AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Ba abin da zai hana mu rushe Kasuwar Barci -Gwamna El-Rufa’i

Daga Aliyu Saleh


A cikin wata hira da ya yi da manema labarai a makon jiya, Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ya sake jadadda aniyarsa ta rushe kasuwar, har ma ya yi barazanar cewa za su wayi gari wata rana su ga an kewaye kasuwar da motocin rusau (bulldozers), kuma shi zai hau kanta ya fara rusa kasuwar, kamar yadda ya yi a kasuwar Wuse da ke Abuja, shekaru 12 da suka gabata. Aliyu Saleh ya saurari hirar da aka yi. Ga abin da Gwamnan ke cewa:

“Tsari ne muka fito da shi, kasuwannin Kaduna sun matsu sun cika, Allah ya sawwake in aka samu wani tashin hankali, ko gabara, yawancin kasuwanninmu sai dai su kone kurmus, domin tsarin da yadda za a shiga a fid da kaya, ko a kashe wutar ma babu. Mun duba wannan a duk kasuwannin ban da kasuwar Abubakar Gumi, ko ita ma sai an yi gyare-gyare, domin mutane ba su ma kasuwancin a shago, sun fito sun rufe hanyar da za a bi.

“Shi ne muka ce, ya kamata kasuwannin nan a fadada su. Kasa ba karuwa take ba, amma wajen da aka yi shago hawa daya ko hawa biyu, yanzu zamani ya kawo za a iya yin hawa uku, hudu, biyar, shida, a sa ‘lifter.’ In ka je Dubai ba za ka ga irin kasuwar da muke gani ba a kasuwar Barci. Domin an ci gaba, an wuce wannan.

“Shi ne muke ganin jihar Kaduna ta kawo wani lokacin da ya kamata a sake gina kasuwanninmu. Ya za a gina kasuwanninmu? Bari mu dauki kasuwar Barci misali. Tsarin da muka yi shi ne wanda muka kawo, wannan ba kudin gwamnatin ba ne, ba mu za mu gina ba. ’Yan kasuwa ne muka kawo, muka ce masu ku zo wannan abu ne wanda yake akwai riba a ciki, ku sa kudinku ku gina.

“Kamar kasuwar Barci za a zo a dauki kashi daya cikin kashi uku na kasuwar, wadanda suke da kantuna a wajen su tashi, mun samu wajen da za su ci gaba da kasuwancinsu don kar abin da suke samu na cefane ya tsinke. Aa su koma wani waje su ci gaba da kasuwancinsu. Za mu shiga rediyo mu gaya wa mutane, masu neman sayen kaji (misali idan aka ce ’yan kaji muka tayar a kasuwar Barci), masu kajin kasuwar Barci sun koma wuri kaza, ku je can. Za mu sa a rediyo. In suka tashi, sai a rushe abin da suke da shi, sai a gini hawa uku, hudu, in aka gama gini sai su dawo, wadanda ma suke da kantuna a wani bangare na kasuwar, sai su dawo nan din, domin wajen mutum daya, ya koma wajen mutum hudu. Sai wadannan da ke wajen da kuma wasu da ke wani wajen, su dawo su shiga. Sai a samu wajen da za a sake gina wani ‘block’ din. In aka gama wannan, sai a gina wani, sannan a gina hanyoyi da sauransu.

“Tsarin da muke da shi ke nan. Mun yi wannan tsarin ne domin mu tabbatar da cewa ba a hana mutane su ci gaba da harkokin kasuwancinsu ba, kuma in ma za a matsa wa mutum, tsanin babu yawa, kuma babu dogon lokaci.

“Shekara daya ke nan da wani abu muna wannan tsarin don mu tabbatar da cewa babu wanda ya cutu, kuma duk masu shaguna a wajen za a sake ba su shaguna a sabuwar kasuwa. Wadanda ma suke kasuwanci a kan titi ba su da shaguna za su iya saye, ko su yi haya. Kuma shagunan ga wadanda suka gina shi ne; ba wai za su bayar haya ba ne, kowa za a ba shi ya sai shagonsa. Kuma muna da tsari kamar yadda muka yi na gidaje, wanda bai da karfi, in zai iya biya cikin shekaru 20, akwai Bankin da za su ba shi bashi ya sayi shagon ya biya cikin shekaru 20.

“Duk wannan mun yi domin marasa karfi su ma su samu, kuma ya zama in kasuwar tana daukar shaguna dubu uku, yanzu ya zama akwai dubu 15, domin mutanen Kaduna sun karu a yawa, muna da mutane miliyan uku a cikin garin Kaduna yanzu. Nan da shekara biyar an gaya mana za su kai miliyan biyar. Ya za a yi kasuwar da aka gina ta wajen shekara 40, me ya sa ake kiran ta kasuwar Barci, domin mutane da aka gina sun ki zuwa, sun ce in ka je wajen ba mai zuwa ya sayi kaya, barci ake yi, shi ya sa aka sa mata kasuwar Barci. Mun sani, domin a gabanmu aka yi ta.

“Mun zauna da su mutanen kasuwar Barci, domin wannan abu na al’umma ne. Saboda haka dole ne mu nuna wa al’umma ga amfaninsa ga fa’idarsa, kuma su yarda. Mun zauna da su mun yi masu wannan bayanin, suka ce su ba su yarda ba. Muka ce in ba ku yarda ba, me kuke so? Suka ce su a bar su yadda suke haka. Muka ce ai ba kasuwarku ba ce, kasuwar nan ta gwamnati ce, babu yadda za a yi ka ce kai abin da kake so da kayan wani, haka za a yi. Ku gaya mana mene ne damuwarku, shago dai za ku samu, kasuwancinku ba zai tsaya ba, za ku je wani wuri ku ci gaba. In kuna da damuwa, ku kuka zabe mu, mu bayinku ne, aikinmu ne in da damuwa mu gyara. Sun ki. Sai su je can, su je can. Sun zo sun zauna da ni. Na ce masu su je in suna da wata damuwa ga ma’aikatanmu su fada masu, mu duba. Amma kar ku ce min a bar kasuwar Barci yadda take. Domin an yi karamar gobara biyu tun da na zo gidan gwamnati, ran da aka yi babbar gobara ya za a yi?

“Ba za mu zauna muna shugabannin muna tunanin kanmu yau ba. Muna da ’ya’ya da jikoki, su ma suna neman shaguna a kasuwar nan, sai kai ka ce yau don kana da shago kar a yi wa danka da jikanka? Wannan ba daidai ba ne. Mun gaya masu ku je ku zauna da ma’aikatanmu, in kuna da wata matsala ku nuna masu, in kun fi mu gaskiya za mu iya canzawa. Amma kar ku ce ba za a yi abin nan ba. Sun ki. An sa mitin yanzu, guda biyu uku, ba su je ba.

“Ina da albishir gare su, su zauna da ma’aikatanmu su gaya mana meye matsalarsu, in za mu gyara, mu gyara, in babu gyara shi ke nan. Akwai ran da za su tashi su ga an zagaye kasuwar Barci da ‘bulldozers’, kuma zan shiga, in suna da wata shakka su je su tambayi mutanen Wuse Market a Abuja, me ya faru shekaru 12 da suka wuce.

“Babu yadda za a yi mutum ya ce shi ba za a ci gaba ba. Ba mu yarda da haka ba. Domin an zabe mu ne domin a samu ci gaba.

“Idan suna jin tsoron kudin fom ne, su sani mu a wannan gwamnati duk wani fom kyauta ne. Magana ta biyu kuma ita ce ina ba su tabbacin cewa wannan gwamnatin APC ce, duk wani mai rumfa za a ba shi rumfarsa. Maganar da suke yi na gwamnatocin da ne, ko gwamnatin mulkin soja wadda ba a zabe ta ba, ko gwamnatin PDP wadanda aikinsu karya alkawari. Mu mun fada ga abin da za mu yi, kuma muna neman kuri’arsu idan muka karya alkawari, ai sun san abin da ya kamata su yi.

“Na gaya masu da muka hadu na ce, kun gan ni nan ban son shago a kasuwar Barci, ‘Chief of Staff’ ma bai son shago. Kuma ba za mu yarda a yi shagunan, ma’aikatan gwamnati su karbe suna ba ’yan kasuwa haya ba, ’yan kasuwa muke so a ba shagunan da sunayensu, a saye masu, wadanda ba za su iya saye ba, mu fito da tsari Banki ya biya, su kuma su biya shi cikin shekaru 20. Duk wannan mun yi masu bayani. Amma ba maganar siyasa ba ce, maganar ci gaba ne. Muna rokon al’umma su gane an gama siyasa, an yi zabe, mun ci zabe, wanda ya zabe mu da wanda bai zabe mu ba, namu ne, mun dauki Kur’ani mun rantse za mu yi masa adalci. Ba wanda za mu yarda a cuce shi ko ya zabe mu, ko bai zabe mu ba, ko yana son mu, ko ba ya son mu, dole ne mu yi masa adalci. Saura kuma mun bari hannun Allah. Amma ba mu so mutane su ce ba su son ci gaba.”

RAHOTON MUSAMMAN

Yunkurin rushe kasuwar Barci, Kaduna

Kasuwar Barci da ke Tudun Wada Kaduna tana cikin tsaffin kasuwannin da ake ji da su a jihar. Tun zamanin Sardauna aka ware filin aka killace shi da nufin yin kasuwa a wajen, yayin da Marigayi Ambasada Magaji Muhammadu a lokacin da yake Kantoman riko na Karamar Hukumar Kaduna, ya bai wa kasuwar Cantral da yanzu ake kira Shaikh Abubakar Muhammadu Gumi su zauna lokacin da suka yi gobara a shekarar 1973.

Saboda rashin cinikin da sabbin ’yan kasuwar ke fuskanta a lokacin aka yi mata lakabi da Kasuwar Barci, amma dai a haka suka daure suka ci gaba da hakuri har zuwa yanzu da ta bunkasa shekaru 44 da suka gabata.

Yanzu dai tana daya daga cikin manyan kasuwannin da suka fi bunkasa, ba kawai a jihar Kaduna ba, amma har a Arewacin kasar nan. An kiyasta mutane fiye da miliyan daya ne ke cin abinci a cikinta duk wayewar gari. Yayin da take samar da kudaden shiga ga gwamnati da jama’a masu zaman kansu.

Da yawa daga cikin wadanda ALMIZAN ta zanta da su dangane da shirin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi na rushe kasuwar Barci domin gina wata, sun bayyana cewa Gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufa’i bai yi masu adalci ba, domin ba a yi masu tanadin inda za su koma ba, kuma babu tabbacin za a mai da masu da rumfunansu.

’Yan kasuwar, wadanda suke magana a cikin tsananin damuwa da wannan yunkuri na gwamnati, sun bayyana cewa Amarya in ba ta hau doki ba, bai kamata a dora mata kaya ba. “Idan gwamnati ba ta taimake mu da jari ba, bai dace ta jefa mu cikin halin damuwa ba”, in ji su.

Sai dai a wata hira da aka yi da shi ta kafafen yada labarai na jihar Kaduna, Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya lashi takwabin cewa, suna shirin bunkasa kasuwar ne, don haka suke son rushe ta, kuma babu wanda iya isa ya taka masa burki daga shirin da yake da shi na rushe kasuwar domin sake gina wata.

Wannan shiri na gwamnati na rushe Kasuwar Barci yana daya daga cikin abin da ya fi jawo cece-kuce a tsakanin jama’ar jihar Kaduna, musamman ganin yadda kasuwar ta zama wata matattara da ke hada hancin duk mutanen jihar.

Yayin da jama’a ke kokawa da yunkurin rushe kasuwar, ita kuwa gwamnati cewa take ba gudu ba ja da baya wajen ganin ta rushe ta, domin gina wata sabuwa mai hawa uku da nufin kara bunkasa harkokin kasuwancin jama’a da kuma samun kudaden shiga ga gwamnati.

Kodayake wasu suna ganin rushe kasuwar alheri ne, domin za a kara bunkasa ta ne, ta hanyar kara yawan rumfuna da kuma mai da ita ta zamani, yayin da wasu ke ganin hakan kamar rushe harkokin kasuwanci ne a garin Kaduna gaba daya.

Wakilinmu Aliyu Saleh ya shiga kasuwar don jin ra’ayin jama’a a kan wannan shiri na Gwamna, shin jama’a sun gamsu kuwa? Ga amsoshin da suka ba shi.

El-Rufa’i bai yi mana adalci ba

-Alhaji Bawa Kasuwar Barci

Alhaji Muhammad Hafizu, wanda aka fi sani da Alhaji Bawa, yana daya daga cikin dattijan da suka fara kasuwanci a kasuwar Barci shekaru 44 da suka gabata. A zantawar da ya yi da Aliyu Saleh ya bayyana matukar damuwarsa a kan yunkurin gwamnati na rushe ta. Ya yi watsi da hujjojin da Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya kawo na dalilin rushe kasuwar. Ya ce idan har ya raba su da wajen neman abincinsu, bai yi masu adalci ba.

ALMIZAN: Zan so in ji sunanka.

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Sunana Muhammad Hafizu, amma an fi sanina da Alhaji Bawa.

ALMIZAN: Alhaji me kake sayarwa a wannan kasuwa?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Ni ina sai da kayan ‘Provision’ ne.

ALMIZAN: Za ka iya tuna kamar shekara nawa nawa ka yi a wannan kasuwa?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Wannan kasuwar an gina ta ne 1973, kamar shekara 44 ke nan da suka gabata. Kuma kafin a gina ta muna kasuwancinmu ne a kasuwar Central. Da aka yi gobara, sai ka tashe mu aka dawo da mu nan aka ce za a gina Central.

ALMIZAN: A lokacin ya kuka yi kasuwar, an gina ta ne kuka shiga, ko kuwa ku kuka gina ta da kanku?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Ai rumfunan kwano muka yi; lokacin Ambasada Magaji Muhammad yana Kantoma a tsohuwar Karamar Hukumar Kaduna, shi ya ba mu wannan kasuwar.

ALMIZAN: A lokacin wane Gwamna ke nan?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: A lokacin Gwamna Abba Kyari, lokacin Gawon ne Shugaban kasa. To tsawon wannan lokacin ina nan, ka ga rumfata nan. Ina nan tun tana ta Barcinta muke zaune a cikin rumfar kwano.

ALMIZAN: Ya aka yi kasuwar ta samu wannan lakabin na kasuwar Barci?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: A lokacin barcin muke yi sosai. Don a lokacin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ce, babu sauran wadannan jaridun, ita ta dauki hotun wani da ake kira Hayatu (Allah ya ji kan sa), ya sa filo yana ta barci. Amma wani da ake kira Alamuna (shi ma ya rasu), lokacin da za a taso mu daga can a dawo da mu nan, yana cewa to me za a yi in ba barci ba?

Ita wannan kasuwar tun zamanin Sardauna take, an tsara za a yi kasuwa ne tun a lokacin, amma sai aka kewaye ta. Ashe mune za mu zauna a cikinta. A lokacin da aka dawo da mu nan shi ne Alamuna ya sa mata kasuwar barci.

ALMIZAN: A lokacin me kake sai da wa?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Ni tun ina Centra, provision nake sai da wa, kuma har yanzu shi ne.

ALMIZAN: Da yake an taso ku an dawo da ku nan ne da nufin za a gina waccan kasuwar ku koma don ku ci gaba da kasuwanciku, ya aka yi ba ku koma ba?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: A lokacin da aka gina an ba ni rumfa. Marigayi Magaji Muhammadu shi ya yi mana ‘interview’ a Res Cinema da mu da Yarabawa, lokacin babu Ibo ko daya a kasuwar. Amma sai muka ci gaba da zama a nan, tun tana ta barcinta, har Allah ya raya mana ita, ya mai da ita haka. Mun ga masu mulki daban-daban, mun ga farar hula, mun ga na soja masu damara.

An taba yin gobara a kasuwar nan, daga nan rumfa ta tashi, lokacin Tanko Ayuba ne Gwamna na mulki soja. Da ya zo yi mana jaje, sai ya ce; “Za mu duba inda za a kai ku kafin a gina maku”. Sai Sarkin kasuwarmu na wancan lokacin ya ce; “Maigirma Gwamna ina rokon arziki, mutum ne da iyali, yake samowa ya kawo, sai aka wayi gari wurin neman abincinsa ya kone, sai kuma aka ce za a mai da shi wani waje, da me zai ji? Tunda inda aka mai da shi din akwai bakunci? Ina rokon Maigirman Gwamna ya taimaka ya tausaya ya bar mu a nan?” Daga nan sai Tanko Ayuba ya ce duk mai iya ginawa, ya gina, wanda zai kafa rufa, ya kafa. A lokacin ne muka fara gina rumfunanmu. Yanzu ga shi nan ana ta dakin, wasu ma benaye suke yi. Mun ga gwamnatoci daban-daban, kamar yadda na fada maka shekaruna 44 a wannan kasuwar, amma ba wanda ya zo ya ce zai tashe mu a kasuwar nan, sai wannan gwamnatin.

Nan wajen dama kasuwa ce, kuma an tsara kasuwar za a yi a wajen tun zamanin Sardauna aka kewaye wajen. Amma a ce wannan gwamnatin da muka zaba da kanmu, ita ce kuma za ta tashe mu? A rushe a bai wa mutane? Mu ba mutane ba ne? In an ce wani yana da rumfuna da yawa, ai wannan ni’ima ce, yana iya ba da ita ga wanda ya so. Tunda ai nasa ne, saye ya yi, ba kwata ya yi ba.

ALMIZAN: Alhaji ita gwamnati tana cewa akwai rumfuna 3,000 a wannan kasuwar, in an sake ginawa za ta zama 9,000, ba ka ganin wannan ci gaba aka kawo maku?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Wannan ba ci gaba ba ne. Domin in sun ta da mu shi ke nan, sai dai Allah. Sai dai su gina su ba kansu.

ALMIZAN: Amma sun ce ba su da bukatar rumfana…

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Karya suke. Ni na gaya maka yaudara ce. Ga wacan kasuwa ta Central ba a yin wuta ba kamar shekaru 20 da suka wuce? Da aka gina ta ba a bai wa ’yan kasuwa ba, in ka ga dan kasuwa haya yake. Duk su suka rabe wa kansu.

ALMIZAN: Abin da kuke tsoro ke nan?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Ai dama haka suke yi. Wanda duk ka ga ya zo nan ya ce zai tashe mu, to zai zalunce mu ne. In za ka yi kasuwa ta zamani, ka je ka nemi wuri, ka shirya, ka ba mutane.

ALMIZAN: Akwai filayen da kake ganin zai iya samu ya gina kasuwar ke nan?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Shi ba mai mulki ba ne? Shi ya san inda zai je ya gina kasuwar ta zamani, duk wadanda suke so sai su je can.

ALMIZAN: Amma sun ce suna so su kawo maku ci gaba ne a wannan kasuwar?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Ci gaba da hakkin talaka za a yi shi? Talakawan nan fa su suka zabe ka. An mutu, maza da mata duk saboda kai. Wannan duk hakkinmu ne, mu muka gina kasuwar nan, muka raine ta, ta zama yadda take yanzu. Duk da cewa kasa ta gwamnati ce, tun da hakkinmu ne in ya tashe mu ai ya zalunce mu.

ALMIZAN: To me kuke so gwamnati ta yi?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Ya samu wani fili ya gina wata kasuwar da yake son ginawa, amma ba wai ya shiga hakkin talaka ba. Ya ce zai kwace, ya gina ya bai wa wasu. In ya yi haka bai yi mana adalci ba.

ALMIZAN: Amma an ce za a bi ta wajen Shugabannin kasuwa, su kawo sunayen masu rumfuna a ba su in an gina?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Wannan karya ne. An bai wa na kasuwar Central? Na gaya maka karya ce. Abin da ya fada ne, wannan kuwa siyasa ce. Ba mu gamsu ba. Mun san zaluntar mu za a yi. Tunda aka kafa kasuwar nan nake nan, duk wanda zai tashe mu a nan ya zalunce mu.

ALMIZAN: Akwai masu ba da shawarar cewa in mutane ake so a bai wa rumfuna, akwai rumfuna da yawa da ba kowa a cikin kasuwar Central, kai ma ka gamsu da wannan shawarar?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Sosai kuwa. Akwai rumfuna da yawa da ba kowa a can, tun da aka sake gina ta har yanzu ba ta rayu ba shekaru 20 da suka gabata. Ba sai su kai mutane can ba.

ALMIZAN: Kuna ganin in an tashi wannan kasuwar aka kai ku wani wajen, kamar an karya maku gwiwa ke nan?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Ai dama. Ai ba ma za a ba mu ba in an gina. In an kai mu wani waje ne an cutar da mu, kuma in an gina nan din ba za a ba mu ba, bayan kuma mu muka raya nan din domin can Central haka aka yi, ba a bai wa ’yan kasuwa ba, rumfunan mafi yawa na ma’aikatan gwamnati ne.

Wai har yana cewa masu tura baro ma za su iya mallakar rumfa, duk dadin baki ne. Misali a Rigasa ana so a gina kasuwa a can cikin daji, na ji an ce yankan fom din ma akwai na dubu 200, to can ma ke nan, ina kuma ga nan tsakiyar gari? Wannan fa kudin yankan fom ne, in an yi rumfar in ka samu, ba ka san abin da za a ce ka biya ba. Ina talaka zai iya wannan? In talaka na da kudin fom din, ai ya ishe shi jari. Ina sake jadaddawa in an yi mana haka, ba a yi mana adalci ba, ya yi mana zalunci babba ba karami ba. ALMIZAN: Alhaji a wannan kasuwa bisa kiyasi za a iya cewa rushe ta zai shafi mutane nawa?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Wa ya san iyakar mutanen da rushewar za ta shafa. Masu abinci, bayan masu rumfuna, wasu kuma suna da yaran da ke kasansu, ga kuma iyalai. In an rusa ta, ka ga shi an rushe shi, an rushe wadanda ke karkashinsa.

Kuma wani abu shi ne; a lokacin yakin neman zabe, wannan gwamnati ta ce talakawa za ta bai wa aikin yi. Ko ba haka ta ce ba? Yanzu maimakon ta ba da aikin yi, ga masu aikin yin za ta rushe su. In ka rushe wannan kasuwar, Allah ne kadai ya san iya adadin mutanen da za su rasa hanyar neman abincinsu.

ALMIZAN: Alhaji in an ce yanzu ga Gwamnan Nasiru El-Rufa’i a gabanka, wacce shawara za ka ba shi?

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Zan ce masa wannan abin da zai yi, ya yi hakuri ya janye, ya bar mu yadda Allah ya taimake mu ya rufa mana asiri, kar ya ce zai wulakanta mu, ya yi mana hakuri. Mun san ita kasa ta gwamnati ce, amma mu muka raya ta. In an kwace mana ba a yi mana adalci ba. Ya sake duba wannan nufi nasa na tashin kasuwar Barici. Yau shekarata 44 a nan kasuwar, in ya ture mu ga ’ya’ya ga jikoki, ina za mu? Ya duba fa Tanko Ayuba Soja ne, amma ya tausaya mana. Soja ba su yi mana haka ba, sai gwamnatin da muka zaba da hannunmu? In an tashe mu, ba sake ba mu za a yi ba, zai jefa mu a wahala ne kawai.

ALMIZAN: Mun gode Alhaji.

ALHAJI MUHAMMADU HAFIZU: Ni ma na gode.

Hoto: Ya kamata a sa hotonsa.

Rusa kasuwa, rusa al’umma ne

In ji Alh. Nasiru Ahmad Bawa

Nasiru Ahmad Bawa yana cikin matasan da tauraruwarsu ke haskawa a kasuwar Barci. Ya shaida wa Aliyu Saleh abin da suke jin tsoron game da shirin gwamnatin na rushe masu wajen mena abinci da nufin sake ginawa. Ya ce, duk lokacin da aka rushe kasuwar, ana dawo da mutane baya ne, su fara daga farko.

ALMIZAN: Zan so in ji sunanka?

NASIRU AHMAD BAWA: Ni sunana Nasiru Ahmad Bawa Kasuwar Barci.

ALMIZAN: Kamar shekara nawa ka yi a wannan kasuwar?

NASIRU AHMAD BAWA: Na yi kamar shekara 23 ina sai da kayan ‘provision’.

ALMIZAN: Akwai shiri da gwamnati take yin a rushe wannan kasuwar domin ta gina wata, a matsayinka na dan kasuwa da ke cin abinci a nan, meye ra’ayinka?

NASIRU AHMAD BAWA: Ra’ayina shi ne gaskiyar magana akwai kuskure sosai. Ya kamata gwamnati ta duba wannan abu da idon basira. Idan an rushe kasuwar, kamar gwamnati za ta mai da mutane ne su fara daga farko. An ce wai gwamnatin za ta karbe ne, sannan kuma wai sai ka je ka yi ‘applying.’ Ka ga mai rumfa 10 zai zama bai da ko daya ke nan, zai zama kamar yau ya fara nema. Ka ga wannan ba adalci ba ne. Asalan ita wannan gwamnatin nan fa ta ce za ta samar da aikin yi ne ga jama’a, amma kuma sai ga shi za ta durkusar da masu aikin.

Misali ga Central nan, lokacin da aka yi wuta, sai ya zama gwamnati ta karbe, ita ce take raba rumfunan, shekaru 20 ke nan, amma har yau akwai rumfunan da ba kowa a ciki, kashi ma ake yi a ciki. In gwamnati tana so ta taimaki mutane ne wadanda ba su da rumfuna, ai abu ne mai sauki, tana iya zuwa ta ba su jari su bude harkokin kasuwansu a wajen da babu da kowa a ciki a Centra. Ko kuma ta je ta shaci wani fili ta yi kasuwa a ciki.

Amma yanzu a zo a ruguje wa mutane, wata nawa za a dauka ana ginawa kafin a kammala a bai wa kowa rumfa? Ta yaya za su samu abin da za su ci? Kamata ya yi gwamnati ta kammala ayyukan da ta dauko, kamar cike kwalabatocin da aka haka a kofar gidajen mutane. Mu yanzu haka a kofar gidanmu, barnar da gwamnati ta yi mana na sassake mana kofar gidada yawa yake. Ta sami wajen lafiyayye, har da dakin a kasa, amma sun buge mana, famfunanmu ma sun lalata, kudin da aka kiyasta za mu kashe kafin mu gyara barnar da aka yi mana, ya fi Naira dubu 50. Gwamnati ta zo ta yi mana wannan gyara, ba wai maganar rusa kasuwa ba, rusa kasuwa, rusa al’umma ne.

Mutane suna bukatar karin jari da kuma kara karfafa masu harkokin kasuwancinsu, ba wai suna bukatar a sake wargaza su ba ne su kama tambele. Saboda haka lallai gwamnati ta duba wannan abu. Su duba tsakanin su da Allah, kar su je su sake jefa mutane cikin wata fitinar. Da ma ana fama da talauci, sannan su zo su karo shi. Abin da ya kori waccan gwamnatin shi ne rashin adalci. Bai kamata ya zama gwamnatin ta muka zaba ce za ta saka mana da irin wannan zaluncin ba. Gwamnati ta ji tsoron Allah, ta duba wannan abu da za ta yi, barna ne ga talakawa, sake sanya su cikin rana ne.

ALMIZAN: Mun gode kwarai da gaske.

NASIRU AHMAD BAWA: Ni ma na gode.

Hoto:

Ba mu taba tunanin gwamnatin APC za ta yi mana haka ba

-Jibrin Aminu

Jibrin Aminu yana daya daga cikin ’yan kasuwar da ke kasuwanci a kasuwar Barci Kaduna, ya bayyana matukar damuwarsa game da shirin gwamnatin APC na rushe kasuwar. Ya ce, ba su zabi gwamnatin nan don ta raba su da hanyar cin abinsu ba. Ga abin da ya shaida wa Aliyu Saleh.

ALMIZAN: Da farko zan so in ji sunanka?

JABRIN AMINU: Sunana Jabrin Aminu Kasuwar Barci.

ALMIZAN: Me kake sayarwa a wannan kasuwar?

JABRIN AMINU: Ina sai da kayayyakin masaka ne, wato ‘textile material’, irin su zanen gado, bargo, yadudduka da sauransu.

ALMIZAN: Kamar shekara nawa ka yi a wannan kasuwar?

JABRIN AMINU: Na kai kamar shekara 21.

ALMIZAN: Akwai shirin da wannan gwamnati take yi domin ta rushe wannan kasuwar ta gina maku wata sabuwa ta zamani, ya kake ji a ranka?

JABRIN AMINU: Tsakani da Allah ban ji dadi ba. Ba mu yi tunanin wannan gwamnatin ce za ta yi mana wannan rashin adalcin ba.

ALMIZAN: Ban gane ba.

JABRIN AMINU: Yawwa. Saboda wannan gwamnatin an ce mai adalci ce, in aka yi haka, ba a yi mana adalci ba. Saboda mu muka zabi gwamnatin nan da kanmu. Tunda aka gina Nijeriya ba a taba yin gwamnatin da ta wahalar da talakawa a kan ta zabe ta irin wannan ba. Babu wani da ya wahala don ya ga gwamnati ta kafu, irin talakan Nijeriya da suke zabe, amma sai aka wayi gari duk gwamnatocin baya da ake cewa ba su da adalci, sun cuce mu, shekara 16 suna ba mu wahala, amma daidai da rana daya ba su taba hana mu neman abincinmu ba. Amma yau an wayi gari gwamnatin da ake cewa tana da adalci, wacce muka hana idonmu barci, mazanmu da matanmu, muka tabbatar da gwamnatin nan ta hau, amma yau an wayi gari za ta hana mu cin abinci.

ALMIZAN: Kamar yaya za ta hana ku cin abinci?

JABRIN AMINU: Duk wanda ya hana ka kasuwancinka, ai ya hana ka cin abinci. Yau mutum bai kawo Naira 10 ya ba ka ba, amma ya zo ya ce zai raba ka da rayuwarka gaba daya.

Saboda mu nan kasuwar Barci ba mu taba zuwa wajen gwamnati mun nemi a ba mu kudi ba, amma mun kashe kudinmu don mu ga gwamnatin nan ta tabbata. Muna daga cikin wadanda suka kai ruwa rana, mun rika bi shago-shago don wayar da kan jama’a a kan a kiyayi PDP, amma yau an wayi gari ’yan PDP na yi mana dariya.

ALMIZAN: Da wane buri kuka yi wannan aikin na wayar da kan jama’a don su zabi wannan gwamnatin?

JABRIN AMINU: Mun yi haka ne don Baba Buhari ya daga hannun wannan Gwamnan (Nasiru El-Rufa’i), ya ce mutumin kirki ne mu zabe shi, kuma zai mana adalci. Kuma duk wanda Baba Buhari ya ce mu zaba, mun yarda da shi.

ALMIZAN: Ba ka ganin adalci zai yi maku yanzu?

JABRIN AMINU: A’a, babu adalci ko miskala zarratin a ciki. Tun a wancan lokacin ’yan PDP suka ce mu kiyayi wannan mutumin da muke cewa za mu zaba a matsayin Gwamna saboda abin da ya yi a Abuja. Muka ce ai a Abuja ‘appointment’ aka ba shi, wannan kuwa mu muka zabe shi, saboda duk mutumin da ka zaba, kana tunanin zai yi maka adalci. In ka ce ba ka son abu zai bari, in ka ce kana son abu zai yi kokari ya yi shi, a matsayin kai ka wahala ka kawo shi. Wannan abin da zai yi bai yi mana dadi ba. Ba mu yi tunanin gwamnatin APC za ta yi mana haka ba.

ALMIZAN: Me kuke so gwamnati ta yi?

JABRIN AMINU: Abin da muke so a yi shi ne; in gwamnati ba za ta taimake mu da jarin da za mu kara mu bunkasa harkokin kasuwancinmu ba, to ta yi mana addu’a, ta bar mu haka, mu zauna lafiya. Mu ’yan kasuwar Barci masu neman zaman lafiya ne. Ba a taba jin mu da wata rigima ba a kasuwar nan. Duk gwamnatin da ta zo muna ba ta goyon baya. Gwamnatocin da suka gabata da ake ce wa macuta, har gudummawa suke ba mu na jari, amma wannan ko sisin kobo ba su ba mu ba.

ALMIZAN: Kana nufin a matsayinsu na gwamnati tun da suka hau ba su tallafa maku ba ko da a kungiyance ne?

JABRIN AMINU: Mu dai kasuwar Barci ba su ba mu ba, ba mu san ko sun ba da a wani waje ba. Duk da kuwa wannan kasuwar ita ce ta fi kowacce yawan talakawa, in ka cire kasuwar Central. Ina mai tabbatar maka a tsakanin mai shago da yaransa da ke rabowa suna cin abinci, da kuma masu kawo talla da masu zuwa neman taimako, an fi mutane miliyan daya. Ka ga in ka rusa wannan kasuwar, ka rusa fiye da mutane miliyan daya da suka zabi APC, ban da irin gudummawar da muke bai wa Malaman addini da wuraren ibada.

ALMIZAN: Kana ganin rusa wannan kasuwar zai iya shafar farin jinin jam’iyyar APC?

JABRIN AMINU: Sosai kuwa. Ni bari in fada maka gaskiya, tunda Baba Buhari ya fito takara ta farko nake gwagwarmayar ganin ya ci zabe. Har dambe na yi da mutane saboda shi, kuma har gobe muna tare da shi, amma tsakani da Allah yanzu jikinmu ya yi sanyi. Idan shi Maigirma Gwamna bai san ni ba, Kanwarsa ta san ni. Tana zuwa nan ta kayan kamfen, muna bi shago-shago muna rokon mutane su zabe shi. Mutane suna cewa ana jin tsoron wannan mutumin, saboda an ga abin da ya yi a Abuja, amma muke nuna masu cewa ba zai yi haka a nan ba. Sai ga shi yana neman ya watsa mana kasa a ido. Amma dai ba shi yake da kansa ba, akwai Allah. Mun tabbatar yana da Sojoji yana da ’yan sanda, amma mu ba mu da su. Ya ce za mu wayi gari mu ga an gewaye mana kasuwa da motocin rusau, mu je mu tambaya abin da ya yi a Abuja. Mun san ya yi, amma kana taka, Allah na nasa.

Mun sani akwai ’yan bakin ciki da ke zuga shi, amma halal dinmu muke nema. Ba sata muka yi ba, ba kudin gwamnati muka wawura ba, kasuwanci muke yi, Annabi ya yi wa ’yan kasuwa addu’a, kuma ita take bin mu, shi ya sa muke ci gaba.

ALMIZAN: Amma shi ya ce yana so ya bunkasa kasuwar ne?

JABRIN AMINU: Ai mu har kasar ma muna so a bunkasa, ba wai kasuwarmu kawai ba. Ta fara dubawa, kasuwa ya kamata ta fara bunkasawa? Muna da Asibitoci, muna da makarantu, har ciyarwa an fara, yanzu ana yi? Ka kalli titunanmu ka gani? Mu muka zabi gwamnatin nan da kanmu. Ya kamata a duba a ga me ya fi muhimmanci a yi.

ALMIZAN: Wato wannan yunkurin ya jawo damuwa a tsakanin ku ’yan kasuwa ke nan?

JABRIN AMINU: Ya jawo. Ba ranar da zan kwanta in tashi ba tare da wannan tunanin a cikin raina ba. Ina tabbatar maka, wannan duk wadanda suke cin abinci a wannan kasuwar haka muke kullum.

ALMIZAN: Wasu na cewa wannan yunkurin ya rage yawan masu zuwa sayayya, wanda hakan ke shafar cinikin da kuke yi saboda tsoron abin da ka iya biyowa baya?

JABRIN AMINU: Ya rage mana. Mutumin da ya ce za a wayi gari an kawo jami’an tsaro da motocin rusau, ba dole ya jefa tsoro a zukatan mutanen da muke hulda da su ba. Ka ga dole mu samu koma-baya a harkokin kasuwancimu. Amma da yake Allah ne ya kafa mu, muna rokon ya ci gaba da tallafa mana. Abin takaici kuma wannan gwamnatin muna cewa tamu ce.

ALMIZAN: Akwai wani sako da kake da shi ga sauran ’yan uwanka ’yan kasuwa?

JABIR AMINU: Sakon da nake da shi ne, mu ci gaba da addu’a, Allah kadai muke da shi, kuma da shi muka dogara. In mutum ya fi karfinka, bai fi karfin Allah ba.

ALMIZAN: To, ga shi Gwamna Nasiru El-Rufa’i fa?

JABRIN AMINU: Muna kira gare shi ya sani cewa, amana ce mu mu a wajen sa. Yadda yake son ’ya’yansa su ji dadi, don ran nan ma na ga ya sa hotonsa a Facebook yana kwance kan kafet yana wasa da ’ya’yansa, mu kuwa yaranmu in muka je kuka suke mana saboda ba mu da abin da za mu ba su. Wani lokacin sai mu je mu nemi abin da za mu ba su, ina kuma da a ce ya rushe mana wajen neman abincinmu. Kowa yana son dansa, yadda yake wasa da ’ya’yansa suna dariya, haka mu ma muke son namu. Ya kamata ya sani mulki na Allah ne. An yi gwamntoci a baya tun daga na Soja har zuwa na farar hula, amma babu wacce ta yi yunkurin rushe mana kasuwa, sai dai su taimake mu. Babu gwamnatin da muka wahala kanta, wacce ko ba mu ce Allah ya saka mana ba, zai saka mana, in aka zalunce mu irin wannan gwamnatin. Saboda haka muna kira ga Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i, ya sani shi dan’adamu ne, mu ma ’yan’adam ne, Allah ne ya yi shi, mu ma shi ya yi mu. Saboda haka ya ji tsoron Allah, ya sani babu abin da yake dawwama in ba ikon Allah ba.

In yana so ya sabunta kasuwar Barci, ba wai dole sai ya zo ya rushe mana wannan ya kore mu ba, duk dazuzzuka na gwamnati ne, yana iya zuwa ya share ya gina. A sauran kasashen duniya in ana so a fadada birane, ba wai cikin gari ake zuwa a yi rushe-rushe ba, budawa ake yi. Saboda yadda aka kawata can din, sai ka ga mutune da kansu sun ji sha’awar zuwa can wajen. Ya je duk dazuzzukan da ke kewaye da garin nan ya bude shi ya yi ‘modern market’ iyakar son ransa, in ma za ta fi ta Washington DC ne, amma ba wai ya zo ya rusa mana wajen da muke neman abinci ba. Duk da yake fili na gwamnati ne kamar yadda yake a doka, amma kasuwar ta jama’a ce, su suka gina ta, suka rene ta har ta bunkasa. Amma ya sani in ya nuna mana fin karfi ya kwace ta, bai fi karfin Allah ba. In ya kwace mana wannan kasuwa, ya zalunce mu.