Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1131, ISSN 1595-4474


Babban Labari

Shahidanmu Gwarazanmu

- Shaikh Zakzaky


Harin Bom
A ranar Asabar 25 ga Rajab, 1435 (24/5/2014), Mu’assatus Shuhada ta shirya taron tunawa da Shahidan Harkar Musulunci a Najeriya a filin Polo da ke kusa da Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya, inda a wajen taron Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky ya bayyana cewa Shahidanmu sune gwarazanmu... ..

Sannan ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na 24 da muke yin Yaumus Shuhada. Su kuma shuhada dinmu, wanda har yanzu ba mu gushe ba muna samun su, kowace shekara akan samu Shahidai 2,3,4, wata shekarar sai ta zo ta wuce ba a samu shahidi ba.

“Tun 1402 (1982) aka samu Shahidin farko. Ya zuwa yau har aka samu Shuhada 145.”

Shaikh Zakzaky ya nuna yadda shahada ba tana da arha ba ne. “Wanann ya isa ya nuna maka ko adadi ma ya nuna maka cikin shekara 33, shahidi kasa da 200. Shahada ba tana da arha ba ne.”

Sannan ya ce; “in son makiya ne, duk su kashe kowa da kowa. Sukan zo da mugun fushi da nufin su bude wuta, ya zama sun kashe duk wanda za su iya kashewa, sai ka ga sun karata sun kashe mutum 1 ko 2.”

Sannan ya kawo misalin yadda suka taba zuwa wani masallaci a Kaduna tun lokacin yana tsare, ana Ta’alimi, kuma suna ganin Ta’alimi ne, sunan ganin akwai Mata har da jarirai, amma suka rika aikawa da harsasai masu rai. Sai da akwatinan harsasansu suka kare, suka hau motarsu suka gudu. Sai suka ji a BBC a labaru, ance ainihin an kashe mutum.

Har ila yau Shaikh Zakzaky ya nuna cewa, “daman al’adar masu aukar da shahada, daga masu satar Akuya, sai mai satan bargo. Sai mai na Agwagi da Kaji. Barayi ne duk.” Sai ya yi tambaya da cewa; “ka taba jin mutumin kirki yana kashe bayin Allah?”

Sannan ya nuna shahada tsada gare ta. “Kun san farashin shahada kuwa? Aljanna fa! To, aljanna kuma tana da tsada.”

Ya kuma jaddada wa masu aukar da shahada cewa; “masu tunanin za su bude mana wuta, su kawar da mu su fid da rai. Za ku iya bude mana wuta, amma wadanda Allah ya kaddara ma Shahada ne kawai za su yi. Biyu ko uku, an gama.”

Ya ci gaba da cewa, “shahada ba sassaukan abu ba ne. Zabin Allah ne. Shi ya sa duk lokacin da ka ji an ce wane ya yi Shahada, in ka bincika, sai ka ji mutumin kirki ne. Sai ka ji mutane suna yabon sa.”

Sannan ya tabbatar ma Shuhadan wannan Harka cewa; “ga Shuhada din mu, sai mu ce, muna taya ku murna, na cewa; ku karshenku ya zama shahada ne ma. Ma’ana shaida. Muna ba ku tabbacin insha Allahul azim, abin da kuka ba da jinainanku a kai, to, muna nan a kai, har ya zuwa lokacin da za mu cim muku insha Allah.”

Sannan ya bayyana cewa, daga bara zuwa bana, mun samu shahidai guda hudu. Wanda guda uku suka yi shahada a lokacin raka ’yan uwa na Sakwkwato. Sannan dayan ya yi shahada ne ta sanadiyyar harbin su da aka yi a kan hanyarsu ta dawowa daga muzaharar Ashura da aka yi a Sakkwato.

Bai karkare jawabinsa ba, sai da ya tunatar da ’yan uwa dangane da hakkokin shahidai.

Har ila yau cikin jawabinsa ya karfafi ’yan uwa wajen biyan hakkin Shuhada. Sannan ya tabo janibin shahidai masu rai, wadanda aka jijjima ciwo. Inda ya kawo misali da Hizbullah, wadanda suke da Mu’assasa din masu rauni na daban. Amma sai ya ce; “amma mu, Mu’assatus Shuhada ita take kula da masu rauni.”

An yi taro lami lafiya, kuma kowa ya koma gidansa lafiya.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron