Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1131, ISSN 1595-4474


Babban Labari

Kisan Fulani a Saminaka: Majalisar Jigawa ta aiko da Kwamitin bincike

Daga Mahdi Muhammad


Dokar ta baci

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta aiko da wani Kwamiti na musamman daga jihar zuwa jihar Kaduna, domin bin kadin kisan da aka yi wa wasu Fulani kwanakin baya a garin Saminaka, bisa zargin cewa ’yan ta’adda ne...

Hon. Rabi’u Dangarba Kwalam ne Shugaban wannan kwamiti da Majalisar ta turo, kuma ya bayyana wa manema labarai a Kaduna cewa, “mun zo ne domin mu kawo godiya ta Majalisa, a madadin al’ummar jihar Jigawa, mu gode wa duk wadanda suka taimaka wajen wannan abu. Mun je Saminaka, mun sami Sarkin Saminaka, Shugaban Karamar Hukuma, da DPO, duk mun zauna da su. Mun nuna masu godiyarmu, Allah ne zai saka masu,” in ji Hon. Kwalam.

“Wani abu muhimmi da Majalisar ta aiko mu a kai, shi ne mu tabbatar wa jama’a cewa wadannan Fulani da aka kashe, ’ya’yan jihar Jigawa ne, kuma makiyaya ne, ba masu laifi ba ne. Sannan majalisa ta umurce mu cewa mu yi kokari mu bi duk hanyoyin da suka dace mu nemo bayanai na yadda wannan al’amari ya kasance. Sannan mu roki Hukuma, a binciken da take yi, idan an samu masu wannan mummunan aiki, to a tabbatar an hukunta su,” in ji shi

Ya ci gaba da cewa wadannan Fulani suna tafiya ne a hanyoyin burtaloli na kasa da kasa. To, amma sai aka yi masu wannan ta’adi, “saboda haka duk wanda aka kama da hannu a wannan abu, to ya kamata ya dandana kudarsa don ya zama darasi ga ’yan baya,” in ji shi.

Daga nan kuma ya ci gaba da cewa shi da sauran ’yan Kwamitinsa, sun nemi gwamnatin jihar Kaduna da sauran wadanda abin ya shafa da su taimaka su biya diyya, ko tallafa wa iyalan wadannan bayin Allah, “don a rage radadin rashin da iyalansu da aka bar su suke ciki. Wadannan abubuwa ne Majalisa ta turo mu da mu yi, kuma abin da muka nema ke nan,” ya ce.

Daga nan ya tabbtar da cewa yanzu haka ana nan ana bincike, kuma sun yaba da matakan da ake dauka kan wannan lamari. Don haka suka nemi cewa a tabbatar da cewa an bi diddigin wannan abu. Kuma cikin su shida din nan da aka kashe, hudu daga cikin ’yan jihar Jigawa ne, iyayensu duk sanannu ne a jihar Jigawa.”

Mambobin wannan Kwamiti sun hada da Hon. Shehu Liman, Hon. Umar Liman, Hon. Yaro hadi, Hon. Adamu Sarki Niga, Hon. Adamu Shu’aibu, Hon. Babbangida Usman Hadejiya da Barsita Musa Aliyu Abubakar a matsayin Sakatare. ...Ana neman adalci a kisan da aka yi wa Fulani a Sanga

An yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta yi bincike cikin gaggawa kan yadda aka yi wa wasu matasa Fulani biyu kisa a Fadan Karshi da kuma wani dattijo a fadar Sarkin Numana, ta kuma tabbatar an hukunta wadanda suka aikata laifin.

Wasu matasa biyu ne, Yusuf Idris da Yahuza Yusuf daga Ator a gundumar Aboro, wasu gungun jama’a suka yi musu kisan gilla a Fadan Karshi, kuma ’yan sanda ba su bai wa iyalansu gawawwakin ba don janaza. Ba a kuma fadi wani dalili na rafke matasan har mutuwa ba.

Haka kuma wani mutum, Malam Isa Idris daga gundumar Aboro, wanda aka kira shi zuwa fadan Sarkin Numana, shi ma an yi masa bugun kawo wuka har sai da ya mutu.

Shugaban Miyetti Allah na Karamar Hukumar Sanga, Alh. Alhasan Naruwa ya ce wajibi gwamnati ta bincike wadannan lamurra biyu, don hukunta masu laifi a ciki.

Ya kuma nemi ‘’yan sanda su ba da gawawwakin matasan biyu don a yi musu janaza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron