AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Muharram 1436 Bugu na 1154 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Kungiyar RED CROSS ta ziyarci Shaikh Zakzaky

Daga Haruna Shelleng


Yan bindiga

Ranan Talata da ta wuce ne, wata tawaga ta ’yan Kwamitin Agaji na kasa da kasa, wato INTERNATIONAL COMMITTEE OF THE RED CROSS, karkashin jagoranci Hatim Ibrahim Fadlallah suka ziyarci, Shaikh Ibraheem Zakzaky a Hussainiyyar Bakiyatullah, Zariya...

Tunda farko Malam Mhammad Awwal Musa shi ya gabatar da tawagar ciki har da Shugaban ofishinsu na Kano, wato Malam Ibrahim Aliyu, sai shi Jagoransu daga ofishinsu da ke Abuja.

Da yake bayyana makasudin zuwa nasu da kuma manufar ita wannan kungiyar, Malam Ibrahim Aliyu ya ce dama sun jima suna ta kokarin su sadu da Malam, sai yau Allah ya nufa. Da ma yana daga cikin aikinsu su ziyarci Shugabanin addini da Wakilan jama’a.

Sai ya ci gaba da cewa dama su aikinsu galiban ya fi ne idan ana rikici, ko yaki a kasa, su ke zuwa su ba da Agaji.

Har ila yau yayin da ake zama lafiya, suna ziyarar Shugabanni domin su saba da su, su kuma amfana da shawarwarinsu da hangen nesansu.

Shi ma Shugaban tawagar ya yi dan gajeruwa bayani. Sannan ya yi tambaya ga Malam Zakzaky ya amsa masa. Sai ya ce “Da mun zauna a Abuja muna karanta jaridu da ba mu iya fahimta ta haka ba”.

Shaikh Zakzaky ya bayana masu cewa tun da jimawa, tun yana cikin garin Zariya, sun saba wannan kungiya kan kai masa ziyara. Ya gode masu da zuwan da suka yi.

Da yake magana a kan abin da ke faruwa a Jihar Borno kuwa, Shaikh Ibraheem Zakzaky cewa ya yi babu wani abu wai shi Boko Haram, gwamnati ke kidanta da rawanta. Ya ce Shekau wani mahaukaci ne da suka boye shi a barikinsu sai su fito da shi su gaya masa abin da zai fada, su sa masa irin kayan da suke so ya sa. Amma babu wata tsiya wai ita Boko Haram, in ji shi.

A nan sai Shaikh Zakzaky ya ambato abin da ya faru a waki’ar Kudus inda ’yan uwa 34 ciki har da ’ya’yansa uku suka yi shahada.

Sun tambayi Malam wane hali ake ciki? Suka ce ana kotu ne? Sai Shaikh Zakzaky ya bayyana masu cewa har magana ta je gaban Majalisar Dinkin Duniya. Kuma za a soma zama don a watan Nuwanba a karkashin Hukuma kare hakki bil’adam ta kasa da ke Abuja.

Malam ya bayyana irin rawar da ’yan uwa suka taka lokacin ricikin zabe na 2009. Ya ce babu mai zirga-zirga sai Ambulance din ’yan uwa, da ita ake kai marasa lafiya Asibiti. “To wannan Ambulance din ita ce soja suka ce sun kama a matsayin ganimar yaki! Ka ji wauta! Alhalin tun lokacin yakin basasa idan masu tarzoma suka hangi Ambulance na zuwa suna kauce wa ne su ba ta hanya, ta haka aka tserar da mafi yawan Ibo”, ya ce.

A nan sai shi Hatim ya ce ya kamata a samu ci gaba daga wancan lokacin, amma dai koma baya aka samu.

Shaikh Zakzaky ya karkare bayanin nasa da cewa; “Su jami’an tsaro a nan kasar ba su da aiki sai kisan jama’a. Tsaron kasa ma ba a hannusu yake ba, daga waje ake juya akalarsu”.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • ash0Sallar ash a Hussainiyya Bakiyatullah
  • ash1
  • ash2
  • ash3
  • ash4
  • ash5
  • ash6
  • ash7
  • ash8
  • ash9
  • ash10
  • ash11
  jquery photo gallery by WOWSlider.com v5.3