AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Malam Yakubu Yahya ya ziyarci Shugaban Izala na Katsina

….Na Izalar Kano ya ziyarci Shugaban Kadiyya na Afrika


Ziyara

A kwanakin baya ne Malam Yakubu Yahya Katsina, Wakilin ’yan uwa musulmi na Katsina ya ziyarci Shugaban kungiyar Izala na jihar Katsina, Shaikh Yakubu Musa a babbar Makarantar Riyadul Kur’an, domin sada zumunci...

Tun da farko a jawabinsa, Malam Yakubu Yahaya ya ce wannan ziyara ce ta ’yan uwantaka da kuma sada zumunci, domin tattaunawa a kan mas’ala ta addini, wanda daman shi ya hada tun kimanin shekaru arba’in da suka gabata.

Malamin ya kara da cewa, “kawo wannan ziyara, a irin wannan lokaci kawai ya wadatar, ba tare da yin wata magana ba, wanda haka zai nuna cewa akwai ’yan uwantaka da zumunci na tuntuni; abin da kawai ya rage shi ne mu fadi abin da ke damun mu.”

Wakilin na ’yan uwa ya ce, “muna da damuwa iri daya, kuma wannan duniya ta sa Musulmi gaba bilhasali ma ta kama Musulmi, sauran neman mafita, wanda shi ne ya kamata a kari juna da shawarwari.”

Ya kuma ba da wani misali da tsohon Shugaban kasar Amurka na wancan lokaci, wato Bush, inda ya ce, “duk abin da muke yi a Iraki somin tabi ne, duk inda wata Islamiyya take a duniya, in dai hannunmu na kaiwa, ba za mu bari ta zauna lafiya ba.”

Malam Yakubu Yahaya ya kara da cewa, su wa ke da Islamiyya? Musulmi ke da ita.

Haka kuma Malam Yakubu Yahaya ya bayyana cewa, shi a tasa mahanga, abin da kawai zai yi maganin makiya shi ne a ga Musulmi tare, da kuma yin magana iri daya cewa, addini ake yi, duk wanda aka taba za a ji ba dadi. Idan an taba Malam Yakubu Yahaya a ji haka, idan an taba Malam Yakubu Musa a ji haka. Ya ce, “wannan shi ne babban makami.”

Daga nan sai ya jaddada cewa, babban hadafin Harka Islamiyya shi ne babu bukatar wani ya bar abin da yake yi, ya dawo yana yin na Harka Islamiyya, amma inda za a zamo ana da magana iri daya da manufa iri daya, to da wadanda suka sanyo Musulmi gaba, Allah zai sa hannu a cikin lamarin, kuma zai jefa tsoro a cikin zuciyar makiya.

A cewar Wakilin na ’yan uwa musulmi na Katsina, wannan kasa da ake kira Nijeriya, wadda muke cikin ta, akwai Musulmi miliyan dari da biyu da suke zaune a kasashen Afrika sama da hamsin, wadanda daga wannan kasa suke, banda wadanda suke nan ciki. Kuma wannan yankin da ake cewa Arewa, nan ne arziki yake. Arewa ke da jama’a da fadin kasa da arzikin cikin kasa da kuma na wajen kasa da addini da kuma al’ada.

Shi ma a nasa jawabin Shaikh Yakubu Musa Hasan, ya bayyana jin dadinsa da wannan ziyara, wadda ya ce Malam Yakubu Yahaya ya sha kawo irin ta gare shi, kamar yadda shi ma ya sha kai irin wannan ziyara domin sada zumunci na ’yan uwantaka.

Ya kara da cewa, wannan ziyara ta nuna ’yan uwantaka, manufa ita ce, yaya za a yi addinin Allah ya ci gaba, sannan a samu tabbataccen zaman lafiya a cikin wannan kasa. Duk wani Malamin addini mai da’awa, wadannan abubuwan su ya saka a gaba.

“Gaskiyar magana, matsalolin da suke damun mu, kamar yadda Malam ya bayyana sune yadda muke nisantar juna. Ni kuma zan kira abin da rarrabuwa, domin Allah Ta’ala ya ce “wa’atasmu Bihablillahi jami’an...” Haka kuma Allah Ya hana rabuwa. Tabbas ko yara sun san idan aka rabu, to an samu matsala,” in ji Shaikh Yakubu Musa.

Haka kuma bayyana cewa, matsalarmu guda ita ce rarrabuwa, kamar yadda Annabi (S) da Sahabbai suka samu nasara, cikin kankanin lokaci Musulunci ya cinyen gabashin duniya da yammacinta, to babban abin da muke bukata shi ne hadin kai. Kuma wannan ba zai yiwa ba, sai ana zama ana tattaunawa irin wannan, kuma ana karantar da mutane su fahimci hakikanin addinin Allah.”

Daga karshe Shaikh ya kara nuna farin cikinsa, musamman irin yadda Malam Yakubu Yahaya ya bayyana halin da wannan duniya take ciki, da kuma makamin da za a yi amfani da shi wajen rushe makiya da hana su kawowa ga addinin Musulunci.

Haka kuma ya yi fatan alheri ga Malam Yakubu Yahaya tare da ’yan tagawarsa da suka raka shi, domin yin wannan ziyara mai cike da farin ciki da kuma tarihi. ….Na Izalar Kano ya ziyarci Shugaban Kadiyya na Afrika Daga Ali Kakaki

A karshen makon da ya gabata ne Shugaban Izala na jihar Kano, kuma Daraktan masallatai na kasa, babban Limamin masallacin Juma'a na Shaikh Ja'afar Mahmud Adam da ke unguwar Tudun Murtala, Dk. Abdullahi Saleh Pakistan ya kai ziyarar dubiyar rashin lafiya ga Halifan Tijjaniyya na Afrika, Khadimil Kur'an, Shaikh Ishak Rabi’u.

Shaikh Pakistan ya bayyana wannan ziyara a matsayin girmamawa ga Halifa domin jajanta masa kan nauyin jikin da ya samu a 'yan kwanakin nan. Ya yi addu'ar samun sauki da tsarkaka da kankarewar zunubi.

A nasa jawabin, Halifan Tijjaniyya, ya bayyana matukar jin dadinsa da wannan muhimmiyar ziyara da Jagoran na Izala ya kawo masa. Ya kuma ce, wannan ziyara ya dauke ta a matsayin wata hanya ta hadin kai, don haka ya yi kira ga musulmin kasar nan da a kara hada kai, in aka yi la’akari da irin bala'in da ke tunkarar musulmin kasar nan.

Halifan ya nuna wa tawagar karimci bisa yadda ya karbi Shehin na Izala da tawagarsa.

Shugaban Izalar ya tafi da kusan dukkan 'yan Majalisar sa da suka hada da Daraktan yada labarai na kungiyar Izala ta kasa, Malam Ali Dan Abba.

Allah ya kara wa Malam lafiya, ya kuma sanya albarka cikin wannan ziyara, in ji wani da ya shaidi ziyarar.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron