AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Fada ya sake rincabewa a Afrika ta Tsakiya


Afrika ta Tsakiya
Mutane biyu sun yi asarar rayukansu a cikin wata zanga-zangar nuna kyama ga gwamnatin jamhuriyar Tsakiyar Afrika. Masu zanga-zangar sun nemi Shugabar kasar na Wucin-gadi Catherine Samba-Panza ne da ta yi murabus, sannan kuma dakarun kiyaye zaman lafiya na Burundi su fice daga kasar... ..

Hakan ya faru ne bayan wani hari da aka kai wa wata Majami’a ta kiristoci, da ya haddasa mutuwar mutane 15.

Akwai alamu cewa ana mai da taho da aka daga a kan neman maslaha game da rincabewar da al’amura suka yi a jamhuriyar Tsakiyar Afrika. Hakan kuma sakamakon yakin addinin da ya farraka al’ummomin kasar har ya kai ga a yanzu suna kyamar junansu, sashe da sashe.

Yanzu dai Catherine Samba-Panza, Shugabar wucin-gadi ta jamhuriyar Tsakiyar Afrika, wadda aka sanya wa kauna wajen hadin kan kasa, kusan abubuwa na kubuce mata, watanni biyar ke nan bayan da Majalisar wucin gadin kasar ta zabe ta. Hakan kuma ya kai ga a yanzu jama’ar kasar na fitowa kan titi suna kira ya zuwa yin murabus din ita Catherine.

Shi kuma Firaministan kasar, Andre Nzapayeke, fitowa ya yi yana zargin wasu mutanen da yake kira na boye da suke ingiza jama’ar kasar ya zuwa ga neman yi wa gwamnatin kasar zagon kasa.

Su kuma sojojin Burundin da ake bukatar su fice daga kasar, tuhumar su ake yi da yin sako-sako wurin kare nuna kyama ga kiristoci.

Wasu rahotanni kuma sun ce an gina shingaye a wasu muhimman wurare na birnin Bangui, dakarun kiyaye zaman lafiya kuma sun dinga yin harbi da bindiga a sama domin tarwatsa masu yin zanga-zanga.

Tun watan Junairun shekarar nan dai fadace-fadace a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika suka juye zuwa na addini. A hannu guda akwai su Anti-Balaka masu kishin addinin Kirista da kuma su Saleka, wadanda akasarinsu musulmi ne. A dalilin haka ne ma kowanne daga gare su ke rusa wuraren addinin kowa.

Mal. Usman Abubakar, wani mazaunin birnin Bangui ya shaida wa gidan rediyon BBC halin da suke ciki da cewa, “mu kam tun safe jiya ba dama, bindiga da bindiga kawai kake ji, gari motoci ba su shigewa. Yau ne gobe ne, ba mu san abin da muke ciki ba. Tun abin karfe 3:00, kafin mu tafi masallaci Assalatu, sun zo sun kawo mana hari. Da ma unguwa daya, 10 Kilo, ya yi saura wanda musulmi suke ciki. Shi ne ’yan Anti Balaka suka ce sai sun zo sun gama da mu, kuma su yi juyin mulki, tsohon Shugaba Bozize ya dawo mulki. Sojawan Afrika su ne suka kewaye unguwar musulmi na 10 Kilo. Yanzu masallatan da suka yi saura mana guda biyar ne. Na Juma’a guda uku suka yi saura mana a 10 Kilo.”

An tambaye shi cewa, amma ana maganar Kiristoci ne suka yi zanga-zanga saboda kona wani Coci da aka yi. Sai ya ce, “Kiristoci ne, amma Bozize ne yake bayan su. Ba duka mutanen Afrika ta Tsakiya suke bayan abin ba.”

Aka ce masa kuma, ana cewa suna zanga-zanga ne don nuna bacin rai saboda kona wannan coci, suna ganin kamar cewa sojojin kiyaye zaman lafiya na Faransa da na Afrika ba su kare fararen hula. “Tunda sojawan nan suka zo, mu musulmi muke da wahala. Mu ne aka farfasa mana masallatai, aka farfasa mana gidaje duka. Inda muke din nan ba mu isa mu yi komai ba. Ba ma fita, yau kusan wata shida ke nan. Ko ’yan uwanmu ko abokanenmu sun aiko mana da kudi, in mun je banki daukawa, Anti Balaka suna kashe mu,” in ji Usman Abubakar

Sai aka tambaye shi, me ya sa ba za ku fita ku bar kasar ba, kamar yadda sauran ’yan uwanku suka yi? Sai ya ce, “Domin kasar tamu ce. Mu ne asalin kasar nan. Mutane ba su san komai ba. Nasaru ba su sani ba ne suka goyi bayansu. Bangui din nan duka namu ne. Bailaru din nan musulmi ne, Lakombga sunan musulmi ne, Saydou sunan musulmi ne, Moammadou Bakiy sunan musulmi ne 10 Kilo sunan musulmi ne, unguwanni ne. Shi ne mu musulmi muka ce ba za mu fita ba, gwamma a kashe mu a wannan garin, da ma gari na Allah ne. Mai salla ma na Allah ne, wanda yake so ya yi kirista ma nasa ne.”

Aka sake ce masa, kun gamsu da matakan kariya da sojojin kiyaye zaman lafiya suke ba ku na Faransa da na Afrika? “Mu mun yarda da aikinsu, da kyau. Muna so su ci gaba. Wasu ne suka kawo fada na Kirista da Musulmi, amma ai mu da ma ba mu da matsala da kirista. Mun jima a nan ba mu da wannan matsalar. Kawo mana shi aka yi,” in ji Usman Abubakar mazaunin birnin Bangui na jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron