AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Jimada Ulai, 1436 JBugu na 1172 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Jonathan ya bai wa Malamai Kudi? Lalle an ba mu Inji Fasto Emos Ishaya


Imam Khumaini
A ci gaba da takaddamar shin ko Malamai da Fastoci sun karbi kudin Jonathan don su tallata shi da jam’iyyarsa ta PDP, Fasto Emos Ishaya ya yi hira da gidan rediyon Liberty, inda ya ce tabbas sun karba. Babu wani bangare da bai karbi kudi ba domin tallata wasu ’yan takara. Amma a cewarsa, ya kamata Malamai da Fastoci su ji tsoron Allah.

FASTO EMOS ISHAYA: Abin da ya kawo ni wannan gidan rediyo mai albarka shi ne in yi ‘clarifying’ wani ‘issue’, wata magana wadda ke tafiya yanzu.

TAMBAYA: Wace magana ke nan?

FASTO EMOS ISHAYA: Maganar cewa su ’yan PDP sun ba mu kudi, mu Fastoci, wai mu yi musu talla. Eh magana wannan gaskiya ne. ‘Infact’ (a hakikanin gaskiya) abu ma wanda nake so na gyara a cikin wannan magana shi ne cewa shi wanda ya fito da maganar, Gwamnan Rivers state, Ameachi ya ce, an ba mu Naira biliyan shida ne, magana din ba ma biliyan shida ba ne, magana din biliyan biliyan bakwai ne aka ba mu. Idan ka je Borno, akwai Ciyaman namu na Voice of Christian Movement, wanda aka sani da Fasto Kallamu Musa, shi ma ya yi wannan maganar. Ya jaddada cewa ‘quite alright’ an ba mu kudi. Amma abin da yake ba mu haushi shi ne, ana maganar cewa an ba Fastocin Kirista kudi, me ya sa ba za a yi maganar wanda aka ba Malaman Musulmi ba?

TAMBAYA: Amma su ma ana ta caccakar su cewa an ba su kudi, amma suna ganin cewa su ba su karbi kudi ba, wasu da suka ba su kudin sun ce sun ba su wanda za su sha mai ne na taron da suka kira su.

FASTO EMOS ISHAYA: Ai wannan magana karya ne. Maganar da suke fada cewa ba su karbi kudi ba, karya ne. Saboda mu namu mun karba on 26 ga Junairu, 2015, shi ne aka ba mu namu, Naira biliyan bakwai. ‘Infact’, bari ma in gaya maka wani abu, wannan ‘issue’ din ya so ya jawo mana rigima, saboda lokacin da aka ba mu Naira biliyan bakwai, kashegari sai su Muslim clerics (Malaman Musulmi) suka je aka ba su Naira biliyan 12. Shi ne da muka ji, muka ce uban kuturu bai isa ba, ba za mu yarda ba. Don mene ne, za a ba su 12 biliyan, mu a ba mu biliyan bakwai? Shi ne aka gaya mana cewa, ai su nasu aiki din ya fi yawa, shi ne aka ce su su rike Naira biliyan 12, mu aka ce mana mu yi hakuri.

TAMBAYA: To, yanzu duk wannan bayanan naka me kake so ka fada?

FASTO EMOS ISHAYA: Yawwa! Maganar da nake so na fada shi ne jama’a, don Allah ku yi hakuri, mun yi kuskure, mun je mun karbi kudi muna tallata PDP, muna bata Buhari da duk ’yan takarar APC. Ku yi hakuri. Kuma ina so su ma Malamai Musulmi su ma su fito su ba jama’a hakuri, saboda su suka fi yin mummunan aiki. In ka je masallacinsu za ka ji suna cewa a zabi wanda ya fi cancanta. In ka ji Malami yana ce maka a zabi cancanta, ‘to there is something behind’, wato akwai lauje cikin nadi.

TAMBAYA: Amma ba ka ganin suna cewa wannan kage ne, sharri ne, ita kanta cancantar da ake magana, a zabi mutane na gari shi ake nufi?

FASTO EMOS ISHAYA: Wane irin sharri? Wane ne ya yi musu sharri? In suna so za mu fito musu da ‘decuments’ (takardu) da dukkan su suka karbi kudi, kudin nasu ma ya fi namu. Ka gani! ‘So is very simple’ su amince sun karbi kudi, amma su daina bata mutane ‘unnecessarily’, ’yan takarar APC saboda wannan ne manufa, mu mu bata ’yan APC a coci, su su bata ’yan APC a masallaci. Su ba jama’a hakuri, su ci kudinsu, sun ci banza, saboda kudin Nijeriya ne.

Malamai A Kaduna sun musanta zargin tallata Jonathan

Daga Baban Mahdi

Cikin makon da ya gabata ne wata takarda ta bulla a Kaduna, musamman a shafukan intanet, wacce aka ce daga ofishin yakin neman zaben Goodluck Jonathan ta fito, kuma tana dauke da sunayen wasu Malamai a Kaduna, inda aka nuna an ba su kudaden da suka kama daga Naira dubu dari biyar zuwa miliyan dai-dai.

Wannan abu kuma ya zo ne a makon da ofishin mai ba Shugaban kasa shawara kan harkar addinin Musulunci ya gabatar da wani taro da Malaman addinin Musulunci don wayar da masu da kai game da muhimmancin zaman lafiya, musamman a lokacin zabe mai zuwa, wanda kuma Mataimakin Shugaban kasa, Namadi Sambo ya zama babban bako, kuma bayan tashi taron aka ba wadanda aka gayyata kudin mota.

Bayan fitar wannan takarda ce, sai wasu daga cikin Malaman da sunayensu suka fita a cikin wannan takarda suka nuna rashin jin dadinsu, inda kuma suka yi Allah ya isa da la’anta ga duk wanda ke da hannu a wannan takarda.

Malaman sun nuna wannan bacin rai nasu ne a wani taron manema labarai da suka kira cikin mnakon da ya gabata, inda mai magana da yawunsu, wanda aka nuna yana daga cikin wadanda aka ba Naira miliyan daya, wanda kuma ya halarci wancan taro, har ma ya yi jawabi a wurin, wato Malam Musa Asadussunna ya bayyana cewa, wannan takardar da aka fitar wani shiri ne na wasu ’yan siyasa don bata sunan Malaman addinin Musulunci.

Ya ci gaba da cewa, shi bai amshi kudi don halartar taron da aka yi ba, sai dai ya tabbatar da cewa an sanar da shi cewa za a ba baki wadanda suka zo daga nesa kudin mota Naira dubu hamsin-hamsin a matsayin karramawa, kamar yadda Musulunci ya koyar.

Malamin ya ce, ba wanda zai kalubalanci abin da ya fada a taron, da har zai nuna an kira su ne don tallata wani dan siyasa, illa dai don su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na sanar da al’umma da shugabanni hakkin da ke kansu, musamman a siyasar da ake ciki.

Malam Musa ya ce, “mu ba ’yan siyasa ba ne, harkar addini muke yi. Duk wanda ke APC ko PDP, matukar Musulmi ne, to namu ne, ba tare da nuna bambanci ba. Don haka duk wanda ya gayyace mu wani abu da ke da alaka da addini, za mu zo. Amma maganar wai an ba mu wani abu, wannan karya ce, batanci ne. Da yake wadanda suka shirya taron, jam’iyyar da mutane ba su so ne, amma da a ce jam’iyyar da mutane ke so ne, idan muka je ba mu yi laifi ba”.

Malamin ya kuma karyata takardar da cewa, karya ce, don ba adireshin wanda ya sa hannu a takardar, kuma sunan ba a yi shi ba. Ya kuma ce akwai wasu sunaye cikin takardar da ba Malamai ba ne, ’yan siyasa ne.

Ya kara da cewa, wasu ne suke yakar su a gefe bisa tsayuwarsu ta nemar wa al’umma mafita. “Wannan takarda kage ce daga wasu ’yan siyasa don bata wa Malaman addini suna”, in ji shi.

Shi ma wanda sunansa ne a farko a wannan takarda, wanda kuma aka nuna yana daya daga cikin wadanda aka ba Naira miliyan daya, Malam Isah Adarkake ya bayyana cewa karya aka yi masa, don bai ma halarci wancan taron ba, kuma ba a gayyace shi ba ma, ballantana a ce ya karbi wasu kudade har Naira miliyan daya, kamar yadda takardar ta nuna an ba shi.

Ya ce, shi ba ya zargin kowa, amma duk wanda ya yi wannan aiki, “na bar shi da Allah, Ya fi mu sani”. Sai dai ya kalubalanci wadanda suka yi wannan kazafi da cewa: “Duk wanda ya san an ba ni kudi, to don Allah ya fito ya fada. Idan ya rufa mani asiri, kada Allah Ya rufa masa asiri!”

Malam Adarkake ya kara da cewa, ita wannan takarda ta gabaci wannan taro, kuma akwai shakku a kanta, “don har yanzu ba wanda zai nuna maka ya san Ambasada Gazzali wanda ya sa hannu a takardar”.

Sai dai Malamin ya kawo wani hanzari ba gudu ba, inda ya ce: “Idan akwai wasu Malamai da suka rubuta sunansu, suka amshi kudin da sunansu, to Allah Ya isa!”

Daga karshe ya bayyana cewa, shi ba dan siyasa ba ne, kuma bai jingina kansa da wata kungiya ba. A cewarsa, yana da ’yancin zaben wanda ya kwanta masa a zuciya bisa cancanta a matsayinsa na dan kasa, “amma ni ba dan siyasa ba ne”, in ji Malam Isah.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron