AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Gasar Hadisai 20 ta Sayyida Fatima (SA):

Malama Aina'u ta lashe kyautar mota a Kano

Daga Muhammad Isa Ahmad (muhd1389@gmail.com)


Aina'u
Domin girmamawa da yada sanin wace ce Sayyida Zahra (AS), ’yan uwa mata na Da’irar Kano suka jibinci al’amarin gasar rubutu a kan Sayyida Zahra (AS), aka kuma yada ta kafafen labarai ga duk wanda ta zama gwarzuwa za a ba ta mota...

Hakan ya kasance a ranar Asabar 2 ga Sha’aban 1435(31/5/2014) a filin masallacin Juma’a na cikin gari, inda Shaikh Muhammad M. Turi ya mika wa Malama Farida A. Hasan mukulli da takardun motarta kirar Mazda.

Malam Yusuf Abdullahi, kafin ambata gwarzuwa ya yi takaitaccen bayani a kan gasar, inda ya fadi irin ka’idojin da aka sanya a kan rubutun, da kuma yadda aka bi wajen tantance wadanda suka cika ka’idoji, kuma aka duba, aka kuma ga wanda ta zama gwarzuwa.

Gasar dai an bude ta ne ga wadanda ba ’yan Harka Islamiyya ba, an kuma samu rubutu 31, wadanda suka cika ka’idoji 18 ne kuma Malama Farida A. Hasan ta samu maki 87, Hajiya Maimunat A. Giwa ta samu maki 85 da kuma Malama Aina’u Malama Surajo maki 73.

An raba kyauta kashi biyu ga wadanda suka shiga gasar suka kuma samu maki mai yawa, mata hudu da Shaikh Khidir ya mika masu kyaututtuka, da kuma kashi na biyu da Shaikh Muhammad Turi ya mika wa ta uku da ta biyu kyautar keken dinki, yayin da ta daya aka mika mata mukullin motarta.

A hira da ’yan jarida suka yi da wadanda aka karrama da kyaututtuka, sun nuna farin cikinsu da yadda ’yan uwa domin girmama al’amarin Sayyida Zahra (AS), suka yada alamarinta tare da karrama su da kyaututtuka.

Malama Maimuna Abdullahi, wadda take jibintar al’amarin mata na Harka Islamiyya a Kano, ta nuna farin cikinta, da yadda a kullum ake kokari wajen riko tare da son koyi da Ahlul Baiti (AS) kamar yadda a kullum Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky yake nuni da kwadaitar da mu. Ta yi fatan ya kasance a kullum an ci gaba.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron