AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Ana yi ma Musulmi kisan mumuke a Taraba

- Al'ummar Musulmin Wukari
Daga Mahdi Muhammad


Kisa

Kungiyar Al’ummar Musulmin Wukari da ke karkashin kungiyar Muslmin Council of Taraba State, reshen Karamar Hukumar Wukari ta koka kan kisan mummuke da sojoji ke wa Musulmi da sunan cewa su ‘’yan kungiyar Boko-Haram ne...

Shugaban Wukari Federation of Muslim Ummah, Jalingo, jihar Taraba, Alhaji Sanny Sule Saleh tare da sauran shugabannin al’ummar musulmi, sun yi watsi da maganar da ake yi cewa rikicin da ake yi a yankin rikici ne da ke tsakanin Fulani makiyaya da Jukunawa manoma.

Saleh, wanda ya yi wannan bayanin ga manema labarai a Abuja, ya ce rikicin tsakanin musulmi ne da kirista; su Kiristocin yawancin su Junkunawa da Tibabe, wadanda kuma suke samun kariyar wasu ‘’yan siyasa da kuma manyan jami’an tsaro.

“A lokuta da dama kuma a wurare daban-daban mutanenmu ana ta damun su, ana kama su, ana tsare su ba bisa doka ba, kuma wasunsu jami’an tsaro na kashe su ta haramtacciyar hanya. Kodayake wannan kusan a kullum yake aukuwa, jami’an tsaron da abin ya shafa kullum musantawa suke yi, kuma ba su damu su binciki gaskiyar koke-koken da muke yawan kaiwa ba,” a cewar Saleh.

Ya kuma ce a ranar 15 ga Afrilu, 2014 sojoji rike da muggan makamai suka mamayi gidan wani musulmi mai suna Goshi Musa Garba, wanda ke sana’ar gyaran takalmi a Wukari, suka kama sh da dansa Nasiru, suka kuma je gidajen wasu musulmi a garin suka kama mutane 15, ciki har da wani Danini Nuhu Bala, kuma har yanzu ba iyalansu da al’ummar musulmi ba su san inda suke ba.

Ya ce, sun sha mamaki da kawai suka ga hotunansu a jaridu da Talabijin, ana cewa an kama ’yan boko-Haram.

Ya ce, takardar koke, sun gabatar da ita ga Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa (NHRC), kuma daga cikin abin da suka bukata shi ne suna neman duk jami’an tsaron da aka zargin suna sakaci da aikinsu ko suna wuce-gona-da-iri a ayyukansu, to a tsamo su kuma a tabbatar sun fuskanci shari’a.

Mai magana da yawun Ma’aikatar tsaro, Manjo-Janar Chris Olukolade bai ce komai kan wannan koke ba, kuma bai ba da amsa ga sakon wayar salula da aka aika masa ba, har aka buga rahoton nan.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron