce Majalisar Dokokin kasa ta amince mata da hakan.

Alhaji Sanusi ya shawarci Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya fi dora fifiko wajen farfado da tattalin arzikin kasa.

Ya ce hakika gwamnatin Buhari ta gaji matsaloli daga gwamnatin da ta gabata, amma kuma ba ta dauki matakan da suka dace ba na gyara kura-kuran gwamnatin da ta gabata, da kuma farfado da tattalin arzikin kasa ba.

A baya bai, Shugaban Nijeriya ya ce karbo bashin Dala biliyan 30 din yana da muhimmanci saboda karancin kayan bunkasa tattalin arziki da kasar ke fama da su a daidai lokacin da farashin mai ya faddi a kasuwannin duniya.

A martanin da ta yi a kan batun, fadar Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ta ce ba daidai ba ne kalaman da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi cewa gwamnatinsa ta karbi Naira tiriyan 4.5, yana mai cewa Naira tiriliyan 1.5 ta karba.

A wata sanarwa da Kakakin Shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar ya ce; “Ina matukar mutunta Mai Martaba saboda shi Sarkina ne; domin ni dan Kano ne. Amma akwai gyara a alkaluman da ya bayar. Gaskiya ne gwamnati ta karbi kudi sosai daga Babban Bankin Nijeriya, amma ba ta zarta ka’ida ba”.

Malam Garba Shehu ya kara da cewa; “Mu dauka maganar da ya fada gaskiya ce. Duk da haka gwamnati tana da kudin da ya zarta wanda ta karba a ajiye a asusun bai-daya. Kamar mutum ne mai asusun Banki biyu; daya babu kudi, dayan akwai makudan kudi. Menene illar kwaso kudin daya asusun domin biyan bukatar al’umma?”.

Kakakin na Shugaban Nijeriya ya ce ba zai yi wa Sarki Sanusi raddi kan adawar da yake yi ga kudurin gwamnati na karbo bashin Dala biliyan 30 ba, yana mai cewa Ministar kudi za ta tanka masa.

A cewarsa; “A matsayina na dan kasa zan so na sake karanta jawabinsa game da wannan batu ba. Amma ai za a karbo bashin ne domin yin ayyukan ci gaban kasar, cikin su har da kafa layukan jirgin kasa da samar da hasken wutar lantarki”.