Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1127, ISSN 1595-4474


Babban Labari

Mun gano inda daliban Chibok suke

- Hafsan tsaron Nijeriya
Amurka na tababar ikirarin


Yan matan chibok

Rundanar sojan Nijeriya ta bayyana cewa ta gano inda daliban makarantar sakandire ta garin Chibok da ke jihar Borno da ’yan kungiyar da ake cewa Boko-Haram suka sace suke...

“Daddadan labari ga iyayen wadannan ’yan mata shi ne mun san inda suke, amma ba za mu gaya muku ba,” cewar Hafsan tsaro na sojin Nijeriya, Air Chief Marshall Alex.

“Ba za mu zo muna gaya muku sirrin soja ba, ku kyale mu kawai, muna aiki tukuru don mu ga mun dawo da ‘’yan matan nan,” ya ce.

Ya kuma tabbatar wa da manema labarai cewa ba su da burin amfani da karfi wajen kwato ’yan matan da aka ce yawansu ya kai 250.

Sannan ya ce, “lokacin da Shugaban kasa ya ce akwai Alka’ida a Afrika ta yamma, na yarda da shi dari bisa dari.”

Sai dai kuma Amurka ta ce ba ta da bayani mai zaman kansa da ke tabbatar da cewar an san inda ’yan matan Chibok da aka sace suke.

Kakakin Ma’aikatar harkokin kasashen wajen Amurka, Jen Psaki ta ce, “Ba mu da bayanai masu zaman kansu game da ikirarrin cewa an san inda ’yan matan suke.”

Ta kara da cewa, “A cikin tsarinmu da kuma batun lafiya da kariyar ’yan matan, ba za mu yi magana a bainar jama’a ba a kan bayanai irin wadannan.”


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron