AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Muharram 1436 Bugu na 1154 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Husainiyya Bakiyyatullah na bukatar sadaukarwar jama’a

In ji Sayyid Muhammad Zakzaky
Daga Haruna Shelleng


Yan bindiga

A ranan Lahadi da ta wuce ne aka gudanar da Mu’utamar na Maulidi na yini daya na Wakilai da ’yan Kwamitin Maulidi na garuruwa, sai Sayyad Muhammad ya yi amfani da wannan dama ya isar da sako gare su, inda ya yi bayani a kan halin da Hussainiyan Bakiyyatullahi, Zariya ke ciki a halin yanzu...

Ya ce da yake ana gini ne, kuma ana amfani da wurin, sai ya zama kudin da ya kamata a yi amfani da su wurin ginin, dole ta sa a yi amfani da su wuri gudanar da Hussaniya din.

Ya ce ko nawa aka samu, maimakon a yi gini da su, sai su zama ‘runing cost’, waton kudin tafi da Hussainiyya na yau da kullum. Kuma ko shekara nawa za a yi haka za a yi ta tafiya matukar ba an dau mataki ba. Shi ya sa ya ga bari su yi hubbasa.

Sayyad Muhammad ya ambata cewa babu shakka ’yan uwa suna iya bakin kokarinsu wurin taimaka wa Hussaniyya din, amma dai yana tafiya ne wurin gudanar da ita, ba gini ba.

Sai ya yi bayani cewa ana bukatar ’yan uwa su sadaukar Fisabililah, saboda Hussaniyya cikin watanni biyu; kawai Muharram da Safar, sai a yi ta manya-manya kawai ta kare. Ya ci gaba da cewa masu ilimin kiddigi na abin da gini ke bukata (quantity surveyors), sun fid da komai da ginin Hussainiya ke bukata na rodi, siminti, katako, dss, wanda zai isa a gama ginin. Idan aka tsara bayanai mutum na iya ganin wane bangare zai dauka na kayan aiki. Ya kawo misali mutum daya ko gungu na iya cewa za sun dauki nauyi duk rodi ko siminti da ake bukata, dss.

Ya kuma ce za a tsara na masu albashi, shi ma su ba da kashi daya bisa biyar na albashinsu na wadannan watannin, za su kuma a aika da akwatuna na Hussainiyya a garuruwa lokacin zaman juyayin Ashura.

Ya ce bai kammala tsara abubuwan ba, amma da zarar an gama za a buga a ALMIZAN don kowa ya gani.

Yana gama jawabi sai Dakta Abdullah Danladi ya kara bayani.

Shi ma a nasa bayanin, Malam Mukhtar Sahabi cewa ya yi, yanzu ma su wadanda ke nan su fara nasu, kowa ya ba da duk abun da ke aljihunsa.

Tun farko Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi wa maharlata tarom Mu’utamar jdin awabi, inda yake cewa, ya kamata sakon ’yan uwa a lokacin tarurrukan Ashura da Maulidi ya zama daya ne.

Ya ce ba burgewa ba ne ga dan uwa ya ce zai kirkiro sabon abu, matukar kana dan Harka, to ka bi uslubi irin na Harka, idan kuma kai ba dan Hrka ba ne, ka je can wajen Harka sai ka isar da duk sakon da kake bukata. Amma matukar kai kana tare da Hrka, to dole ka bi koyarwar Harka.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • ash0Sallar ash a Hussainiyya Bakiyatullah
  • ash1
  • ash2
  • ash3
  • ash4
  • ash5
  • ash6
  • ash7
  • ash8
  • ash9
  • ash10
  • ash11
  jquery photo gallery by WOWSlider.com v5.3